RUƊIN ƘURUCIYA 15_16

100 6 1
                                    

         🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️

RUƊIN ƘURUCIYA

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P. W. A

*Story and written by*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

Writer of

WATA KISSAR..(Sai mata)
ABDUL JALAL
AƘIDATA (paid book)
WUTA A MASAƘA
NOW RUƊIN ƘURUCIYA (paid book)

_Labarin RUƊIN ƘURUCIYA, na iya zuwa da wani salo, wanda baku saba ganinsa a rubutuna ba, hakan ya biyo bayan akan abunda aka gina labarin, wani abun ze ɓoyu wani Abun baze ɓoyu ba sakamakon labari ne akan teenegers, yara masu tashen Balaga, but hakan ba ya na nufin na sauka daga kan tsarin yadda nake Rubutu bane, ƙofata a buɗe take dan karɓar ƙorafi, gayra ko shawara_

⚠️⚠️⚠️ƘIRƘIRARREN LABARI NE, BAN YADDA A JUYAMIN SHI TA KOWACE SIGA BA SEDA IZININA ❌❌‼️

     

                            15_16


Suka sake kwashewa da dariya gaba ɗaya.

Farhan kuwa har gaban mota ta raka Sadik, ya kalleta yace "shigo mu tafi mana"

Ta girgiza masa kai tace "A'a, na ga ba ka jin daɗi, gara ka tafi gida da wuri, Allah ya sawwake"

Ta miƙa masa jakar sa tai gaba, Sadik ya bita da kallo yana lumshe ido, a hankali ya koma ya jingina da seat ya rufe idanun sa, babban burin sa be wuce ace ya mallaki Farhan ba, abunda yake ji game da ita yana neman yafi ƙarfin sa gaba ɗaya.

Farhan ma har ta tafi hanya tana tunanin Prince, ba ta san meya same shi haka wanda ya sa shi shiga wannan yanayin na damuwa sosai ba.

Ko yana cikin damuwa idan ya ganta ya kan saki ransa, yai ƙoƙarin ɓoye damuwar ta sa, amma yau kam ya gaza ɓoye damuwar tasa gaba ɗaya.

Da wannan tunanin taje gida, ta tarar da Umma suna cin Abinci tare da ƙannen ta, duk sun sanya Uniform ɗin islamiyya, suna hira Umma nata dariya, amma Farhan na sallama ta haɗe rai, ta dena dariyar da take.

Ta kalli Umman tace "Umma na dawo"

"Sannu" shine kawai abunda Umman tace.

Farhan ta shiga ɗakin su ta ajiye jakar ta, ta canza kaya ta fito ta shiga wanka, bayan ta kammala tai salla ta shirya cikin Uniform ɗinta na Islamiyya ita ma, ta fito da niyyar cin Abinci, sedai tasan za'a kwashe wa kowa Abinci idan baya nan a adana masa, amma ita kuwa nata sedai ta tarar da shi a tukunya ya sandare.

Haka ta zuba Abincin ta shiga ɗakin umman nata ta zauna tana cin abinci.

Tana son tai hira da Umman, amma babu fuska sam.

Umman Farhan cikakkiyar ba fulatana ce, gaba da baya, kuma Farhan ita ce 'yarta ta fari, bisa ga al'adar Hausa fulani kuwa, dama ɗan fari ba'a jansa a jiki saboda kunya, sedai idan uwa tana da wata yaya wannan 'yar fari ko ɗan fari ya riƙi 'yar uwar uwa a matsayin uwa.

Sedai Umman Farhan ba ta da Yaya mace ko ƙanwa, duk se maza gashi ba'a gari ɗaya suke ba, dan haka abubuwa suna bawa Farhan wahala.

Wasu lokutan ta kanji a ranta anya kuwa Umma ce ta haifeta? Saboda abun ya wuce alkunya, abunda take mata tamkar tsana ne, har gara kwanan nan ta kan yadda su zauna a guri ɗaya, amma a baya ko zama tai a guri Umma ba zata zauna ba.

RUƊIN ƘURUCIYAWhere stories live. Discover now