9-10

168 6 3
                                    


BOOK 1
PAGE  9-10

Cafkar gashin kanta, sabida tsananin zafin daya ratsa jijiyoyin kan Julde ya sanya bata san lokacin data saki wani gigitaccen ihu tare da fasa ƙara da dukkan ƙarfinta,
Wanda hakan ya ƙara haddasa juyewar blue ɗin Idanunta wanda suka gama rinewa da jaaa sabida azabar da tayi mata yawa.
Baya Arɗo yayi cikin matuƙar jin daɗi da kuma farin cikin yau ya kama ɓarauniyar da take shiga cikin garken shanun har take samun damar tatse masa madarar shanunsa,
Zabura yay cikin son dukiyarsa da kuma son bawa dukiyar tasa kariya yace.
"Billahi Yaron nan ya kashe mu, madarar shanu ƙwarya biyu, dole ai masa hukuncin da yafi wannan, dole sai kayi mana kiwon shanu na mako biyu"
Da Zallar mamaki Lamiɗo ya tari numfashin Arɗo yace.
"Tayaya ne wannan ƙaramin yaron zai iya kiwon Nagge wajan guda 100?"
Murmushi Arɗo yayi yana mai jinjina kansa domin shi kaɗai yasan dalilin daya sanya yace haka,
Ba tare daya bada waccen amsar ba cikin bada umarni ya ƙara cewa.
"Cire sumar nan yanzu wannan kuma shi ne hukumcin ɓarawon madarar shanu, barin irin wannan a Rugar Mahinjo babban hatsari ne, domin cigaban faruwar hakan zai iya kawo daƙoshewar tattalin arziƙin  Fulani makiyaya, kunfi kowa sanin cewa wannan shanun sune arziƙin dukkan wani ɗan Rugar Mahinjo,
Da kuma madarar shanun muke samun kuɗaɗan kula da wasu dukkan Nagge da suke ƙarƙashin kulawar mu"

Cike da fahimta kowa na wajan yay na'am da maganar Arɗo, domin yay amfani da abu mafi suyiwa a zuciyar fulanin wato shanunsu,
Babu wani abu dake baƙanta ran Fulani makiyaya irin nakastuwar shanunsu.

Lamiɗo ya jinjina kai tare da murmusawa, shi kaɗai shima yasan dalilin daya sanya Arɗo faɗin hakan,
Da ƙarfi kuma ya ƙara jan sumar kan Julde wacce har yanzu ya kasa kama ƙarshen sumar sabida tsayin da gashin yake dashi,
Ganin yadda Julde take ihu tare da ƙoƙarin fisgewa zata gudu yasa Arɗon Rugar Mahinjo faɗin.

"Ɗaure shi, maza kawo igiya a ɗaure wannan mugun irin"
Julde numfashinta ne ya kusa ɗaukewa sabida sabon tashin hankali,
Ita burinta a yanzu ta koma wajan Yakumbonta bata san halin da yunwa ta sanya ta a halin yanzu ba,
Da rarrafe taja Jikinta ta shiga lalubar inda take jiyo muryar Arɗo, duk da cewa bata gani amma tana iya bin sautin Muryar mutum ta isa inda yake.

Tana zuwa wajan Arɗo ta rirriƙesa tare rushewar da wani irin raunataccen kuka mai tarwatsa zuciyar dukkan wani mai imani da kuma tausayi,
Kuka take wanda yake nuni da irin hali ƙunci da kuma takurar da take ciki,
Kuka take da dukkan ƙarfinta zuciyarta, kuka ne wanda yake nunawa duk wani Mutumin dake wajan irin halin yunwa da kuma ƙishin da suke ciki ita da Yakumbo,
Kuka ne wanda yake nuni da halin ƙazantar da suke ciki domin rabonta da wanka a rayuwa harta manta,
Balle ai maganar gyaran jiki duk da cewa da fulanin daji irin su ba'a san so da haka ba.
Cikin muryar da kuka ya gama cin ƙarfinta tace.

"Kayi mini rai Arɗo, ka taimaki rayuka biyun da basu da wani mataimaki sai Allah, dan Allah kada ki cire min sumar kai ma, za'a min dariya kuma zan zama abin kallo da ƙyamata wajan mutanan Mahinjo,
Kaimin dukkan wani hukunci amma ka janye maganar cire min sumar kai, Ni macace ne, kada kuyi abinda zaku mai dani ta namiji,
Ban taɓa sata ba, yanzu halin yunwar da muke ciki ne yasa Ni fitowa neman abinda zan bawa Yakumbo,
Dan Allah Arɗo ki taimaka kada yunwa ta kashe shi, kada yunwa ya kashe Yakumbo, ka bani madarar ko kaɗan ne na bashi yasha"

Zame ƙafafuwansa Arɗo yayi yana ƙara kallon ƙyakkyawar fuskar Julde wacce take masa kama da wata halitta,
Kallon JULDEN kuma na ƙara ta fasa zuciyarsa, yana san yashi tuno da wani shuɗɗaɗan tarihi wanda tuno sa a yanzu dai-dai yake da bugawa zuciyarsa,
Cikin ɓacin rai yasa ƙafa tare da hankaɗe Julde wacce ta kasance bera a Rugar Mahinjo bata da kowa sai Yakumbo da Madibbo,
Da sauri kuma Lamiɗo yazo ya fisgi gashin kanta ya fara janta jikin wata bukka,
Gaba ɗaya mutanan Mahinjo suka mara masa baya domin suma a lokacin cike zuciyoyinsu suke da tsanar Julde wacce take shirin ganin bayan tattalin arziƙin su,.
Wani tsuhu kowa tuni ya koma gefe ya kuka wiwi, sabida a jikin shanuwarsa Julde ta tatsi nono, gashin Naggen tana da ɗauke da tsohun ciki wannan dalili ya ƙara tayarwa da tsohun hankali a tunaninsa shike nan Julde ta kashe masa abinda yake cikin shanuwarsa.

ABU MALEEKWhere stories live. Discover now