RUƊIN ƘURUCIYA 13_14

89 5 0
                                    

🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️

RUƊIN ƘURUCIYA

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P. W. A

*Story and written by*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

Writer of

WATA KISSAR..(Sai mata)
ABDUL JALAL
AƘIDATA (paid book)
WUTA A MASAƘA
NOW RUƊIN ƘURUCIYA (paid book)

_Labarin RUƊIN ƘURUCIYA, na iya zuwa da wani salo, wanda baku saba ganinsa a rubutuna ba, hakan ya biyo bayan akan abunda aka gina labarin, wani abun ze ɓoyu wani Abun baze ɓoyu ba sakamakon labari ne akan teenegers, yara masu tashen Balaga, but hakan ba ya na nufin na sauka daga kan tsarin yadda nake Rubutu bane, ƙofata a buɗe take dan karɓar ƙorafi, gayra ko shawara_

⚠️⚠️⚠️ƘIRƘIRARREN LABARI NE, BAN YADDA A JUYAMIN SHI TA KOWACE SIGA BA SEDA IZININA ❌❌‼️


13-14






A tare Khairat da Sadik suka juyo suna kallon Nana, dake tsaye tana musu kallon banza.

Khairat tace "is this girl serious?"

Sadik yace "A beg forget about her, she's mentally abnormal"

"Nima na gani"

Cikin tsiwa Nana tace "Wallahi Inna ta hana, tace babu kyau, kwata kwata babu kyau irin wannan abun, amma kai kuma kazo kana taɓata, tace marasa tarbiyya ne suke haka, kuma Allah ze fushi da mutum, Allah ya hana amma ka ke aikatawa, wallahi se na gaya mata"

"Dan ubanki tsayuwar me kike a gurin baki tafi gayamatan ba? Kifi ruwa gudu banza da baki kamar mazirari"

"Kaine banza bani ba wallahi"

Ta juya ta tafi ɗakinsu da sauri dan ta sanar da Inna.

"Innarmu, Inna" ta shiga ƙwalawa Innan kira.

Inna tace "Ya akayi meye kike kirana haka?"

Se kuma Nana tayi saroro ta kasa Magana, kawai ta basar tace "kawai nemanki nake"

"Dan kina nemana seki biyoni da wannan kiran Kamar wata sa'arki?"

"To yi haƙuri"

"Naƙi haƙurin"

Nana ta ɗan sosa kai, ta nemi guri ta zauna.

A yanzu Kusan duk lokacin da Sadik ze shiga gida ya haɗu da Inna, se tai masa faɗan wani abun, kodai na sumar kansa, ko rashin son mutane, ko kuma taɓara, saboda haka yana dawo wa daga makaranta, yake ficewa yawon sa baze dawo ba se dare, se ya tabbatar da Inna tai bacci, se ya shigo ya ɗau Abincin sa ya fice ya bar falon, in ma Mother ze gani ya ganta a lokacin.

Wasu lokutan da ya fara ɓuruntu ze ɗau Abinci Nana ke farkawa daga bacci, ta fuskanci baya shigowa se kowa yai bacci, dan haka ta sa ido sosai ta lura be zo ɗaukar abinci da wuri ba, dan haka ta gane se daren ze zo ya ɗauka.

Har sun kwanta bacci, Nana ta daidaici Inna tai bacci, ta miƙe cikin sanɗa ta fito falon, ta janyo ƙofar falon ta rufe, ta kulle da mukulli ta ciki, ta nemi guri ta kunna TV tai zamanta tana kallon cartoon.

Wajen sha ɗaya da rabi na dare, Sadik yazo yana murɗa ƙofa ze shigo dan ya ɗau Abinci, amma yaji a rufe gam.

Ya jinjina ƙofar yaji ta a kulle, nan ya shiga ƙwanƙwasawa, nan ma ba wani respond.

RUƊIN ƘURUCIYAWhere stories live. Discover now