PART 6

2 1 0
                                    

*ABINDA BABBA YA HANGO.......!*




*MALLAKAR DOCTOR MARYAMAH IBRAHEEM.*

*Whattpad@MaryamIbrahim244.*



________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

*LEMON ARDEB*

*Assalamu alaikum. Uwargida, tare da fatan alheri kuma ana cikin koshin lafiya.*

*Na san mutane da dama ba su san me ake kira ‘ardeb’ ba. Wannan ardeb dai yana nan ne kamar lemun tsamiya. Kuma yana da alaka da mutanen Maiduguri.*

*A irin wannan yanayi da muka shiga ana yawan hada wannan ‘ardeb’ din ko kuma jus din tsamiya, sannan a sanya shi ya yi sanyi domin sanyaya zuciya a lokacin zafi.* *Akwai hanyoyi biyu da ake bi don yin wannan hadin.*

*KAYAN HADI*

*Tsamiya*
*Siga*
*Masoro*
*Kanamfari*
*Citta*
*Ruwa*
*A samu tsamiya a wanke tsaf ya fita sannan a jikata ta jiku sannan a daka kayan yaji; masoro da citta da kuma kanamfari. Sannan a dora tukunya a wuta, bayan tayi zafi, sannan a zuba sukari, har sai ya narke, sannan a zuba ruwa. A dauko wannan jikakkiyar tsamiyar a tace a zuba a cikin ruwan sukarin, sannan a tankade dakakken kayan yajin a zuba a gauraya sannan; Kuma sanya shi a gidan sanyi domin dandano ya fito sosai.*

*Daya hadin kuma shi ne, a tafasa tsamiya tare da kayan yaji sannan a tace. A dora tukunya a wuta bayan tukunya tayi zafi, sannan a zuba sukari ana gaurayawa, har sai sukarin ya narke sannan a zuba ruwa da wannan tsamiyar da aka tace. Hadin ‘ardeb’ ya hadu*

*بسم الله الرحمن الرحيم.*


*EPISODE 26_30.*


🖊️Cikin ɗan ƙanƙanin lokaci ya kammala ya ɗauko ya kawo mata har Parlour, cikin jin daɗi ta hau ci tana lumshe idanuwa "ba ƙarya ya iya girki ashe", ta faɗa cikin ranta.

Tana kammalawa ta miƙe ta nufi bedroom tana bashi umurnin kamin ta fito daga cikin ɗaki ya kankanta Parlourn ya yi shara da morping.

Jikinsa har rawa yake yi gurin sharar, yana kammala shara harya ɗauko bokitin morping kiran sallar magarib ne ya ratsa dodon kunnen sa.

Ɗan jim ya yi yana shawarar yaje ko ya bari harya kammala?, amman inaáh sai kawai ya ci gaba da morping ɗin.

Sai da ya mayar da Parlourn fess dashi sannan ya yi zaune yana jiran fitowar ta.

Wanka ta feso cikin ƙananan kaya sai ƙamashin turare dake fita daga cikin jikinta, fuskarnan tasha uban make up sai ƙyalli ta keyi.

Gurin zama ta nema ta zauna tana mai ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya sai faman ƙarewa Parlourn kallo ta keyi.

Ta gefen ido yake kallon kalar shigar da ta yi, yayinda ita kuwa ta yi kamar bata gansa a gurin ba.

Sunanan zaune kamar kurame a kayi kiran sallar isha'i.

Kallonta ya yi a maraice yana neman yaji ta ce "tashi kaje".
Lura da hakan da tayi ne ya sanya ta cewa "ɗan bara na gwada naga".

Kallonsa ta yi kana ta ce "tashi kaje masallaci."
Da hanzari ya miƙa, ai kuwa saiji ya yi ta ce "koma ka zauna ba inda zaka".

Komawa ya yi ya zauna kuwa yana me faman sakin murmushin yaƙe.

Sosai ta jinjina wa aikin bokan nata, ta saki murmushin gefen baki tana ayyana irin yadda zata wata ya da wannan damar data samu.

ABINDA BABBA YA HANGO......!Where stories live. Discover now