19-20

544 22 1
                                    


BOOK 1
PAGE 19-20

 

    *Feedyn Bash* osí pámí lèriñ lànà😂, emi kinshè *Yoruba* fa, *Hausa* pànbélé nimí, so fún *Bassh* pé aro rén somí.


Sama da rigar jikinta, tare da ƙoƙarin kunce igiyar da aka ɗaure mata ƙirji da ita.
Wani masifafan ihu Julde ta sanya, saboda tsananin tsoran daya shigeta,
Ta shiga kare ƙirjinta da dukkan hannayenta, Jikinta duk rawa yake, cikin rawar murya da gigita tace.
"Waye kai? Me kake so? Noi indema?"
Ta jera masa tambayar lokacin, saboda jin wanda ya Shigo ɗin yayi shiru,
Gashi yana ƙoƙarin yi mata tsirara, Barkido kam tuni ya fara fidda numfashi yana sakin Ajjiyar zuciya saboda santala santalan cinyoyinta da suka bayyana,
Duk da cewa warin dauɗa take amma hakan bai hana cinyarta yin wani kyau ba,
Ganin tana shirin bashi wahala kawai ya sanya hannunsa tare da kama kanta ya gwarata da bango,
Wani gigitaccen ihu ta sanya lokaci guda kuma jini ya ɓalle daga goshinta ya shiga zuba yana sauka zuwa saman fuskarta,
Kafin ta sulale a wajan babu numfashi, wani irin Murmushin jin daɗi yay kana ya miƙe ya shiga ƙoƙarin zame kayan jikinsa,
Da wani irin sauri Barkido yaja baya tare da ɓoyewa a bayan ƙofar bukkar, hakan ya faru ne saboda jiyo Muryar Madibbo yana faɗin.
"War Julde, Hai kazo kana ina?"
Ya faɗa yana leƙawa tare da ƙarasawa inda ya hangi Julde kwance dafe da ƙirjinta babu numfashi,
Da wani irin saurin gigita Madibbo ya ƙarasa shiga cikin bukkar tare da nufar inda Julde ke kwance,
Yana shiga Barkido ya fita da sauri yana Murmushin jin daɗin babu wanda ya kansa.
Jawo Julde yayi jikinsa yana jijjiga ta tare da kiran sunanta, ganin ko motsi ba tayi yasa Madibbo faɗin.
"Ko dama ta maa?" (Meke damunki?"
Da sauri kuma ya kwantar da ita tare da fita da sauri ya nufi inda yake ɓoye, Ɓoyayyan Sirrin da yake ɓoyewa Julde daman irin wannan ranar yake jira,
Wacce ta tazo ya faɗa Julde komai dake faruwa Wanda bata san shi ba.
Yana fita ya nufi can wata ƙuryar duhuwa duk da cewa dare ne Amma haka ya shiga cikin duhuwar tare da haƙe ƙasar ramin daya ɓoye abun.
Yana gama tunuwa ya miƙe da sauri tare da fara tafiya ya nufi cikin Rugar,
Murmushi Arɗo da Lamiɗo sukai, a hankali kuma Arɗo ya saki wani zabgegen Maciji dake hannunsa zuwa ƙasa,
Kai tsaye macijin kuma wajan Madibbo yayi saboda yaga gilmawarsa,
Sosai Madibbo ke sauri domin ya isa ga Julde ya faɗa mata shuɗɗaɗan tarihin daya huce kafin Zuwan wannan ranar.
Kamar daga sama yaga saukar Macijin a gabansa yana sara kai tare da fiddo da harshen bakinsa, ya shiga wa yiwa Madibbo tsartuwa,
Wani irin kyarma jikin Madibbo ya ɗauka, gashi ya kasa koda mutsawa, tsoro da gigita suka cika masa zuciya.
Wani irin tsalle Macijin yayi tare da.

   *Daga wannan page ɗin na gama free pages, sabida halin rashi da ake ciki na raba tsarin biyan gida biyu, 500 for VIP posting safe da yamma, 300 for nrml grp, posting idan anyi yau babu gobe👏🏻 via 0116886423 sulaiman Naima s union bank evidence of payment 08119237616*

Sarawa Madibbo bakinsa a dai-dai satin ƙahon zuciyarsa, nan take kuma Madibbo ya faɗi yana fitar da wata iriyar kumfa daga cikin bakinsa,
Kullin abinda ke hannunsa wanda yake son faɗawa Julde ya ƙwace daga hannunsa tare da faɗuwa ƙasa,
Ɓat kuma kamar Aljani Macijin ya ɓace daga wajan,
Kakarin mutuwa Madibbo ya fara idanunsa ya shiga lumshe bakinsa ɗauke da sunan JULDE,
Arɗo da Lamiɗo ne suka ƙarasa inda yake kwancan tare farayi masa dariya,
A hankali kuma Lamiɗo ya ɗauki kullin ba tare daya buɗe yaga ko menene ba, ya cilla kullin sama,
Kana sukai gaba Abunsu cike da farin cikin samun nasarar raba Madibbo da ransa,
Bakinsa ɗauke da salati Ubangiji ya amshi ran Madibbo.
Sanyin safiya mai cike da dadɗar iska ne ya farkar da Julde daga suman da tayi,
Wata ƙaƙƙarfar ajjiyar zuciya ta sauke, tare da runtsa idanunta wanda suka kumbura saboda kuka, ga kuma rashin wadatacciyar lafiya da idanun yake da shi,
A hankali ta miƙe zaune tare da kifa fuskarta a tsakanin zuciyoyinta ta saki wani irin raunataccen kuka!
Hakiƙa tana buƙatar mataimaki a rayuwarta, amma waye zai zama gatanta? Waye zai zama Garkuwa a gareta? Waye zai zama tubalin da zai gina mata sabuwar rayuwa harta mata da wannan rayuwar da take mata ƴanci?
Waye zai zama Muradin ranta? Wanda zai zama madubi abin haska zuciyarta? Ko dai TABI ABINDA ZUCIYAr take faɗa mata ne?
Kuka take mai cike da ladamar rayuwa ƙunci kuma da baƙin ciki,
Ganin bata da wani gata sai Allah, bata da wanda zaice mata tayi shiru ya sanya ta sassauta kukan tare da ɗaukan sandar ta, ta shiga laluban hanya idanunta na ɗan juyawa,
A haka ta samu ta fita daga cikin Bukkar hannunta ɗauke da ruwa,
Can bayan Bukkar ta tsuguna tare dayin fitsari kana tayi alwala ta koma bukkar tare da gabatar da sallah bayan ta yane kanta da wani siririn abu.
Tana idarwa ta fara jin surutai bata motsa ba, sai da taji ana faɗin Madibbo ya mutu, kusan mutuwar tsaye tayi, jinta da gaba ɗaya ya ɗauke, bugawar da zuciyarta take ya ɗan tsaya na wasu daƙiƙo,
Farkawa tayi ta kanta kwance ashe tun a lokacin ta suma sabida trumer ɗin data shiga.
Yini tayi kuka babu abinda ke tsayar da ita sai Sallah, daman sallar ba wata iyawa tayi ba sosai, bare kuma ta iya yiwa mamaci addu'a,
Haka ta ƙara kwanciya bacci banda ruwa babu abinda yake cikinta,
Ji take kamar itama tamar Duniyar ko zata huta, idan tana da rabon jin daɗi a lahira sai ta samu,
Washe gari da safe, Arɗo ya sanya wasu mutane zuwa su tafi da ita, kwallon ta Arɗo yayi yace.
"Wato kai yaron nan bakaji ko? Haii sai da ka sake sace mana nonon nagge ko? Gashi dalilin hakan ka sanya Nagge ya mutu"
Jikin Julde ya ɗauki rawa, domin ba zata mance da cin zarafin da akai mata na aski ba, ga azabar da aka gana mata na murje mata nono,
Kuka ta sanya ta shiga rarrafawa duk da bata ganin kowa amma a haka ta ƙarasa gaban Arɗo tare da riƙe masa ƙafa tace.
"Kayi min rai Arɗo, kada ko sake murje min nono, da ƙyar nake numfashi saboda abinda kuka sanya Min, Aradon Allah ban saci komai ba"
Da sauri Lamiɗo yace.
"Arado ƙarya ka, Arɗo zai maka ƙarya? Da kanshi ya ganka kana tatse mashi nono, dole ka kiwata mana Nagge guda ɗari bisa abinda ka aikata"
Zuciyar Julde ta buga da ƙarfi Tayaya zata iya kiwo? Tayaya ne zata iya kula da Nagge guda ɗari?"
Gaba ɗaya wajan suka sanya ihu akan dole Julde tayi masu kiwo ai tana sandar ganin hanya,
Arɗo ne yayi gyaran murya yace.
"Maza ki haɗa mana Nagge guda ɗari a fito dasu daga garke yanzun nan, kuma kada ka sake a rasa guda ɗaya idan hakan ya fara to walle kai ma saika matu"
Allah sarki baiwar Allah bata da wata mafaka dole tabi abinda sukace mata,
Yin kiwon ma zai sanya tana samun abinci ci,
Haka ta tisa Nagge guda ɗari a gaba zuwa daji, tana dafe da ƙirjinta da yayi mata wani irin nauyi, da ƙyar take jan numfashi,
Tana zuwa wata ƙorama taja ta tsaya tare da kwanciya wajan ruwa ko taji sauƙi daga azabar da ƙirjinta yake mata gaba duniyar tayi mata zafi,
Ajjiyar zuciya ta sauke tana ƙara riƙe ƙirjinta a haka wani wahalallan bacci ya ɗauke ta.

ABU MALEEKWhere stories live. Discover now