Episode Two: Affairs of the Heart.

21 2 0
                                    




Episode Two: Affairs of the Heart.

   Sassanyar ajiyar zuciya ya sauke alokacin da idanunshi suka sarƙe acikin na Kiki,tafiya take cikeda yauƙi jikinta sanye da white top da dogon crazy pencil jeans black color,hannunta na dama riƙe da files, yayinda na hagun ke riƙe da wayarta ƙirar Iphone 13pro Max,Tsayuwar shi ya daidaita yana ƙara kallon fuskar ta,wacce take fitar da yalwataccen Murmushi,saida ta ajiye files ɗin sannan tayi taku biyu backward tabashi wata kyakkyawar hugg,ajiyar zuciyar dabai shirya ba ya sauke even though ko riƙe ta baiyi ba,hasalima hannayen shi na rungume asaman ƙirjinshi,bakin ta mai girma wanda yasha nude lipstick ta ɗora asaman kunnen shi tace"good morning starshine,the Earth says hello"tareda manna mishi light kiss akan ears ɗin.

Yace"morning"tareda ɗaukar file ɗinda ta ajiye,saurin riƙe hannun shi tayi,tace"baby you look pale,meyake damunka? bakada lafiya ne?".samun kanshi yayi da cewa"I'm just overthinking akan mafarkin danakeyi these days". Yafaɗa with his well arranged extra white teeths,ƙamshin breath taking mouth wash ɗinshi mai ƙamshin gaske yasa ta lumshe idanu sannan tace"karka damu,komai zai wuce,we should be more prayerful"cikin aminta da maganar ta yace"thank you".tareda komawa mazauninsa ya zauna,a kujerar dake opposite dashi ta zauna tana duba himilin files din dake jiran shi,and from all indications mafarkin na damun shi,miƙewa tayi tsam ta zagaya inda yake, tare da zama akan laps ɗin shi,hannayen ta dogaye wanda suka sha zirconia ring tayi cupping fuskar shi,tana kallon shi cikeda tsantsar tausayi,ƙauna, girmamawa da kuma mutuntawa,tace"bari na tayaka Aikin".bai ce komai ba illa kallon ta daya cigaba dayi kamar wani gaula, hannunshi na dama ta riƙo Wanda yake fari tasss,mai tsananin taushi da santsi,pen tasa mishi ahannun Sannan takama hannun nashi (kamar yadda ake koyama yara rubutu)haka tariƙa buɗe files suna signing papers ɗin da Yakamata,wanda bai kamata ba kuma su ajiye a gefe,duk da ita ke jan ragamar aikin amma He's very focused akan papers din,sunyi masu yawa kafin daga bisani ta ajiye pen din ta waiwaya tana kallon fuskar shi wacce take ahaɗe kamar hadarin gabas,cikin rashin son halin dayake ciki tace"baby Please,ka cire abunnan aranka, Focus on me and your work,munfi muhimmanci agareka koba haka ba?".

Gyaɗa kai yayi asannu yace"kiki koda nayi ignoring ɗin shi,yana matuƙar damuna, saboda jikina yana bani babban al'amari ne". tace"bazan yafe ma wannan mafarkin ba tunda yana sa ka cikin damuwa,i want you to worry about nothing and be happy forever".

Yace"You too". yafaɗa Da cute pink lips ɗinshi ƴan madaidaita masu shegen kyau,da kallo tabi lips ɗin tana haɗiye wani miyau mai ƙarfi,wanda da daƙyar ya iya wuce mata,tana bala'in son James,so na bugawa a jarida,irin son daya ke mamaye zuciya,domin bata ganin komai da kuma kowa sai shi, tana son tayi tasting bakin shi,tana son sun kasance tare da juna,amma takasa gane kanshi, domin ko sau ɗaya bai taɓa bari hakan ta faru ba,kamar ba namiji ba,duk wata seductive kwalliya babu wacce batayi but to no avail, ahankali take kokarin manne lips ɗinsu, bayan ta yi dabarar riƙe hannayen shi,tana sakar mishi wasu looks wanda suka daskarar dashi awurin,lips ɗinta na ƙasa ne ya haɗu da nashi na sama,atake sukaji wani electrification,ya runtse idanu tare da fizge hannun shi ɗaya ya yi shunning kiss din as usual,sosai hakan ya ɓata mata rai,duk ba ba yau bane karo na farko dayake mata hakan,amma na yau ɗin yafi tsaya mata arai sannan yafi mata takaici,saide yadda take bala'in son shi baze bari ta iya faɗa mishi magana ba,haka nan sonshi baze bari ta ɓata mishi rai ba.

Dan haka saita miƙe tana gyara zaman jeans ɗinta,wanda ya fito da Asalin figure 8 dinta,wanda suke madaidaita,bai kalli gefen datake ba domin ya tabbatar da biyu takeyi.batareda tace komai ba ta fita daga office din,lumshe idanu yayi yana jin wani abu na tsarga mishi tun daga maɗigar kanshi har tafin ƙafafuwan shi, cappuccino coffee as usual ya haɗa yana kurɓa da zafin sa, domin shine ke ɗebe mishi kewa akodayaushe.

Afusace ta koma office ɗinta,wanda yake akusa dana James,takalli Daniel cikeda ɓacin rai bayyananne sannan tace"lafiya?meya kawoka office ɗina?". ƙaramin Murmushi yayi sannan yace"nazo ne na duba ki, fatan kina lafiya".

ASMA...Where stories live. Discover now