❤️❤️SO SANADI💔💔
{so sanadi na zubar da hawayena 😭ba da son raina ba dakai zanyi bankwana✋🏻nai nazari a dare ko ko rana🌗har abada da sonka raina yake kwana💔}
Episode 11
Hafsat ta gama kallon dramanta karfe 12am, sai a lokacin ta tuna da Ja'afar ya fita kuma bai dawo ba, cikin sauri ta shiga dakinta ta dauki waya ta kirashi, yayita ringing bai daga kusan sau 5 tana Kira baya daga, baki ta tabe tayi kwanciyarta.
Ringing wayarsa ne ya tadashi daga baccin da yake, guntun tsaki yaja ya dubi wayar, LOML ne manne a wayar saka wayar a silent yayi ya janye Joy daketa sharar baccinta a kirginsa, ya mike dakyar ya sanya kayanshi ya xari makullanshi da wayarshi ya fice yabar Joy naci gaba da baccinta.
Koda Ja'afar ya koma gida ya samu har Hafsat tayi bacci wanka yayi yaxo ya rumgumeta ta baya, nan kuwa ta farka ta juyo ta dubeshi a hankali tace" ina kaje haka kayi dare" hannu ya saka mata a bakinta alamar tayi shiru "shiiiit dare yayi muyi bacci" bbu musu Hafsat ta kara rumgumeshi taci gaba da baccinta.
Washegari taje breakfast a restaurant kusa da office dinsu, taji ddi ssai data hangi Queen na xauna tana breakfast a wajen, gefe da ita taje ta xauna, Queen ta bita da harara, Ciro wayarta Joy tayi ta Kira promise ta saka handsfree"Kawa ki wuce gidanki don ni banyi breakfast ba yau, kin san duk na gaji wlh, Ja'afar ya gajiyar dani, duk ya xubamin gajiya a jikina" cike da Mamaki Queen ta juyo tana kallon Joy "Ja'afar kuma da Joy, shine ita yace mata ya daina wannan harkan tunda yayi aure, inaaaaaa ai bataci ta xama ba" a dayan bangaren Promise tace" ai naga alama yadda yaxo yanata narke mikin nan" dariya Joy tayi hadda shewa tace" kekam bari kawai wani abun sai mun hadu xakiji" fuuuuuu Queen ta dauki Jakarta tabar wajen cike da haushi, ranta fari kall Joy tayi breakfast dintaMAID
Duban Zahra dake kwance tana latsa wayarta Nana tayi tace" baxaki tashi ki shirya ba, xamu tafi mu barki ai" dariya Zahra tayi tace" ki kyaleni ina hira mai ddi da Mustyna" baki Nana ta ta6e tace" sai kiyita yi ai, mutum kamar aljani ban ta6a ganinsa ba sai uwar suna" dariya Zahra tasa tace"baxaki gane ba wlh, soon xaki ganshi, kuje fah ni bbu inda xani, pls kiyomin tsaraban chocolate" harara Nana tayi mata tace" shi Musty ya turo miki, niba 'yar aikanki bace" Ficewa Nana tayi tabar Zahra nata dariya.
Zubawa Nana Ido Mainah yayi yana kare mata kallo tun daga nesa, tayi mishi kyau ssai, shigarta na dogon rigar atamfa ta burgeshi gashi kayan yayi matukar amsarta, bude Motar Nana tayi ta shige ta kulle, dubansa tayi tareda wankesa da murmushi tace" sorry na ajiyeka koh" shima murmushin ya sakar mata yace" kin Kalli mirror kafin ki fito kuwa" duban jikinta Nana tayi taga meye baiyi ba, ganin komai yayi ne tace" na gani mana meya faru" xuwa yayi daf kunnenta ya rad'a mata "Anya Kinga kyau da kikayi" Nana batasan danda ta saka dariya ba tace" haba dai, kai bakaga yadda kyaunka ke diga ba sai nawa, nasan dole idan muka fita sai an samu crusher's" murmushi Mainah yayi ya tada Motar suka bar gidan.
A ranar Nana tasan tazo Maiduguri sun xagaya Maiduguri ssai, Mainah ya kaita wajen shakatawa da dama ssai, Nana taji ddin wannan fitar, suna dawowa wayarsa ta fara ringing duban Nana dake Shan ice cream yayi yace" Cutie duba min wake Kira" Ciro wayar daga aljihunsa Nana tayi tace" Mimi ce" Dan tsaki yaja yace" yi picking kice mata bana kusa nabar wayar a wajenki" dariya Nana tasa tace " karya fah bbu kyau" hararta Mainah yayi tayi picking, a dayan bangaren Mimi tace "Hello Sweet" baki Nana ta ta6e tace" bashi bane Kuma baya kusa" cike da matsifa Mimi tace" wacece ke" katse wayar Nana tayi tace"Kaii Sweet Girlfriend dinkan nan ta fiya matsifa" dariya Mainah yayi yace" bafa girlfriend dita bace, abokiyar aikina ce and Dad dinta abokin Dad ne" "Amma dai tana sonka" cike da Mamaki Mainah ya dubi Nana yace" meyasa Kikace haka" baki Nana ta ta6e tace "ai kishine ya sakata wannan masifar" shima Mainah baki ya ta6e irin I don't care nan yaci gaba da tukinsa hankali kwance.Cike da damuwa Mimi ta shigo falon Mommy ta xauna kusa da ita, dubanta Mommy tayi tace" Mimi lafiya kuwa" ajiyar xuciya Mimi tayi tace" bbu komai wlh, ina Ya Mainah" harararta Mommy tayi tace" don Allah ki barshi ya huta, weekend ma sai kin dameshi da aiki" yake Mimi tayi tace" ba batun aiki bane wlh" tabe baki mommy tayi tace" ki duba dakinshi mana" kwantar da kanta Mimi tayi a jikin Mommy tace "na duba baya nan" suna maganar sai ga Zahra, da murmushi Zahra ta karaso ta xauna a gaban Mimi tace "Anty Mims me kika kawomin" murmushi Mimi tayi tace" kice na baki aikanda Ya Musty ya aiki miki" dariya Zahra tayi tace "a'a fah" nan suka cigaba da hira Amma Mimi hankalinta baya kansu.
Da sallama Nana da shigo da ledoji a hannunta, Mainah na biyota a baya, Zahra na ganinta ta mike da sauri "oyoyo Anty Nana" dariya mommy tayi tace "to shaxumami, bata shigo da ledoji ba dole ta xama Anty Nana" Duban Mainah Nana tayi kasa kasa tace" idan na cinka daidai wannan itace Mimi koh" duban Mimi data tsaresu da ido Mainah yayi yace" ke ai komai kin sani daidai itace" karasawa cikin falon sukayi, Mainah yaxo ya xauna kusa da Mimi ya mata rankwashin wasa" Hajiya daga ina, ke ko weekend dinma baxaki xauna a gida ki natsu ba" a shagwabe Mimi tace " mommy bakin gansa da cin Zali ba" mikewa Mommy tayi tace" bbu mai shiga tsakaninku, don anjima xaiji kunya" Mommy na karashe maganar ta shige cikin bedroom dinta, duban Nana dake bajewa Zahra tsarabarta Mimi tayi tace" kece kikamin picking na call koh" ba tareda Nana ta dago Kai ta dubeta ba tace" eh nice" yatsina fuska Mimi tayi ta dubi Mainah da hankalinsa ke kan wayarsa tace" ita kuma daga ina?" Dubansa yakai kan Nana yace" daughter Anty Maryam Jalingo ce" nan Mimi ta saki ranta tace" ayyah shine ko kaban labari" ta karashe da bugunsa a kafad'a, ficewa Nana da Zahrah sukayi a falon suka barsu sunata hira, karfin hiranma Mimi ce.
ABUJA
Nuna halin ko in kula da Hafsat ke nuna Ja'afar wajen bukatunsa shi ya sanya Ja'afar komawa ruwa tsundum, duk sanda bukatarsa ta tashi idan yaga Hafsat na mishi kwana Kai tsaye yakan wuce wajen Fannah ko Joy ko Queen hankalinsa kwance, yakan kwana ma a waje don yasan bayada matsala da Hafsat, tun abun baya damun Hafsat har ya shiga damunta yau ta kuduri niyar tambayarsa.
"Wai nikam meyasa kake kwana a wajena" Hafsat ta tambayi Ja'afar dake kokarin Kai abinci baki, sanda yakai baki har ya tauna ya had'iye kan yace" zargina kike kenan" cikin sauri Hafsat ta girgiza kanta tace" a'a kawai tambaya ce" harararta Ja'afar yayi yace" naga ai nike aurenki bakya ke aurena ba da idan na kwana a waje zaki tambayeni" cikin sanyin murya Hafsat tace" nifa ba haka nake nufi ba, kawai naga ya kamata na sani ne don na daina damuwa" kallon renin sense Ja'afar ya mata yace" damuwa? Daman kin damu danine?" Nan idanun Hafsat ya ciko da kwallah kamar xatayi kuka tace" na damu dakai mana Bobbo" cike da takaici Ja'afar ya mike yace" Wai Bobbo can you imagine, My wife calling me Bobbo" tsaki yaja yabar wajen ba tareda yaci ko rabi daga abincin dake gabansa ba, kuka Hafsat ta saka cike da bakin ciki.
MAID
Cikin kankanin lokaci Mainah da Nana sukayi muguwar shakuwa, suna matukar son maganar juna da kula da juna, Zahra kam ta koma gefe ta xama 'yar kallo, yadda al'amarin ke tafiya Kuma Sam baya yiwa Mimi ddi don matsayinta a wajen Mainah ya ragu da Kaso 40% cikin 100%, koda akayi hutu ma kin komawa jalingo Nana tayi don tana matukar jin dadin xamanta a Maid.
"Yarinya bakisan Soyayya bane wlh, shiyasa kike ganin kamar hauka nake" cewar Zahra tana gwada kayanda Mustapha ya turo mata daga London, limshe idanunta Nana tayi jin Zahra ta ambaci soyayya, take Ja'afar dinta ya fad'o mata, murmushi Nana tayi tace" kodai kece bakisan Soyayya ba, ke ai kina son mai sonki ne, ni kuma wadda nakeso bai San ma inayi ba Amma still kullum sonsa ninkuwa yake a xuciyata, wlh Zahra ko numfashina akace na bashi xan iya katsewa na bashi" dariya hadda shewa Zahra tayi tace" ikon Allah, wani mai sa'ar ne ya sacemin zuciyar 'yar uwa ko Ya Mainah ne" murmushi kawai Nana tayi ta janyo pillow ta rumgume tana tuna sweet moments dinsu, batareda ta bawa Zahra amsa ba.
Mainah dake tsaye a bakin kofar dakin yanajin duk abunda suke tattaunawa, yayi murmushi ya juyo ya fasa shigan, Yana mai jin dadi a ransa don gani yake fad'uwa taxo daidai da xama.
Ummu Subay'a ♥️
