FADHEELATUN NISA 9.

33 4 2
                                    


Nagarta writers Association.

FADHEELATUN NISA.

FITA TA TARA.

Mallakin
   QURRATUL-AYN.

     ***
         "Khamis..!"

Junaid ya ambata cikin wata irin murya wacce shi kanshi bai san yana da ita ba, a hankali Khamis da ke tsaye bakin gadon ya zubawa bayan Madiha ido, ya juyo da kallonsa zuwa ga bakin ƙofar da Junaid yake tsaye, firgigit Madiha ta farka daga ɓarawon baccin da ya yi awon gaba da ita, Junaid takawa ya yi tare da isa gefan gadon kan locker da ake ajiya ya ɗora ledar, kafin Khamis ya sauke wata irin ajiyar zuciya wacce ta sanya Junaid sake juyowa ya dube shi, Madiha ma duban nasa ta yi cike da mamaki kafin ya kaɗa kai ya fice cike da kunya da kuma gudun abin da Junaid zai iya aiwatar a gareshi domin shi kaɗai ya san abin da ya hango cikin idanuwansa.

        Da kallo suka bi bayansa, kafin Junaid ya dawo da kallonsa ga Madiha yana faɗin.
                    "Kafin ta tashi zamu iya zuwa gida ki ɗauko kayanku."

"Au ba yau zasu sallame mu ba.?"

Ta yi tambayar idonta ƙir akan fuskan Junaid wanda ya ɗauke kansa gefe fuskarsa ɗauke da guntun murmushin da shi kaɗai yasan ma'anarsa, sake gyara tsayuwarsa ya yi kafin ya ce.
      "Kin duba jikinki kuwa?."

Sai a lokacin Madiha ta sauke kallonta zuwa ga shigar da ke jikinta, sannan ma ta ga ashe ko mayafi babu a jikinta, sosai zuciyarta tahau har bawa musamman da salon ɗinkin kayan dake jikinta dake bayyanar da dukkan wani shape nata, gajeren tsaki ta ja tana mai ɗan takurewa gefe, shi abin ma sosai ya bashi dariya kasancewar shi ba ma'abocin dariyar ba ne sai ya yi murmushi, zai sake magana ta rigashi da faɗin.
    
     "Idan ta farka kafin mu dawo kuma fa.?"
          "Akwai masu kula da ita."
Ya bata amsa yana mai juyawa zai fi ce, Madiha ta biyo bayansa da sauri hannunta na rungume a ƙirjinta kai a ƙasa tsabar kunya na yanayin da take ciki, ji take kamar ta nutse ƙasa, amma ba yanda ta iya lalura ce kuma ba ta wuce faɗawa kan kowa ba, kusan a tare suka isa jikin motar tasa da sauri ya buɗe mata ɓangaren mazaunin gaba, yayin da ta kafe shi da ido ya ɗauke kai gefe kamar ma bai san abin da take nufi ba, a hankali ta shiga ta zauna ya mayar da ƙofar ya rufe kafin ya koma ga zagaya mazauninsa ya zauna ya tayar da mota suka fi ce daga harabar asibitin.

"Hankalina yaƙi kwanciya Mama, gidansu a buɗe babu kowa fa."

"Ni kaina a wannan  halin nake Nabila, Allah dai ya kare su da kariyarsa a duk inda suke."

"Amin ya Allah Mama."

"Kinga tashi muje gidan na kakkanta musu shi a kulle saboda samari 'yan bana bakwai."

Mama takai magana tare da miƙewa ta janyo hijab ɗinta dake jikin ƙarfen window ta sanya, Nabila tabi bayanta kasancewar tun da ta dawo daga gidansu Madiha bata cire nata hijab ɗin saboda tsananin tashin hankali.

Tun bayan da suka fara tafiya babu wanda ya ce komai har suka isa cikin layin gidan nasu, can baya ya yi parking motar kamar dai ɗazu kasancewar mota bata iya shiga ɗan ƙaramin lungun nasu, a ƙafa suka taka har ƙofar gidan ya ja ya tsaya kafin ya ce .

    "Na raka ki?."

Kai ta girgiza alamun Aa, kafin y sanya hannu jikin aljihun wandon jeans ɗinsa ya fiddo da waya ya danƙa mata a hannu yana faɗin.

"Haska to."

Wani santsi ta ji ya kwashe hannunta wayar na neman saɓulewa tabi ta da sauri ta riƙo tana fidda ido waje, kau da kai gefe ya yi yayin data fara ƙoƙarin kunna fitilar, abin ya so ba shi dariya amma ya kanne, sosai yarinyar na ba shi dariya da mamaki akan wasu abubuwa nata, hannu ya miƙa mata alamun ta ba shi wayar, a hankali ta ɗora masa akan tafin hannunsa tana mai sake naɗe hannunta a jikinta, dubanta ya yi ƙasa-ƙasa a daidai sanda ya kunna fitilar kafin ya ce.
                    "Idan ta fashe za ki biya ni."
Ido ta zaro waje domin tasan da gaske yake yi, kai ta girgiza kafin ta ce.

FADHEELATUN NISADonde viven las historias. Descúbrelo ahora