PART 3

4 1 0
                                    

*ABINDA BABBA YA HANGO.......!*

_Short Story._

*MALLAKAR DOCTOR MARYAMAH IBRAHEEM.*

*Whattpad@MaryamIbrahim244.*



________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

*YADDA AKE DAFA SHINKAFAR KWAKWA*

*Yana da kyau uwargida ta san yadda ake dafa nau'ukan shinkafa. Kada ta tsaya a shinkafa fara da dage-dage ko jalof din shinkafa kawai.*
*Yana da kyau idan za ta dafa shinkafarta, ta dan kawata ta da su ganye domin karin jini da lafiya a jiki. Idan a sati kina dafa shinkafa ba tare da yi mata wani hadi ba to tabbas ne abincinki zai fita daga ran maigida.*

*ABUBUWAN DA AKE BUKATA*

*Garin kwakwa ko markadaddiyar kwakwa*
*- Shinkafa*
*- Karas*
*- Koren tattasai*
*- Koren wake kanana (Peas)*

*YADDA AKE HADAWA*

*A dora ruwa a wuta. Idan ya tafasa sai a zuba shinkafa har sai shinkafar ta tafasa na tsawon minti 15 sannan sai a wanke da ruwa a sa a matsami a ajiye._ _A kankare karas, sannan a wanke kamin a yayyanka shi kanana.*
*A wanke tattasai da koren wake da koren kanana (Peas) sai a yayyankasu amma banda (Peas) din.*

*Bayan an kankare bayan kwakwar an markada farin, sai a zuba ruwa sosai. Da ruwan kwakwar za ayi sanwar dahuwar.*

*A zuba ruwan kwakwar a tukunya bayan ya tafasa sannan a zuba wannan ajiyayyen shinkafar idan ta kusa dahuwa sai a zuba yankakken koren tattasai da karas da koren wake da kuma koren wake kanana (Peas) a rufe da murfi a rage wutar girkin.*

*Bayan mintuna biyar, sai a gauraya wannan shinkafar a sauke. Shikenan an kammala._ _Ko da maigida ba mai son cin shinkafa bane zaki ga ya fara sha'awar cin irin wannan girkin. Za a iya hada wannan girkin da miyar kaza ko miyar kifi.*

*بسم الله الرحمن الرحيم.*

*EPISODE 11_15.*

🖊️"Sorry abokina , kasan mata zama dasu sai da haƙuri don haka ka ƙara haƙuri wata rana sai labari".

Girgiza kai kawai ya yi , kana suka ɗauko maganar shigo da kayan da za'ayi jibi.

Zaune suke a cikin wani ɗaki wanda gaba ɗaya sa kayan tarkacen tsubbu ne a ciki, sai wani sunku cecen mutum baƙiƙirin dashi sai ƙaton cikin dake maƙale da jikinsa, baya sanye da komai na dangane da sutura sai wani ƙyalle daya ɗaura a ƙugunsa, buɗan idanuwa kawai ya keyi yana faman lashe baki.

Kallonsu ya yi sannan cikin muryarsa mai firgitarwa ya ce "dole ne aikin ki ya dinga gaba yana dawowa baya, mahaifiyarsa ce tsaye a kansa bata bacci kullum itace ke faman wargaza mana aikinmu."

Cikin marai raicewar murya ta ce "yanzu ya za'ayi kenan ya shugaba?."

"Idan har kina son aikinmu ya yi kyau a kansa ba makawa sai an kawar da waccen tsohuwar, muddin tana raye ba zaki taɓa cin galaba a kan ɗanta ba."

Ɗan jimm ta yi sannan ta ce "to a kawar mana da'ita don kuwa akan na mallaki komai na Ƙasim ba abinda bazan iya aikata wa ba."

Wani ƙullin magani ya miƙo mata sannan ya ce "ki tabbatar da kin sanya mata wannan a cikin abinci, da zaran taci sa to tabbas sai dai wata ba ita ba, mutanen mu basa iya tunkarar gidan sune, dasu zamu sanya domin su kawar mana da ita cikin sauƙi, amman ko wannan me sauƙi ne kije ki jarraba ki gani."

ABINDA BABBA YA HANGO......!Where stories live. Discover now