11-12

247 7 1
                                    


BOOK 1
PAGE 11-12

         *INA MARA BA DA WANDA ZA'A TALLATAWA HAJARSA (BUSINESS)*


Baƙin zanan dake saman ƙirjinsa, zuwa ƙasan cibiyar sa, gaba ɗaya zanan wanda akai da baƙin abu ya mamaye ilayin farar fatar cikinsa,
Sai ya zamana kamar anyi masa zanan Tattoo ne,
A duk lokacin daya buɗe idanunsa yaga zanan sai yaji zuciyarsa ta halba tare da buga masa da ƙarfi,
Yana samun kansa cikin ruɗu haɗi da fargaba,bai san lokacin da zanan ya kasance a jikinsa ba,
Shi dai ya buɗe idanunsa yaga zanan,
Menene shi? Wane yay masa gaba ɗaya bashi da masiyyar komai,
Amma yana ji a ransa Tabbas akwai Ɓoyayyan abu game da wannan zanan,
Shiyasa baya taɓa bari wani ya gani,
Duk da cewa baya son zafi da kuma manyan kaya amma yana ƙoƙarin ainun wajan ganin ya bawa zanan kariya,
Lumshe idanunsa yay tare da cafko laɓɓensa na ƙasa wanda ya gama jiƙewa da ruwa ya shiga tsotsa tare da cijawa,
Ƙuri yaywa zanan da gajiyayyun idanunsa masu kaifi da sanya mutum cikin firgici,
Shi kansa a wannan lokacin yana son ya fahimci zanan menene? Amma duk yadda yakai dan son fahimta baya gane komai na jikin zanan,
Sai kuma baƙin zanan ya ƙara haska farar jikinsa, ya zama kamar wani adoo ne a jikin masa musamman shi da yake tare da turawa,
Cikin nutsuwa haɗi da kamewa ya miƙa hannunsa tare da ɗaukan bathrobe ya sanya jikinsa tare da covering ƙirjinsa sosai,
Idanunsa a lumshe lashes ɗin nan zara-zara, sai ɗigar da ruwa suke ga girar a cike baƙa sosai da ita.
Yana fitowa ya nufi dressing mirror yana daga tsaye ya ɗauki wani lotion mai kyau da ƙamshi ya shafa, sabida garin sosai yake da sanyi,
Yana gamawa ya ɗauki body spray ya fesa saman fatarsa,
Sai kuma ya ɗauki handrayer ya shiga gyara sumar kansa, ya shafa oil a ƙwantaccen sajansa,
Nan da nan kyau da kuma haibarsa haɗi da cikar zatinsa suka bayyana yay wani mugun kyau like takeaway,
Wata red ɗin Armless ya ɗauka wacce take da zip daga gaba amma yay unzipping rigar, sai hula red daya ɗauka ya sanya saman sumar kan nasa,
Ta rufe iya saman gashin banda wanda ya kwanta can ƙasan wuyansa,
Yasubuhanallah! A.m ya zama wani damn cute are extremely ɗin nan,
Long wando sleeves ya sanya wanda ya kasance blue black,
Yana gamawa ya juya walking slowly ya nufi Parlo hannayensa sanye duk cikin aljihu, duk da cewa sanyin bai damunsa amma yana jin yadda tsigar jikinsa ke tashi,
A Parlo ya samu sweet kwance saman 3seater tana bacci duk ta cure waje guda,
Tattausan Murmushi ya saki wanda iya saman laɓɓansa ne kawai, gently kuma ya nufi wajan deep freezer ɗin dake Parlon ya ɗauki zallar madarar shanu mai ɗan zafi kasancewar yau setting ɗin freezer,
Yana ɗaukan madarar shanun ya cire tankar Inibi guda ɗaya a hankali cike takun ƙasaita ya juya ya zauna kusa da kitty ɗinsa.
Daɗi da garɗin madarar ya haddasa masa rufewar idanuna ba tare daya shirya ba, sosai yake son madarar shanu tana ƙara masa kuzari musamman idan ta kasance zallar ba haɗi.
Idanunsa ya rufe sabida murɗawar da cikinsa yay, a hankali ya shafa cikinsa wanda ya kusan haɗewa da bayansa,
Daga can outside kowa wanda maid ɗin hotel ɗin ce ta shiga danna blet ɗin door ɗin tana jiran permission,
Taɓe baki yay kana ya Marai-raice fuska kamar wanda aka tilastawa magana yace.
"Come in"
Tuni daman ya buɗe da remote a hankali take turo table breakfast ɗin nasa,
Ko inda take bai kalla ba, sai rufe idanunsa da yay ya haɗe rai sosai,
Ƙasa tayi da kanta tace.
"Sir! Breakfast is ready"
Shiru yay mata ita kuma ganin hakan ya sanya ta ƙara maimaita wa idanunsa a rufe yace.
"Out"
Da sauri ta juya zata fita Murya can ƙasa yace.
"Come and pick your jagwalgwalo"
Yana faɗin haka ya miƙe tare sanya hannunsa ya ɗauki sweet kai tsaye art room ɗinsa ya shiga,
Ya ɗauki pen da different colors a hankali ya fara zanan idanunsa a lumshe a haka yake zanan,
Yana gamawa ya buɗe idanunsa dai-dai lokacin sweet ta farka ƙuri yaywa zanan yana kwaɓe fuska ya ɗauki sweet ya rungome tare da faɗin.
"What I'm did? Mace na zana ko namiji? Why kai babu gashi but ƙirji yay the same dana mace mai...,"
Da sauri ya shiru yana ƙara kallon zanan shikam duk sanda ya rufe idanunsa yay zanan abinda yake zanawa kenan ya rasa wacce kalar halitta ce macace ko namiji kullum kuma idanun a rufe suke mikewi yayi tare da rungome sweet wacce take ƙara shigewa jikinsa.

ABU MALEEKWhere stories live. Discover now