FADHEELATUN NISA 16

9 2 0
                                    


FADHEELATUN NISA
  
  16
Mallakin
QURRATUL-AYN.

       
    Da sauri ya miƙe tare da zare wayar daga hannunta, manyan idanuwansa ya waro waje yayin da ya bisu da kallo ɗaya bayan ɗaya, a gaggauce ya yi deleting hotunan bayan ya ajiye mata wayar a gabanta ya koma daɓas ya zauna tare da dafe kansa da hannu biyu wanda ya ji yana sara masa tamkar zai tsinke.
  "Madiha ! Madiha !!."
Firgigit ta waigo ta dubi Hamah dake kiran sunanta, sai a lokacin ta ankare da ruwan hawayen da yake bin kuncinta hannu ta sanya ta share yayin da ta wurgawa Junaid wata irin muguwar harara ta miƙe tsaye tana mai ɗaukar jakarta zata bar wajen, Hamah ta riƙo hannunta tana faɗin.

"Wai lafiya Madiha?."
"Babu komai."
"Kin bar wayar taki."

Wani kallo ta watsawa wayar tabar wajen a fusace, Hamah ta ɗauki wayar tare da duban Junaid kafin ta ce.
    "Me ya faru Junaid?."

Da kallo ya bita, duk iya ƙoƙarinsa na son ɗaga harshensa domin bata amsa abin ya gagara, ganin ba shi da niyar bata amsa ya sanya tabi bayan Madiha wacce tuni ta yi nisa, Sumayya ma miƙewa ta yi bayan ta watsa masa wani magulmacin murmushi ta wuce tare da barin wajen, bin bayanta ya yi da kallo yana ji a ransa tamkar ya shaƙota amma babu damar hakan, ƙwafa ya yi tare da miƙewa ya nufi parking space kamar yadda ya saba a kullum a hakan ya figi motar ya fice, zuciyarsa na tafasa tsabar ɓacin rai.

     "Madiha dan Allah ki tsaya, wai me ya faru ne?."

Juyowa ta yi ta dubi Hamah har sai da ta ƙaraso gareta kafin ta ce.
        "Duba wayar mana za ki ga abin da ya faru, Hamah ta fara ƙoƙarin neman abin tayar da hankali a wayar bata ga komai ba.
     "Ke ban ga komai ba wallahi."

Madiha ta karɓi wayar tana ƙoƙarin nuna mata hotunan, wayam ta gani da mamaki ta dubi Hamah kafin ta ce.
    "Ya goge saboda ya san dole zan nuna muku."

Takai maganar tare da yin ƙwafa, Hamah ta dafa kafaɗarta kafin ta sake maimaita mata tambayar a karo na biyu.
         "Me aka turo miki a wayar?."

A jihar zuciya Madiha ta yi tare da kau da kai gefe kafin ta bata amsa da faɗin.
            "Wasu hotuna ne shi da Lailah, suna kwance.."

Ta yi shiru tana kallon Hamah, Hamah gyaɗa kai ta yi kafin ta ce.

"Na fahimta, amma waye kike tunanin zai turo miki?."

Bata kai da sake magana ba, wayarta ta sake ƙara alamun shigowar message ta whtsApp ɗin ta, duba ɗaya ta yi wa wayar ta miƙawa Hamah tana faɗin.
      "Gashi nan an sake turowa."
Hamah ta karɓa tare da buɗe hotunan ta ƙare musu kallo da kyau, hotuna ne guda uku, Junaid na kwance Lailah ta ɗora kanta akan ƙirjinsa, ɗayan ma har da rungumeta ya yi, abin dai babu wanda zai yi wa daɗin kallo, Hamah ta mayar da kallonta kan fuskar Madiha kafin ta sake jefa mata tambaya.
      "Madiha kina son Junaid ne?."
"Allah ya tsare ni."
"Amma duk wannan fushi da kukan da kike duk na mene ne idan har kinsan ba sonsa keki yi ba?."
"Nima bansan dalili ba."

Hamah ta yi ajiyar zuciya kafin ta ja hannunta tana faɗin.
    "Mu nemi guri sai mu yi magana."

****
  Junaid bai tsaya ko ina ba sai cikin farfajiyar gidansu, ko da ya yi horn mai gadi ya buɗe masa gate bai wani tsaya daidaita tsayuwar motarsa ba bare har ya kasheta ya fice a fusace kai tsaye bangaren Hajiya ya nufa, duk wanda ya kalleshi a wannan lokaci yasan babu lafiya, Hajiya na kwance falo akan carpet ta ji shigowar mutum kamar anjeho shi a firgice ta miƙe zaune tana faɗin.

"Subhanallahi ! Junaid me ya faru da kai?."

Neman guri ya yi ya zauna kan kujera ba tare da ya ce da ita komai ba sai aikin ajiyar zuciya yake yi.
   "Lafiya Junaid Kai da waye?."

FADHEELATUN NISAWhere stories live. Discover now