♥️♥️ SO SANADI💔💔
Episode 1
Yau an tashi da ruwa a garin Jalingo duk wani sako daga lungun gari ruwa ake kamar da bakin kwarya, titin da zai tsada mutum G.R.A daga Yagai ya biyo dodar yana karewa garin kallon, yanayin titin ya burgesa ssai ganin bbu hayanayi, ga ni'imar ruwa, ga sautin kira'ar Fareed Al'abbad na tashi a motarsa a hankali, wayarsa ce ta fara ringing ya kai dubansa gareta Sis Hafsat ce manne a screen din, katsewa yayi ya Kira yana duban hanya.
Cikin sanyin murya ta mishi sallama, ya amsa yana mai limshe idanunsa" Bobbo Sebo ce tace na fada maka Wai don Allah ka biya makaranta ka d'ibo mata yaran nan" yadda tayi maganar da alamun tsoro a tare da ita, baice komai ba ya kashe wayarsa, tsaki taja don yaci daf kwanar da zata sadashi da G.R.A bayan ya wuce Specialist.Kamar Hafsat zatayi Kuka ta isa kitchen ta samu Sebo na faman wanke waken gembu tace" Kinga ko ansawa baiyiba ya kashe wayar, ina tsoro kada ya dawo yayi min fada" tsaki Sebo taja tace" idan ya dawo ya kasheki Hafsat" jiki a sanyaye Hafsat tabar kitchen din ta shige dakinta ta kwanta bbu walwala
Dalibai ne a tare a bakin Al-Iman duba ganin yadda ake dakuwa cikin kananan yayyafi da ake sakanin yaran mata guda biyu, anata ihu " ki daketa Amira, ki daketa Amira" wata dalibace ta fito daga cikin Makarantar da wata Malama, da alama daliban taje ta Kirata ne, Malamar na xuwa ta kama wadda ake cewa Amiran ta janye gefe ta d'ago wacce take kasa ake dukanta tace" yanzu Balkisu dana hanaki binta sanda kika bita, meyasa bakya jin maganane, dubi yadda kika 6ata jikinki mezakije kice a gida" huci kawai take ta kasa cewa komai.
Tun daga nesa ya hangi abunda yake faruwa har ya iso bakin Makarantar, sauke glass yayi yace "Batul kuzo mu tafi" dik suka juya suka dubeshi, da sauri Batul ta shige ciki don ta kira sauran 'yan uwanta, kwace Hanunta Nana tayi daga rikon da Malamarsu ta mata ta nufi bakin Motar a d'an tsorace, ta kama handle na murfin Motar zata bude ta shiga "Idan kika shigarmin Mota sai na karyani wlh" a maganar a tsawace, a tsorace Nana ta sake handle din daman tasan za'a Rina.
Su biyar suka iso wajen Maza biyu mata hudu suka gaisheshi suka shiga Motar, aka bar Nana na tsaye a wajen tana raba idanu kamar an tare kulliya, ganin yana kokarin Jan glass ne ya saka Nana cewa" Don Allah Bobbo kayi hakuri wlh bazan sake ba" kamar badashi take ba yaja glass yaja motarsa yabar wajen, Kuka Nana ta saka gwanin tausayi, dalibai suka dinga dariyarta.
A nutse duka suka fito cikin Motar kowa ya nufi sashin su, Gogan kuma ya nufi part dinsa hankali kwance kamar babu abunda ya faru.
Yusrah iyayen gulma bata wuce part dinsu ba ta shige part din Dada Sare don kai mata rahoto, a kan sallaya ta samu Dada na karatun Al-Qur'ani ta zauna a bakin gado tace" Dada kin san meya faru" tunda Dada Sare taga Yusrah tasan akwai labari don ba'a ganinta banza, gashi ko uniform bata cire ba, cike da natsuwa Dada sare tace" ko fe'i?(meya faru)" nan Yusrah ta kwashe labari ta bawa Dada Sare, limshe ido Dada tayi a hankali tace" jeki cire Uniform dinki yanxu zan tura a daukota" mikewa Yusrah tayi ta fice ranta Kal ta sauke nauyin dake kanta.Babu yadda Malama Aisha batayi da Nana ta shiga Keke- napep ta kaita gida ba taki a cewarta ita sai mota bazata hau adaidaita ba, ana cikin haka ta hangi Motar gidansu, bbu ko sallama ta day Jakarta tazo ta bude Motar ta shiga fuska a had'e.
Batul ce ta shigo dakin da Hafsat ke kwance tace" Anty Adda na kiranki" duban Batul Hafsat tayi tace" waya dawo daku" tsaki Batul taja tace" Bobbo ne, kuma yabar Nana ma a can Makarantar" ido Hafsat ta zare tace" saboda me" dashike Batul ba mai son magana bace tace "Ohoooo nima ban saniba" mikewa Hafsat tayi tabar dakin don amsa Kiran Adda.
"To gashi Allah ya dawo dani, ai ba Motar mutum bace kawai tasan hanyar gidan nan" Nana ta shigo falon tana mita duk jikinta ya 6aci da ta6o, Sebo dake kokarin jona burner ta saka tularen wuta ta dubi Nana tace" naga randa zaki dawo gidan nan normal kamar yadda 'yan uwanki ke dawowa, Nana bazaki yiwa kanki fad'a ba" baki Nana ta tura tace" Yanxu kawai sai na dinga ganin ana tsokanata bazan daki yarinya ba" cike da takaici Sebo tace" ki rufemin baki ko na kaiki wajen Bobbonku" da sauri Nana ta shige bedroom dinta tana mita"ai ku Kuka bashi damar yimin wulakanci son ransa".
Kwance Nana take akan cushion tana kallon "Hayaty" a Abu-dhabi tv hankalinta kwance, tanajin ddin yadda soyayya ke tafiya a film din, Hafsat ce ta shigo falon ta dubi Nana tace" Sebo fah" kamar bazata amsa tace "tana part din Bappa" zama a daya daga kujeran falon Hafsat tayi tace" kin gama assignment dinki ne" tsaki ciki ciki Nana taja ita ta mance da an basu assignment ma, daman tunda taganta tasan sai ta Kira mata ruwa, Rai 6ace Nana tace" na gama" murmushi Hafsat tayi don tasan ko tayi rantsu akan Nana batayi ba bazatayi kaffara ba tace" kawo na duba miki kilan akwai inda kikayi mistake" kamar Nana zatayi kuka ta mike tayi kamar zata shige dakinta ganin Hafsat bata kallonta ne tayi hanya waje ta fice kayanta.
Kai tsaye part na Nenne ta nufa, hannu tasa zata bude labule taji muryan Ya Maher yana cewa" idan na sake ganin kun saka Tv gaba kuna kallo bakuyi assignment dinki ba sai na jimuku ciwo" a hankali Nana ta sake labulen ta koma da Baya a hankali tana kokarin barin part din.
Tunda ya ganta a tsaye a wajen yasan ba abu mai kyau take shukawa ba, yana kallonta tanata Baya Baya, Sarai yasan zata takashi amma yaki matsawa don ya samu hujjar dukanta, aikuwa sai ji Nana tayi ta taka mutum, tana hutawa don ganin wayene taci karo da Bobbo ne, take idanunta suka fito kamar zasu fad'o.
UMMU SUBAY'A ♥️
