RUƊIN ƘURUCIYA 1

441 16 0
                                    


RUƊIN ƘURUCIYA


PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P. W. A

*Story and written by*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

Writer of

WATA KISSAR..(Sai mata)
ABDUL JALAL
AƘIDATA (paid book)
WUTA A MASAƘA
NOW RUƊIN ƘURUCIYA (paid book)





Free pages are not much, subscribe for ₦300 only.
Contact 07063065680 for more information

Page 1

Harabar makaranta ce babba sosai, ɗauke da manyan ajujuwa, da dogayen ƙawatattun benaye, wanda suka sha tiles, a kowane aji yana ɗauke da na'urar sanyaya guri, ko ina ƙal ƙal babu datti ko ƙazanta, kallo ɗaya zaka yiwa ɗaliban dake zirga zirga, da ita kanta makarantar kasan cewa tabbas duk ɗan dake wannan makaranta, ɗan masu ido da kwalline, ko wanda ya tsaya masa ya tara masu gidan rana.

Ɗalibai mata sanye suke da shuɗin skirt me cizawa ga mata, maza kuma wando, se farar riga 'yar ciki me dogon hannu, se kuma 'yar saman kalar skirt ɗin, se ƙaramin farin hijabi ga musulmai mata, saka ƙaramin hijjabin ma ra'ayi ne, babu tilas saka shi ga ɗaliban, da yawa ɗalibai matan skirt ɗin nasu iya gwiwa ne, wasu kuma da kaɗan yafi gwiwar su, da yawansu Uniform ɗin nasu sun matsesu matuƙa, kuma galibin ɗalibai mata suna cire rigar saman kayan su bar ta cikin suna yawansu.

Da yawa masu wannan shigar, za kaga matasan 'yan matane, da suke kan tashen balaga, gasu 'yayan gata, dan haka suna ɗauke da ƙirane me matuƙar kyau da ɗaukar hankali, haka ɓangaren ƙananan yaran ma da suke firamare, wasunsu kansu ko ɗan kwali babu, kai kace makarantar ƙasashen ƙetare ne, saboda yanayin tsarin makarantar da ɗaliban da ke ciki.

Ɗaliban sunata hada hadarsu, sun fito break, wasu na ciye ciye, wasu wasanni wasu kuma suna hira, ƙararar sautin jiniyane ya karaɗe ilahirin makarantar, wanda hakan ke nuna lokacin komawa aji yayi, domin cigaba da ɗaukar darasi.

Nan ɗaliban suka shiga komawa cikin azuzuwansu, dan cigaba da ɗaukar darasi.

Gaba ɗaya makarantar tayi tsit, an koma aji, dan tuni wasu sun fara ɗaukar darasi ma.

wata tawagar ɗalibai maza da mata ce ta ɓullo harabar makarantar, a ƙalla sun kai su goma, suma sanye da Uniform suna tafe suna hirarsu suna ƙoƙarin bin wata baranda dan komawa ajin su.

Wani malami ne yai musu tsawa da harshen turanci "hey, from where are you? "

Wata zaƙaƙura a cikinsu ta kalli malamin cikin iyayi tace. "we went out for breakfast"

'who gives you the permission to go out? Don't you know that you supposed to be in your classes by now?"

Malamin ya sake maganar cikin tsawa.

Wani ɗan kyakkyawan saurayi ne a cikinsu ya ɓata rai sosai, ya kalli malamin Yace "No need to seek permission from anyone, we have the right to go where ever we want at any time to have our break, we are semifinalist, and the teachers have to wait for us to come back, because our parents pay for it, hope I made myself clear?"

Cikin zafin rai malamin Yace "Are You stupid?, is this the way you supposed to talk to me? Semi finalist ɗin banza, me ka taka a harkar karatu da kake gayamin wai You Are semi finalist"

Matashin ya ɗage kafaɗa alamar oho maka, sannan Yace "it seems that you are New here, anyway this is our policy you have to go and know more about it"

RUƊIN ƘURUCIYAWhere stories live. Discover now