CHAPTER 2

158 8 0
                                    

RUƊIN ƘURUCIYA

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P. W. A

*Story and written by*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

Writer of

WATA KISSAR..(Sai mata)
ABDUL JALAL
AƘIDATA (paid book)
WUTA A MASAƘA
NOW RUƊIN ƘURUCIYA (paid book)

_Labarin RUƊIN ƘURUCIYA, na iya zuwa da wani salo, wanda baku saba ganinsa a rubutuna ba, hakan ya biyo bayan akan abunda aka gina labarin, wani abun ze ɓoyu wani Abun baze ɓoyu ba sakamakon labari ne akan teenegers, yara masu tashen Balaga, but hakan ba ya na nufin na sauka daga kan tsarin yadda nake Rubutu bane, ƙofata a buɗe take dan karɓar ƙorafi, gayra ko shawara_


Page2

Sadik na fita harabar gida, ya tarar abokansa sunzo wai zasu snuka, ya bisu suka fice dan yaje ya sarara.

Corper Nazir kuwa ya sha faɗa a gurin director, saboda ƙararsa da Sadik ya kai, ya dinga mamakin wannan lamari, shikenan dan yaran masu kuɗine baza'a basu tarbiyya ba? Yara duk ba ɗa'a? Ai makaranta ba iya gurin koyon karatu bane, hadda tarbiyya shikenan se a zuba musu ido su lalace, baza'a tsawatar musu ba dan kar iyayensu suji haushi?

Abun ya dameshi sosai, Tare da ganin rashin ma'anar wannan lamari akwai buƙatar a duba, idan bahaka ba rayuwar yaran zata ɓaci a banza.

Da wannan damuwar ya koma gidan daya kama, da yake ba'a camp yake a zaune ba, gida ya kama yake zaune a ciki.

Washegari ya shirya Domin zuwa makaranta, kamar kullum anyi assembly an gama, Farhan nata rarraba ido taga ta ina zata hango Sadik, sedai bata samu ganin nasa ba, ta duba inda yake tsayawa amma baya nan, duk setaji ta damu, haka aka sallamesu suka tafi azuzuwansu.

Sadik kam yau makara yayi sosai, corper Nazir yana harabar makarantar a tsaye yana zazzagawa, dan tabbatar da komai ya tafi daidai.

Motar gidansu Sadik ce ta kunno kai cikin makarantar, har Corper Nazir ze shiga cikin makaranta, yaga zuwan Sadik, dan haka ya tsaya.

Sadik ya fito daga mota, ya rufe motar ya saɓa jakarsa, ze shiga cikin makarantar.

Cikin shouting corper Nazir yace "hey come here'

Sadik ya juyo ya kalleshi, sama da ƙasa kamar kar yaje, sukuma yaje kiran, yana wani bossy walking yaje inda Nazir yake tsaye, Nazir ya kalleshi yace "why are you just coming?"

Sadik ya kalleshi ya ɗauke kai.

"Check your watch, what's the time now?"

Sadik ya ɗauke kai kamar ba dashi ake magana ba, principal ne ya taho inda suke tsaye, yana faɗin"what's going on here?"

Nazir Yace 'Sir, wai Babu wani penalty na makara kowani laifi, idan yaran nan sun karya doka? Kalli lokacin da yazo makaranta, kuma na yiwa director magana akan haka amma ya nuna min is like you don't punish them"

Principal ya kalli Sadik yace Yace "Sadik, why are you late? Baka san lokacin da Yakamata kazo school bane?"

Tura baki Sadik ya shiga yi, yana hararar Nazir.

PC yace "idan ka sake makara, sena baka punishment me wahala, ɗau jakarka ka bar gurin nan kafin in ci mutuncin ka"

Sadik ya ɗau jakarsa fuuu yai cikin makarantar, yana tunanin yadda ze koyawa Nazir hankali.

RUƊIN ƘURUCIYAWhere stories live. Discover now