FADHEELATUN NISA 4

36 4 0
                                    

Nagarta Writers Association.

FADHEELATUN NISA.

FITA TA HUƊU.

Mallakin
(QURRATUL-AYN).

***
Madiha ta ja da baya a gigice tare da fidda idanuwa waje cike da tsoro da fargabar abin da bata san ta inda ta samo kwarin gwiwar aikatawa ba, Jaid runtse ido ya yi da ƙarfi yana mai cije laɓɓansa na ƙasa tamkar zai huda su kafin ya buɗe idon nasa akan fuskarta, cikin zafin nama ya ɗaga hannu da nufin wanka mata nata kwakwkwaran marin, lokaci guda zuciyar Madiha ta tsinke tana mai cigaba da harbawa da sauri da sauri tuni jikinta ya fara ƙyarmar rawar sanyi yayin da ta runtse ido tana shirin karɓar hukuncin da yake shirin zartarwa akanta, sauke hannunsa ya yi ƙasa yana mai girgiza kai ya juyawa a fusace ya fi ce daga cikin hall ɗin har yana ture na bakin ƙofar, shiru ta ji ya yi yawa hakan ne ya sanya ta buɗe idonta a hankali har lokacin bata bar ƙyarma ba, wayam ta gani babu shi babu dalilinsa a wajen da sauri ta koma mazauninta ta zauna tare da ɗora kanta akan bencin hawaye masu zafi suka fara zarya akan kuncinta.

Ko da Junaid ya fita kai tsaye inda ya yi parking motarsa ya nufa, duk wanda ya kalleshi a wannan lokacin yasan yana cikin tsananin ɓacin rai matuƙa, cikin motarsa ya shige ya zauna yayin da ya kwantar da kai akan kujera ya rufe ido ƙarar sautin marin na amsa amo cikin dodon kunnensa, hotunan abin da ya faru suka cigaba da gilma masa ɗaya bayan ɗaya.
Cikin makarantar kuwa kafin wani lokaci labari ya bazu kamar zubar ruwan sama ta ko ina maimaicin zancen ake yi har da masu ƙarin gishi da maggi akai domin labarin ya yi armashi, sabuwar ɗaliba ta mari Jaid.

"Madiha da gaske ne labarin da nake ji..!".

Maganarta ta katse a daidai lokacin da Madiha ta ɗago da kanta daga kan bencin ta dubi Hamah dake tsaye a wajen, neman guri ta yi ta zauna da sauri tana faɗin.
"Da gasken ne kuwa ya mare ki? Wallahi sai na yi masa rashin mutunci, danma yasan kina da naki gatan kema."

Ta miƙe a fusace zata bar wajen.

"Ni na mare shi Hamah."

Cak Hamah ta tsaya kafin ta juyo da mamaki ta koma ta zauna jikinta kamar babu laka, yayin da ruwan hawayen dake kwance kwarmin idon Madiha ya cigaba da gangarowa.
"Kika mare shi a garin ya ya? Kuma mene dalilinki?."
Madiha ta gyara zama bayan ta share hawayen nata kafin ta cigaba da bawa Hamah labari, tsaki Hamah ta ja da faɗin.
"Shi ne kuma kike zubar da hawayenki abanza, kin ga kima daina kuka duk inda aka je shi ne da laifi da yasan yana da gaskiya da ya tsaya, ni wallahi na ɗaukama shi ya mare ki kamar yanda ake ta yamaɗiɗin zancen a makarantar duk hankalina ya tashi wallahi."

"Ina kuka ne saboda fargabar rashin sanin irin hukuncin da zai zartar akaina, ban sani ba ko ƙarshen zuwana makarantar kenan."

Hamah ta ja tsaki mai sauti, kafin ta miƙe tsaye tana mai tattara litattafan Madiha ta ce.
"Kinga tashi muje ki wanke fuskarki, babu abin da ya isa ya yi miki wallahi, idan yana taƙama da kuɗi da alfarma muma muna da ita tsaf zan sanya Dadyna ya tsaya miki ka da ma ki sanyawa kanki damuwa abanza har a zo ana kallonki garama ki yi fuska kawai."

Takai maganar tana mai jan hannun Madiha suka fice daga cikin hall ɗin kamar raƙumi da akalarsa.

***
"Laila me ya hanaki zuwa school yau?."

"Mom banjin daɗi ne kawai wallahi.."

Wayarta data fara ringing ce ta sanyata yin shiru tana mai mayar da hankalinta ga wayar, number Salima ta gani ta ɗauka tare da karawa a kunnenta.
Salimah ta fara magana da faɗin.
"Hello Laila, yau ba ki shigo school ba?."

"Banjin daɗi ne."

"Ayya Film ya barki kuwa."

"Kamar ya, ban fahimce ki ba?."

FADHEELATUN NISAWhere stories live. Discover now