43- Haduwar Su

625 59 6
                                    

Suna isowa Almadinat Hospital na Kaduna suka iske Ishraq zaune a reception zaman jiran su. Da sauri ya sha gabansu yana kallon Mahboobah da ke jigace, Mommy da Aliyu sun tallabo ta. Ya kasa dauke kallon shi daga gare ta, ganin yadda ta yi wani irin fayau, ta rame, idanuwanta sun firfito waje, kwantaccen gashin gaban goshinta ya bayyana. Sai ta kara yi mishi kyau sosai da kwarjini.

Da sauri Malaman jinya suka yo kansu, ganin halin da take ciki ya sa aka kai ta emergency, Aliyu kuma ya bada refer letter din, ya bar Mommy da Ishraq tare da Mahboobah. Noor kuwa tun suna shigowa Kaduna ya musu sallama, dama ya karbi lambar wayar Aliyu da ta Mommy. Ya ba su wayar Mahboobah suka rabu.

Kamar yadda likitan Zaria ya fada wa su Mommy na Kaduna ma haka ya fada musu. Saboda babban abun mamaki ne a ce yarinya mai karancin shekaru kamar Mahboobah jininta ya haura ma 180. Mommy ta masa alkawarin da yardar Allah za su kiyaye.

Sai da Saleemah da Haneefa suka zo sannan Mommy ta ce za ta koma gida. Nan fa ake yin ta, domin kuwa Ameerah cewa ta yi babu inda za ta je a bar ta wurin Amminta. Da Mommy ta takura ta a kan su tafi ma kuka ta fasa tana kama karfen gadon Mahboobah.

"Wai Ameerah ya za a yi in bar ki ku kwana asibiti kamar ni ma ke ce." Mommy ta fada tana gyada kanta. "Aliyu maza dauko ta mu tafi gida dare na yi."

"Wayyo Mommy ki daina yi mata tsawa." Saleemah ta fada tana marairaice fuska.

"Kun ga masu diya su fa ba a isa a fadi laifin Ameerah ba. To ai ku da kuka iya lallaba sai ku lallaba ta, in dai Ameerah ce ba sanin mutunci ta yi ba."

Dariya aka dauka duka dakin. Haneefa ta ce "Ta san mutunci sosai mana Mommy. Ko Ameerahna?"

Gyada kai Ameerah ta yi cikin kuka alamar a'a. Mommy me za ta yi ba dariya ba ta hau tafa hannuwa. "Ai dama na fada muku ba ta san mutunci ba ga shi nan iyayen ma ta gwasale su."

"Mamana...ki yi hakuri ki bi Mommy ku tafi gidan kin ji. Kin ga gobe akwai makaranta."

Ta kara noke kafada tana kallon Ishraq da ke mata maganar.

"Mommy ku tafi kawai idan ta yi barci zan kawo ta."

"To Ishraq. Mun gode sosai sannu da kokari, Allah Ya saka da alkhairi, ka sha dawainiya."

Kanshi kawai ya sunkuyar kasa, ko amin din ma kasa-kasa ya fada, shi a ganin shi ai yi wa kai ne, Mahboobah tashi ce don ya mata abu babu faduwa a ciki.

Bayan Mommy ta tafi Mahboobah ta farka. Ganin su Saleemah ya sanya ta sakin murmushi tana jin dadin ganin su a cikin ranta. Domin su din makusantanta ne wadanda za ta iya raba damuwarta tare da su.

Cikin azama Ishraq ya iso inda take, ya dan rusuna a gaban gadonta idonshi a cikin nata yake fadin "Sannu Madam. Ya jikin naki?"

Kauce ma haduwar idanuwansu ta yi tana kara tsuke fuska, ta amsa sannun da su Saleemah ke mata. Duk da haka bai yi zuciya ba ya kara fadin "Sannu Mahboobah. Da ma jiran farkawar ki nake sannan in tafi, ina da night consultation."

"Da sauki." Kawai ta fada ba tare da ko kallon shi ta yi ba, ta mika ma Ameerah hannunta ta je wurinta.

"Ammi ashe kin dawo." Ameerah ta fada tana kokarin hawa jikin Mahboobah.

Bakuwar FuskaWhere stories live. Discover now