chapter 01

5 1 0
                                    

🇿🇦
South Agent


Acardia building,pretoria.

Bayan mai taxi ya saukeshi,tsayawa yai yana karema ginin kallo kaman yanzu ne ya fara ganinsa.Makeken gini ne Mai hawa Shida,kasancewar glass ne gaba daya yai masa ado sai daukan ido yake saboda hasken rana daya bude gaba daya kaman ba Safiya ba. Gini ne dayake matukar kauna kuma yake farin cikin ganinsa a ciki a koyaushe,amma yau sai yakejin akasin hakan,saboda Sam bai tsara  zuwansa ba a cikin kwankin nan. Yasaka hannu a cikin sumar kansa wadda ya bari ta dan fara taruwa yana furzar da hucin iska daga bakinshi. A tsari sai nanda 2weeks 4days sannan zai sake tako kafarsa nan amma da farar safiyar yau an kirawo shi urgently. Banda wanka babu abinda yai dan ko breakfast bai tsaya yayi ba,saboda yanayin aikinsa duk sanda akai kira to dole ka amsa.

Ya fara taku dai-dai kafin ya kai dubansa ga wristwatch dinsa 9:20 iska ya kuma hurowa sannan ya dan kara hanzarin takun nasa, he's 20 mins late.

Daya karasa gaban makekiyar glass door din, Kai tsaye gurin wani black box ya nufa,numbers ne 0-9 a jere,sai kuma # da *. Ya danna combination code din sannan kofar ta bude, admitting him into a cubicle. Scanning dinsa computer tayi from head to toe sannan red arrow dake saman kofar ya koma green a take kuma kofar ta bude,sai gashi a makeken reception.

Ta cikin glass din daya katange receptionist da sauran hall suka hada ido da Mr.zantu,wanda ya dago daya ji alamun shigowar visitor,ganin wanda ya shigo ne yasashi dan sakin fuska sannan yai nodding kansa,shima bakon kai ya daga masa in response kafin ya doshi gurin lift ya hau.

A second floor ya fara tsayawa don ya duba chief louw amma sai ya tarda office din a rufe. A daidai lokacin wayarsa ta hau kara,yana dubawa yaga Assistant Director Siyabonga Cwele ne,dan haka ya amsa wayar.

" Agent Mambo you've already wasted enough time,to the conference hall now!"

Yana sauke wayar yakai dubansa saman corridor dinda yake,sannan ya jinjina kai ga cctv camera,yasan suna kallonshi. Haka maaikatar take sam basu san sirri bah,har toilets akwai saidai cikin cubicles dinne kawai bata haskawa.Haka ya juya wajen lifter ya danna 6th floor dan zuwa conference room.

Kaf saman 5'6th floor kofofi 3 ne kawai a corridor daya,biyu na kallon juna daya ta office din Director Whyte Edison,saita Assistant dinsa Mr Siyabonga Cwele, Sai kuma babbar double oaked door wadda take tightly programmed,ita ce a can bangon karshe dake facing wanda yake tahowa. Shiyasa ba kowa kake gani a saman ba sai babban business ya kawo ka. Shikansa conference room din ba kowa keda licence din shiga ba,dan kananun ma'aikata harsu kare services dinsu a nan bazasu taba zuwa ba saidai idan akwai babban dalili wanda babu mai fatansa dam bazai zamto alheri ba.

Irinsu manyan Agents ne kawai suke shiga,suma saidai idan zasu karbi mission ne ko zasuyi success briefing,ko kuma idan wata matsalar ta taso. Yanzu haka ma tunanin dalilin kiran yake,kuma yafi ta'allakashi da wata tangardar aka samu,tunda dai yasan ko sati biyu baiyi da barin nan bayan briefing akan mission dinda ya gama kuma ya dauki hutu dan rabonsa da samun leave shekaru 3 kenan.

Saida yai scanning ID card dinsa,sannan yai thumb print kafin a bashi access na gurin saka code din bude kofar. Bayan shigarsa kofar ta rufe,shikuma ya tsaya cak bai kara taku ko guda ba yana karema Hall din kallo,wannan room za akirashi ne ko house? dan tafkeken gaske ne,ga seats nan in a circular pattern,a jikin kowane seat akwai siriryar microphone dazata bawa mazaunin kujerar damar tofa albarkacin bakinsa ko a ina yake a zaune. Ga makekiyar majigi ta kusa shafe tsayin bangon gabashin dakin. Director Edison na kan kujerarsa a zaune wadda ko a kala ma ta bambanta da tasu,gashi kuma tana daga kan stage yana facing sauran, yadda zai iya ganin kowa,kuma kowa zai ganshi.

SouthAgentWhere stories live. Discover now