Chapter 02

3 1 0
                                    

🇿🇦
South Agent

                                                    0️⃣2️⃣


SOUTH AFRICA

South Africa, officially the Republic of South Africa(RSA) Kasa ce dake a karshen kudancin nahiyar africa,daga ita babu wata kasar sai Atlantic Ocean. Jasa mai samada alumma million 60, the 23rd most populous nation in the world.

Kasa ce da ake ma lakabi da rainbow nation saboda mabanbantan aladu da kabilu. Akwai Farare(Europeans),Asians (Indian and Chinese) sai kuma burbushin Dutch, Mexican da sauransu.

Manyan kabilunsu guda 11 ne; Afrikaans,Ndebele, pedi,Swazi,Tsonga,Tshimbe,Venda,Xhosa,Zulu da Tswana. Kasancewar suma England ne sukayi musu mukin mallaka shiyasa English shine official language dinsu,amma alummar sunfi yin yarukan Isizulu da Isixhosa.

Natural resources, Agriculture, tourism da manufacturing su suka maida ita kasa mai largest economy a gaba daya Africa.

Kasar nada capitals 3, Pretoria, Bloemfontein and Cape town.Kudinsu kuma ana suna cemasa Rand(R).

Dukda kasancewar kasar nada arziki amma kaman Nigeria,fiye da quarter na kasar basuda aikin yi,kuma suna rayuwa a kasa da US$1.25 a kullum.

Addini Bai wani damesu bah kuma majority christians ne(73.2%), Muslims (1.7%),marasa addini(14.9%) duba da yanayin percentage na musulmi zaka gane ba wani musulunci ake a kasar ba.

South Africa kasa ce mai arzikin Albarkatun kasa da kuma coal,anyi mata kiyasin 41% of all worlds gold and 90%of platinum metals.

Kasa daya tak a duk duniya data taba karbar bakuncin world cup na manyan wasannin duniya( football, cricket & rugby).

Kasace Mai guraren bude Ido,da masana'antu. Ga deserts, wetlands, grasslands,bushes, subtropical forest,etc. Kuma ita ce kasa ta uku a duniya a bangaren ingancin ruwan sha.

Kasa ce mai guraren hadari,kama daga barayi manya da kananu,fyade,kasha-kashe. Misali, Pretoria data ke capital nada crime index of 81.78,dan haka tazamo the most dangerous city in the world. Ga Durban me high murder rate data zamto ta biyar a duniya a bangaren kasha-kashe.

•••••

Cikakken sunansa,shine Theodore Schwann Mambo. Jami'in babbar hukuma ta sirri dake south frica(SOUTH AFRICAN SECRET SERVICE,SASS). Agent daya nuna tsananin kwazo da hazaka a bangaren aikinsa,ba a taba tura shi mission baici nasara ba duk hadarinsa kuwa, koda zai dawo da  muggan raunuka wani sa'ilin ma bayan mission dinsa saiya kwanta asbiti,shiyasa hukumar take ji dashi kuma duk wani aiki mai wuya da hadari shi suke turawa gudun faruwar matsala.Wasu lokutan abokan aikinsa kan tafi mission,amma su samu matsalar blown cover,kuma idan hakan tafaru sai yai sanadiyyar rayuwarsu,yawanci inda aka turasun da sun ganosu kisan wulakanci suke musu.

Komai nasu a sirri akeyi,ko ID card dinsu biyu ne,wanda suke nunawa a gaban jama'a idan bukatar hakan ta taso daban[police CID],sai kuma na hukumar tasu,duk saboda tsabar sirri, kasancewar aikinsu mai tsananin hadari ne da kuma bukatar sirri,bayyanar hakan ksmar mutum ya saka ranar mutuwarsa ne tunda akwai batagari da yawa kuma ba lallai kasan da wanne kake tare ba. Ko a family members, parents ko spouse kadai hukumar tabawa damar sanin ainihin sirrin aikin,shima a hakan ba a yarda su san wane mission din kake ko wace kasar zaka ba.

•••••

Ya gama shirinsa tsab! Amma ya kasa fita daga apartment din nasa,kuma ya rasa dalili. Ba wannan karon ne farko dazai fara mission mai hatsari ba,amma a wannan karon sai yakejin jikinsa duka a mace,sam babu kuzari da doki saima wasi-wasin da yaketa ji a zuciyarsa. Yanaji kaman ba lallai ya dawo da rai ba. Ya kai dubansa ga frame din dake manne a bangon gabashin dakinsa, wannan shine karo na uku daya karema hoton kallo dan haka ya taka a hankali zuwa gurin.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Aug 02, 2022 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

SouthAgentWhere stories live. Discover now