Episode One-The beginning and end of me.

78 2 0
                                    




Episode One:The beginning and end of me.

Zuciya!,Annabi yace wata tsoka ce ajikin mutum,wacce idan ta gyaru to dukkan sauran jiki ya gyaru,idan kuma ta ɓaci,dukkan jiki ya ɓaci.Zuciya itace sarauniya ajikin ɗan Adam,wacce alokuta mabanbanta take gudanar da mulkinta a bisa son kai, musamamn idan mamallakin zuciyar baya iya juyata,ya sakar mata ragamar komai,zuciya itace muhallin imani, tsoron ALLAH dakuma son ALLAH.

Alokuta mabanbanta idan na duba rayuwata,ina farawa ne daga lokacin da iyayena suka rasu,daga lokacin da na rasa komai nawa,nazama marainiya mara gata da galihu, idan na waiwaya baya,Rayuwata ta ƙare ne adaidai lokacin dana rasa iyayena,tun daga wannan lokacin,tun daga wannan rana,narasa farin cikina,na rasa hope,na rasa confidence Da strength Dina, nacigaba Da rayuwa bisa turbar da zuciyata ta ɗorani akai,na kasa yadda da ƙaddarar data afku agareni ta rashin mahaifana.

Misalin ƙarfe bakwai da rabi ne na Safiyar Monday,cikeda hanzari nake kammala breakfast,jikina Da zuciyata na ɓari,duk da raina a ɓace yake,wanda hakan ya zame min jiki,dariya ta ƙauracewa fuskata,domin banga dalili dakuma amfanin yinta ba, saida nagama jere abinci a dining sannan cigaba da gyara Kitchen din,Kamar kullum yau ma jiki ba ƙwari na fito daga Kitchen jiki na a mace, ina kallon Arabian style staircase din gidanmu Wanda Daddy ke saukowa,yana ɗaga ƙafa daƙyar yana saukewa cikeda izza da gadara, jikinshi sanye da wata milk colour getzner wacce ta sha aiki,fuskar shi ahaɗe babu rahama acikin ta,ganin shi ne ya ƙara gudun bugawar da zuciyata keyi,nayi saurin saukar da kaina ƙasa ina jiran saukar aradu,Alhaji Mu'az ƙanin babana ne uwa ɗaya uba ɗaya,shine ya cigaba da riko na bayan rasuwar iyayena,zamana a ƙarƙashin Daddy na shekaru biyu na fuskanci ƙalubale kala daban daban, akullum ina kukan rashin iyaye domin na rasa masu sona dakuma ƙaunata,na rasa wanda zan kalla naji farin ciki ko kuma ya sani farin ciki,zama ne wanda akullum nake ɗanɗanar zafin rasuwar iyayena,daga bayan shi mommy ce ke saukowa tana sakin ƙaramin Murmushi,wayarta ƙirar Iphone 13promax na sakale Da kunnanta, waya takeyi da  ƴarsu Heekmah wacce take karatu a Surrey University dake London.

Cikeda girmamawa dakuma ladabin da iyayena suka koyar dani na durƙusa kamar kullum, gwiwowina biyu aƙasa,bakina daya bushe saboda rashin samishi abinda zaiyi hydrating dinshi nace

"good morning daddy,fatan ka tashi lafiya".

baice komai ba illa kallon banza daya watso min,wanda hakan ya zame min jiki,domin idan da sabo na saba, Daddy yayi min tsanar ban mamaki domin tsanar babana ce ta dawo kaina,na tabbatar idan aka baiwa daddy bindiga zai iya harbe Ni, shiyasa hakan bai wani dameni ba na cigaba da cewa"anan zaka ci abinci ko a dining?".

Cikin Muryar shi mai sa mara jin magana nustuwa, Muryar shi ta kololuwar tsanar Asma yace"ɓace min da gani,bana son ganinki,ki ɓace min da gani kafin na ɓarar dake".

yafaɗa cikeda faɗa,hawayen baƙin ciki masu zafi ne suka zubo min,saina miƙe ahankali nayi hanyar ɗakina jiki ba kwari,ko tsaya rufe ƙofar banyi ba na zube aƙasa sabon kuka yana kufce min,hotunan iyayena wanda suke barbaje akan gado.na ɗauka ina kallo cikeda tsantsar so dakuma ƙauna,ko sau ɗaya ko amafarki ko a tunani ban taɓa zaton akwai ranar dazan gani irinta yau ba,mai cikeda tsantsar bakin ciki da tashin hankali, haƙiƙa mutuwa bata min adalci ba,ta ɗauke min mamana Da babana alokaci ɗaya,rasuwar da zafinta ke ƙaruwa acikin zuciya ta,rasuwar data sha banban da saura,Hausawa sunyi gaskiya mutuwa mai tonan asiri ce.

Bayan Asma tabi da kallo tareda sauke wayar daga kunnenta, tace"kadaina tsangwamar ta haka nan,shiyasa take tsallake tarkon dakake ɗana mata,na daɗe ina faɗa maka,ka canza salo,ka jawo ta ajiki ta yarda dakai,kasa ta aminta dakai,kasa ta tabbatar wa kanta kaine zaka bata kariya,da amintar datai maka zaka buga mata saran ɓoye kamar yadda kayiwa iyayenta shekaru biyu dasuka wuce,baka kaini tsanar Asma ba,dan haka yadda nace ayi haka za'ayi daga rana mai kama ta yau".

ASMA...Where stories live. Discover now