FADHEELATUN NISA 14

10 4 0
                                    


Nagarta Writers Association.

FADHEELATUN NISA

FITA TA GOMA-SHA-HUƊU.

Mallakin
   QURRATUL-AYN.

   Tana kaiwa nan ta ɓalle murfin ƙofar ta fice a fusace tare da banko masa murfin da ƙarfi, wanda har sai da ya sanya shi runtse ido yana mai kaiwa hannun hagunsa naushi da dama, yana huci da furzar da iskar zafin ƙasan zuciyarsa, da gaggawa ya figi motarsa ya fice daga harabar gidan yayin da wata baƙar mota dake can gefe a ɓoye tabi bayansa itama cikin matsanancin gudu.

    Tsananin ɓacin rai ne ya hana Junaid lura da binsa da ake yi, kamar da ga sama ya tsinkayi ƙarar ringing na wayarsa, kamar ba zai duba ba sai kuma ya ɗauki wayar yana mai ƙarewa screen ɗin wayar kallo, number Hajiya Falmata ya gani wacce ya yi serving da Aunty, ɗauka ya yi tare da sallama bayan ya sanya a headfree.
                 "Ka zo ina nemanka."

"Me ya faru Aunty?."

"Lafiya ƙalau, amma dai ka zo yanzu maganar mai muhimmanci ce."

"Ok."

Ya faɗa a yayin da ta kashe wayar, Junaid ya juya kan motarsa tare da ɗaukan titin da zai sada shi da gidan Auntynsa, ganin da suka yi ya shiga titi mai jama'a sosai ne ya sanya suka taka burki tare da ɗauke hanya daga bin bayan nasa.

      Ko da ya isa gidan a bakin gate ya yi parking saboda saurin da yake yi daf ake da fara kiran sallar maghriba, bayan ya yi knocking mai gadi ya buɗe kai tsaye ya sanya kai cikin farfajiyar gidan yana mai shigewa ciki, a ƙofar falon ya tsaya bayan ya yi sallama amsawa ta yi kafin ta ce.
   
  "Shigo mana Junaid, gidan baƙonka ne?".

Cikin salon maganarta faɗa-faɗa, a hankali ya sanya kai tare da neman kujera mai zaman mutum biyu mafi kusa da shi ya zauna yana dubanta.
                Harara ta watsa masa kafin ta ce.
      "Wai yaushe zaka canja hali ne Junaid?".

Kau da kai ya yi gefe ba tare da ya tanka ba, sanin halinsa da ta yi ne yasa ta cigaba da faɗin.
                    "Me ya haɗa ka da Lailah?."

Dubanta ya yi tsayin lokaci bawai na mamakin tambayar da ta yi masa ba, take ya ji wani irin abu ya taso masa da ƙyar ya iya haɗa laɓɓansa tare da lankwasa harshensa wajen faɗin.
  
   "Dama akan Lailah kika kira ni?."

"Junaid ! Ya kamata ka nutsu kasan abin da yake yi maka ciwo, kasan dai tun da Hajiya ta kafe akan batun auren nan babu makawa sai anyi shi fa, gara ma tun wuri ka saduda ka miƙa wuya."

   Wani irin murmushin gefan baki ne ya suɓuce masa wanda ke bayyanar da tsantsar takaici akan fuskarsa kafin ya sake dubanta a karo na biyu ya ce.
            "Yanzu rayuwa na tafiya da abin da zamani ya zo mana da shi ne, ko mata a yanzu linzaminsu ya yi nesa da auren dole bare ɗa  namiji Aunty, Namiji nake ! Ina da 'yancin yin rayuwata yanda na so, ni nake da damar da zan zaɓawa kaina abin da nake ganin shi ne daidai da rayuwata ba wani ba, ina tunanin idan har kuka cigaba da matsawa akan auren nan a ƙoƙarin ku na ƙulla zaren zumunchi zaren zai suɓuce muku ya tsinke."

  "Me kake nufi Junaid? Na ce me kake nufi?."

Murmushi ya sake yi kafin ya bata amsa da faɗin.
   "Ina nufin bana son Lailah, bana ƙaunar auren nan."

"Amma Junaid duk akan me hakan? Mene dalilin da yasa baka son Lailah? Ni ko kusa banga wata makusa a tattare da Lailah ba har da wani namiji zai buɗe baki ya ce baya sonta."

"To ni dai bana  sonta, asali ma bata daga cikin mafarkina akan irin matar da nake da burin na aura."
     
    "Yakake ganin Abbanka da Mamy zasu kalli lamarin? Kana tunanin za su goyi bayanka ne wajen cikar burkinka? Ko yanzu nasan sunyi shiru ne saboda basu san halin da ake ciki ba, amma kasani maganar Hajiya ita ce kaɗai Abbanka yake ji fiye da dukkan maganar kowa a duniyar nan, Mamy kuwa tana duban fuskar Abbanka ne bata musu ko jayayya akan abin da Abban ya yanka mata."

FADHEELATUN NISAWhere stories live. Discover now