PART 4

4 2 0
                                    

*ABINDA BABBA YA HANGO.......!*

_Short Story._*

*MALLAKAR DOCTOR MARYAMAH IBRAHEEM.*

*Whattpad@MaryamIbrahim244.*



________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

*LEMON KANKANA DA LEMON TSAMI*

*Kayan hadi*
*• Kankana*
*• Lemon tsami/* *Lemonade*
*• Sukari/sirof*
*• Flavour*

*YADDA AKE HADAWA*

*Uwargida za ki fara dafa sukarinki ya zama ruwa amma fa kada ki bar shi ya kone idan ya dahu shi ne abin da ake kira sirof sai ki ajiye a gefe guda. Shi wannan sirof din ya fi saukin amfani a kan ki yi amfani da sukari na ainihi.*

*Sai ki yanka kankanarki ki fitar da kwallayen sannan ki markade yadda za ta yi laushi sosai.*
*Sa ki samu kofin da kike hada lemo ki zuba a ciki sannan ki kawo lemon ana sayar da shi a manyan shagunan kayan masarufi idan kuma ba ki da shi za ki iya yin amfani da lemon tsami.*

*Idan kika matse sai ki ki tace shi da kyau ki tabbatar babu komai a ciki sai ki juye a kan kankanar nan sai ki dauko sirof dinki ki zuba ki kuma kawo filebo mai kanshin kankana ki zuba, sai ki juya ki sa a firiji don yin sanyi.*


*بسم الله الرحمن الرحيم.*


*EPISODE 16_20.*

🖊️Sai bayan ta sauke Hajiya Turai a ƙofar gidan tane kana ta fara tunanin ta yadda zata samu damar da zata aiwatar da ƙudirinta.

Sosai ta shiga tunani , ta dai san tsawon shekara ɗaya da wata uku da aurensu da Ƙasim sau ɗaya ne kachal ta taɓa zuwa gidan su.
Nan kuma wani tunanin ne ya koma tarbonta , ta tuna ko rasuwar mahaifinsa bata je gaisuwa ba.

Sosai ta shiga cikin ruɗani sai can kuma ta ce "dole ne ma yau ɗin nan mu shirya da Ƙasim.

Cike da ƙwarin gwiwa ta shiga gidan parking space ta nufa ta yi parking kana ta yi cikin gidan.

Karo na farko tun bayan aurensu data nufi kitchin da niyar ɗaura girki.

Sai da ta gyara kitchin ɗin sama sama ta wanke waƴansu kwanukan suma sama sama , kana ta ɗaura girki.

White fice da stew wacce taji kayan lambu, ta girka sannan ta janyo sabbin kuloli ta sanyawa megidan sannan ta sanywa Hajiya Umma a cikin wata haɗaɗɗiyar kula kana ta kawo maganin ta sanya a cikin miya ta motse.

Bedroom ta nufa ta cire kayanta ta ɗaura towel ta nufi ban ɗaki, ta silalo wanka wanda rabonta da wanka ta yi 2weeks kullum sai dai a feshe jiki da turare a bi hanya.

Gaban mirror ta zauna kana fara fente fuskarta da kayan shafa iri iri , daga bisani kuma ta janyo wata doguwar riga roba mai adon stone stone ta sanya ta janyo wani baƙin ɗankwali ta buga ɗauri ta feshe dukkanin ilahirin jikinta da turare.

Sosai kyaunta ya fito ta yi fess da'ita kamar a sace ta a gudu.

Parlour ta koma ta harɗe cikin kujera ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya.

Sai bayan sallar magrib sannan ya shigo gidan gabansa na faman buga wa.

A Parlour ya tarar da'ita ta harɗe sai faman ƙyalli takeyi, da saurinta ta miƙa ta tarbo shi.

Kana ta taimaka masa ya yi wanka , shi dai duk mamakin canjin da yasa mu ya cika masa ciki, amman ba damar tambaya yanzu.

Parlour suka fito ta gabatar masa da abinci , wannan karon mamakinsa kasa ɓoyuwa ya yi saida ya fito fili.

ABINDA BABBA YA HANGO......!Where stories live. Discover now