7-8

203 5 0
                                    

🌈🌈🌈🌈
             *ABU_MALEEK*
                        🌈🌈🌈🌈

         NIMCYLUV

BOOK 1
PAGE 7-8

Idanun Coach ɗin ne suka fito waje sabida tsananin azaba haɗi da ficewar hayyaci,
Ba ƙaramin shaƙa Abu_maleek ya yi masa ba,
Sabida ko buɗe idanu ba ya iyawa, A.m kam cikin rashin sanin abinda yake aikatawa yay cilli da Coach ɗin gefe guda,
Yana sakin numfashi tare da fesar da iska, gaba ɗaya blue ɗin ƙwayar idanunsa ta rine tai jajirrr tamkar gauta!

Yana dafe bango cikin zafin nama kuma kamar walƙiya ya ɓace daga wajan ɓat, da idanu kawai Coach yabi bayan A.m a ransa yana mamakin wanne kalar Mutum Allah ya haɗasa da shi,
Gaba ɗaya gane inda Abu_maleek ɗin ya nufa wahala ne, kaifi ɗaya ne shi, idan yace zai yi Tabbas zai yi, duk tsayin lokacin da suka ɗauka da Abu_maleek babu wanda ya taɓa ganinsa ya tsaya da wani yana magana irin mai muhimmanci ɗin nan,
Bare kuma ai tunanin friendships bashi da yarda ko kaɗan, gani yake kowa zai iya cutar da rayuwarsa, da alama akwai abinda ya gana masa a zaba a rayuwarsa wanda har lokacin babu wanda ya san menene shi.

Maza na rungome matayensu amma shi wata ƴar farar magensa wacce yake ce mata SWEET, ita ta maye masa gurbin mata, uwa da uba,
Magen zai sanya gaba yay tai mata surutai kuma abin mamaki sosai take iya fahimtar kurman baƙin nasa,

Abu_maleek bai son ihu yanzu zaka hargitsa masa tunaninsa bare kuma ka sashi gaba kace zakai masa faɗa, yana da wani Ɓoyayyan hali wanda har yanzu babu wanda ya samu nasarar gane wane hali ne Abu_maleek yake ɓoyewa wanda bai son kuma a gani? Yana da saurin ɗaukan zafi da kuma saurin yanke hukunci shiyasa baya shiga sabgar duk da bai shafesa ba.

Ajjiyar zuciya Coach ya sauke tashin hankali kuma tsantsa ya bayyana a saman fuskarsa, yanzu yaya zai yi? Da wanne ido duniya zata kallesa? Musamman yanzu da kowa ya saka wa wannan babban wasan nasu ido, idan ta tabbata Chelsea sun ciye ƙwallayen ina ya dosa to? Abu_maleek shine hope ɗinsa, cikin sauri ya juya tare da shigewa cikin Stadium ɗin idan da yiyuwar ɗaga ball ɗin sai ai masa alfarma amma abu ne mai wahalar gaske.

A hankali yake tafiya yana haɗe hanya kamar ɗan shaye-shaye, daya rufe idanunsa zai fara ganin wani tsuhun tarihi yana gilmawa cikin ƙwayar idanunsa,
wanda tunusa a yanzu dai-dai yake da bugawar zuciyarsa, hannunsa dafe da goshinsa dake tsastsafar da gumin wahala,
Duk mutanan da suke hanya sai sun tsaya sun kallesa cike da mamaki domin sun san ko waye,
Wasu ma waya suke ɗaukowa suna masa vedio da picture, domin babu wanda ya taɓa ganinsa haka without his guards.

Yana tafe a tsakiyar titin yayinda ya kejin gaba ɗaya duniyar na juya masa a wannan karan ko idanunsa baya iya gani, a dai-dai kuma tsakiyar kan titin ne kuma wata mota tazo da mahaukacin gudu gaba ɗaya tayo kansa,
Cikin ikon Allah, motar ta tsaya cak wata ƙyakkyawar Badurwa ce a ciki sanye da ƙanan kaya masu matukar kyau da kuma ɗaukar idanu, idanunta manne cikin wani tafkeken glass,
Ganin Abu_maleek a gaban motar ta yasa ta saki baki With much surprise ta shiga kallon A.m domin kallo ɗaya tai masa ta gane wanene!

Amma mamakin ganinsa ya kasa barinta ta tabbatar ce eh lallai shi ɗin ne da gaske ba wani ba,
Ganin jini na zuba a gefen kansa dalilin buga kansa da yay daga jikin bango yasa tai saurin buɗe ƙofar motar ta fito,
Tana zuwa ta nufi inda yake tare da leƙa farar ƙyakkyawar fuskarsa tace.

"Sir Are You okey? The you need some help?"
Ta jera masa tambayar lokaci ɗaya!
Ganin mutum kusa dashi yasa a hankali cikin rashin sanin mene yake aiwatarwa ya shiga miƙa hanunsa yana ƙoƙarin kama hannun budurwar da niyyar kare kansa daga faɗuwar da yake ƙoƙarin yi,
Ganin haka yasa budurwar saurin matsawa gabansa Musamman da taga few people suna kallon su, ita kam abin farin ciki ne a gareta da kuma ci gaba a ganta da Abu_maleek mutum mai zarrah,
Wanda sai ka shafe shekaru baka gansa ba indai ba'a t.v ba.

ABU MALEEKWhere stories live. Discover now