PART 5

2 1 0
                                    

*ABINDA BABBA YA HANGO.......!*

_Short Story._


*MALLAKAR DOCTOR MARYAMAH IBRAHEEM.*

*Whattpad@MaryamIbrahim244.*



________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

*LEMON KARAS*

*Abubuwan hadawa*

*Karas*
*Cittah*
*Sugar*
*Flavour*

*Yanda ake hadawa*

*Da farko zaki wanke karas dinki ya wanku sosai sai ki yanka kanana ki zuba a bilenda. Sai ki wanke cittah itama kiyanka kanana ki zuba a bilenda kisa ruwa ki markada da karas dinki, yayi laushi. Sannan sai ki tace kisa sugar da flavour. Ki juya sosai sai ki sa a firinji yayi sanyi.*

*Shi karas yanada kyau sosai wajen kara lafiyar ido*

*بسم الله الرحمن الرحيم.*


*EPISODE 21_25.*

.🖊️Ɗakin daya kama musu ya nufa da ita kai tsaye yana faman shashafa sassan jikinta, ya yinda ita kuwa sai faman ƙara shigewa jikinsa ta keyi.

Kallonsa ta yi da idanuwanta da suka fara canjawa cikin sarƙewar murya ta ce "Alh yaushe ka dawo?."

Janyeta daga jinsa ya yi ya hau rage kayan dake jikinsa , saida ya koma daga shi Sai ƴar ciki da three quater, kana ya zauna a gefenta yana shafar fuskarta ya ce "yanzu yanzun nan muka sauka, nasan kina nan shi'isa kai tsaye nayo nan, don kinsan na yi missing ɗinki irin sosai ɗin nan ", ya faɗa tana mai kashe mata ido ɗaya.

Haka wannan daren suka sheƙe ayarsu ba kunya balle tsoron Allah.

Ubangiji Allah ya tsare mana imanin mu, Amin ya Allah.

Gaba ɗaya hankalinsa ya gama tashi, ganin har 12am ba ita ba labarinta.

Zuwan sa kusan uku gidan Hajiya Turai sai dai har lokacin da yayi zuwa na uku ba ita ba labarinta a ƙargame ƙofar gidan take a haka ya juya ya nufi gida, cike da tashin hankalin ina ta nufa.

Gaba ɗaya ya rasa gunda zai sanya kansa, ba tada gurin zuwa sai gidan Hajiya Turai wacce tace masa ƙanwar mahaifiyarta ce.

Har ƙarfe 2am ba ita , kala yana kiran wayarta tana shiga har aka fara ce masa switch off.

Ƙarfe 6am ya koma jan mota ya nufi gidan Hajiya Turai, a ƙargame har yanzu garkar take.

Ya jima a wurin kana ya ja motar ya bar gurin.
Kai tsaye family hause ɗinsu ya nufa.
Sashen Hajiya Umma ya nufa hankalinsa a tashe yake sanar da'ita komai.

Itama jikinta ya yi sanyi saka yau , amman bata nuna masa damuwarta ba ta daice Allah ya bayyana ta.

Ƙarfe 12pm jirgi ya lula dasu cikin gajime rai daga Kano zuwa Lagos ita da  Alh Sambo zai halarci wani taron ƙarawa juna tsayi na tsawon mako biyu.

A babban hotel ɗin dake cikin birnin Lagos suka sauka, sosai yana yin garin ya tafi da imaninta.
Wannan ne karo na farko data taɓa shiga garin.

Sabon sim card ta sanya a cikin sabuwar wayar da Alh Sambo ya mallaka mata a daren jiya, don ta manta da wayarta a gurin Hajiya Turai.

Gaba ɗaya Allah ya shafe mata sanin wai ita matar aure ce, sosai suke ɓarje lokacin su ita da Alh Sambon ta, wanda ke sakar mata maƙudan kuɗaɗe ita kuwa ta buɗe jikka sai kwasar nata rabo ta keyi.

ABINDA BABBA YA HANGO......!Where stories live. Discover now