episode 4

32 4 0
                                    

❤️❤️ So Sanadi💔💔

Episode 4
Fans na Wattpad rashin comment da vote zai saka na daina posting kwata kwata a Wattpad don Allah a kiyaye

Cike da Mamaki Mujahid ya gama karanta wasikar Batul, shiru yayi nad'an wani lokaci kan ya murmusa yace" yarinta bbu dadi" tashi yayi yaje inda yake ajiye mahimman takardunsa ya ajiye a wajen, yaci gaba da abunda ke gabansa sa'i da lokaci yana dariar wasikar Batul.
Washegari Asuban fari Sebo da Hafsat suka d'au hanyar Maiduguri dakyar Dada tasa Nana taje ta musu Sallama Wai tana fushi dasu, daga nan ta shiga hada-hadarta ta rashin ji ta tsokani wannan ta tsokani wancan, tana shiga part d'in Adda taci karo da Mujahid da sauri tayi baya zata koma ya kirata "Nana zo nan" a d'an tsorace Nana ta karasa shiga falon tazo ta durkusa gabansa kamar mutumiyar kirki tace" afini jam (an tashi lafiya)" bai amsa mata gaisuwar ba yace" kije ki kiramin Batul, kice ta sameni a part d'ina" cike da farin ciki Nana ta mike tace"tooh" tana fita falon ta ruga da gudu sai part d'in Nenne, bata samu kowa a falon ba hakan ya bata damar wucewa kai tsaye bedroom na Batul, bacci ta samu Batul nayi ta haye kan gadon ta kai mata duka a Baya, a firgice Batul ta tashi ta zauna tace" menene Nana" dariya Nana tasa tace" bakiga bacci ba mutumiyar, mikewa zakiyi ki shirya cikin shiga ta kece raini Ya Mujahid yace kije ki samesa a part d'insa" ihu Batul ta saka tace" don Allah mutumiyar" cike da farin ciki Nana tace" bamuda lokacin 6ata lokaci tashi kawai ki shirya" bbu musu Batul ta mike ta shiga wanka, da taimakon Nana Batul ta shirya cikin dogon rigar yadi yayi matukar mata kyau, light make up sukayi Nana tace"iyyeeeeh Mutumiyar kinga kyau" murmushi Batul tayi tace" to rakani muke" kai Nana ta girgiza tace "a'a kije dai kinsan idan ya ganni zaiji kunyar fad'an wasu abubuwan" fari da ido Batul tayi tace hakane" tare suka fita Nana ta zauna a falo Batul ta fice, Batul na fita sai ga Nenne ta shigo ta farawa Nana kallon tuhuma tace "Hajiya Nana ina kika turamin yarinya da safiyar nan" dariya Nana tasa tace" Ya Mujahid ne yace tazo ta rakashi inaga shopping zasuje" murmushi Nenne tayi tace" ke Kuma meya hanaki binsu, bbu natsuwa koh" baki Nana ta tura tace" wlh akwai" dariya Nenne tasa ta shige bedroom dinta tana cewa" naga alama.

Da sallama Batul ta shiga falon Mujahid, bbu yabo ba fallasa ya amsa, murmushi yayi dayaga hadda d'an kwalliyarta, zama tayi a kasa ta gaisheshi, ya amsa yace" tashi ki zauna akan cushion" cike da kunya Batul tace" a'a kasan ma yayi" bai takura mata ba ya tattaro dukkan hankalinsa ya xuba mata, a hankali ya Kira sunanta "Batul" limshe idanunta Batul tayi don yadda ya kira sunan ya mata matukar dadi, bai damu da rashin amsawarta ba yaci gaba da magana "jiya sakonki ya iskeni, na kuma karanta naga abunda ya kunsa, Amma ina mai baki hakuri kiyi hakuri bazan iya soyayya dake ba, bawai don baki kai ba ko akwai abunda baki cika bane No kawai nasan yarinta ce ki d'ibarki, you're just 14 fah, idan kika girma kika mallaki hankalin kanka nasan you will reject me, lokacin zakisan abunda kikeso da kuma abunda yarintarki keso, inaso ki ajiye maganar soyayyar kowa a gefe ki dage da karatu, idan kikai 18 years idan a lokacin zuciyarki ta sake za6a miki ni Mujahid na miki alkawarin zan soki kuma na aureki, but for now bbu batun so ko Batula" da farko bayan nansa sun mata zafi Amma da karshe sai taji sanyi a ranta, Amma tana ganin ko nan da shekara 50 ne shine za6inta"bakice komai ba" Mujahid ya tambayeta, cikin natsuwa Batul tace" Wala kodume(bbu komai) Allah ya kaimu lokacin da Rai da lafiya, nagode ssai da fahimtata da kayi" murmushi ya sakar mata yace" tashi kije" da sanyin jiki Batul ta fice, Mujahid ya bita da kallo yana murmushi yace" nasan wannan duk haukar Nana ce ta ingizata".
"Yaya miyace miki" Nana ta riki Batul data shigo jiki a sanyaye, Kuka Batul ta rushe mata dashi tace" Wai cewa yayi yarinta ne sai nakai 18 sai nazo na fad'a mishi" cike da tausayi Nana tace" kema wayace ki so wannan mugun, kawai ki daina sonshi" "Nana bakisan me nakeji bane, bazan ta6a son kowa ba idan bashiba" Batul tayi maganar tana Jan majina, tsaki Nana taja tace" ni na tsani taurin kai, ai sai ki zauna jiranshi" (hmmmmmm su Nana manyan mata Wai ta tsani taurin kai) Rai 6ace Batul tace"kije na gode Nana, I want to be alone" kwafa Nana tayi tace" basai kin koreni ba zan tafi" ficewa Nana tayi tana mita, Batul ko ta fad'a kan bed ta hau kukan mai cin rai.

                            FCT

Cike da izza, issa, katsaita da kuma takama Ja'afar ya fito daga cikin motarsa na nufi cikin company, fuskar nan a d'aure bbu alamar ya ta6a daria a rayuwarsa, office d'insa ya nufa kai tsaye, jefi-jefi yake amsa gaisuwar ma'aikata kasa dashi, yazo dai-dai zai shiga office d'insa akace "good morning Sir" muryan ta bugeshi amma ya danne xuciyarsa bai amsa ba bai kalleta ba ya shige office d'insa, zama yayi akan kujera ya limshe idanunsa, har ga Allah yayi kewar Joy don she's natural tana biya masa bukata ssai, Queen kuma tasan yadda zata sarrafashi but she's not natural, tsaki yaja ya janyo takardun gabansa ya fara dubawa.

Cike da bakin ciki Joy ta juya xata koma office d'inta, carab taci karo da Queen, harara ta bugawa Queen taja tsaki zata wuce, Queen tayi sautin Shan gabanta tana murmushi tace" Ayyah sorry girl, Queen is always a Queen" dariyar renin wayo Joy tayi mata tace "Joy is always a Joy giver" ganin hankalin mutane na dawowa kansu Queen tayi saurin barin wajen kada labari ya koma kunnen Ja'afar yayi fatali da ita.

Joy na shiga office d'inta ta Kira promise a waya" Promise ya maganarmu ce, Queen naso ta samin hawan jini" a d'ayan bangaren Promise tace" yanxu nake shirin kiranki Dije tace a tura mata pic d'insa don gobe zata Maiduguri" cike da damuwa Joy tace" kaiiii bazan iya sharing na pics nasa ba" tsaki promise taja tace" shikenan ai, tunda sai da pic nasa aiki zaiyi" shiru Joy tayi tana tunani kan tace" Promise are you sure not will happen idan na tura pic nasa, kinsan yaran hausawan nan kada tamin snatching nasa fah" sani dogon tsaki Promise tayi tace" ke Ja'afar ya dama har kike ganinsa wani abu, lemme tell you Dije tafi karfinsa nesa ba kusa ba"ajiyar Zuciya Joy tayi tace" check your WhatsApp zan tura miki" "ok" kawai Promise tace ta katse wayar, badon Zuciyar Joy ya aminta ba ta tura pic d'in Ja'afar.

"OMG, Kawa ina kika samu pic d'in wannan boyfriend material nan" Madonna tayi maganar tana kallon hoton Ja'afar dake wayar Dije, murmushi Dije dake sanya henne a hannunta tayi tace" boyfriend na kawar promise ne, sunaso a kaishi wajen Shanshani ya janyo hankalinsa ya dawo gareta, Nima danaga pic d'in sanda na yaba kawai nasan irinsu basa kula irinmu masu biye biye nan da tuni nayi snatching d'insa" gyara zaman ta Madonna tayi tace" kice daidai nane kawai, kinsan Nima bana biye biye" dariya Dije tasa tace" kina nufin kina ciki kenan" da sauri Madonna ta gyad'a kai tace" of course" jinjina kai Dije tayi tace" lallai Promise suna ruwa, yanzu nakaiwa Shanshani bukatarki ko yaya" tsaki Madonna taja tace" na fad'a miki times without number ni da kyaunka na dogara da kuma Allah bbu ruwana da wani Boka ko Malami, ga zina ga shirka a wani wuta ubangiji zai sakani, barni da zinan kawai ita zan iya dauka, Kinga bara na goge pics d'insa a wayarki ma kasa wata shegiya ta gani tace yanaso, kawai kice musu kinje anyi abun, idan suka sakankance ni kuma sai na biyo ta karkashin kasa na wuce dashi" shewa Dije ta buga tace" daidai ne tawan".






Ummu Subay'a ♥️

SO SANADIWhere stories live. Discover now