Episode Five:Dilemma

18 3 0
                                    





Episode Five: Dilemma

     Cikeda tsantsar ɓacin Rai Daddy ya kalli gefen da Mommy ke zaune yace"har Barr Umar Faruk ya isa yafaɗa min wannan maganar? Maganar banza da hofi akan dukiyar ɗan uwa na?saboda yaya bai ɗauke ni abakin komai ba ina raye ya barma Asma dukiyar shi gabaɗaya?".Saboda bai ɗaukeni da muhimmanci ba ay ni Yakamata ya damƙawa komai nashi tun yana raye,shine ni aka barni Da wahalar riƙe ƴa (Asma)wanda zaici tagomashin alherin dukiya daban,toh Wallahi tallahi bazai taɓa yiwuwa ba,saina yi ma Barr Umar Faruk abinda bai taɓa zato da tsammani ba,da mu'az yake magana".

Da mamaki mommy ke kallon fuskar daddy tana tunanin yadda gabaɗaya ya fita daga cikin nutsuwar shi har ma da tunanin shi,ya zama summun bukumun baya ji baya gani, asanyaye tace"banda abin ka ay dukiya ta Asma ce,haka ALLAH maɗaukakin Sarki yace,duk da inada ƙarancin sani a ɓangaren addini amma dukiya gadon Asma ne tunda mallakin mahaifinta ce,ƙarfa-ƙarfa kawai zamu mata,yanzu miye abinyi?".

Saida ya watsa mata kallon banza sannan yace"yazama dole Asma ta ƙarbo dukiyar ta ahannun barr Umar Faruk,Zan tursasata akan hakan".wani guntun Murmushi mommy tayi sannan tace"Alhaji kenan,bai zama dole tayi abinda kake so ba musamman tasan cutar da ita zakayi,shiyasa tun akaron farko naso mu nuna mata soyayya,yadda bazata taɓa kawo komai acikin ranta ba zata bamu dukiyar hankali kwance,amma ka ɓata komai tun akaron farko, karka manta Asma ba shashashar yarinya bace, sannan kuma ba doluwa bace,tanada matuƙar wayau da saurin ɗago mutum,komai zaka ce mata yanzu bazata aminta ba,saboda ka nuna mata tsantsar ƙiyayya,tun shigowar ta gidan mu bata ƙara farin ciki ba, kullum acikin baƙin ciki take kwana take tashi,kana ganin zata yi abinda muke so? musamman akan dukiyar ta?".

Dogon tsaki daddy yaja sannan yace"ita ɗin banza,Ni dana kara da ubanta kuma saida naga bayanshi balle ita banza abanza, Matsala ɗaya ce nake hangowa,itace ta yadda Barr Umar Faruk zai bada dukiya,amma ƙwacewa ahannun Asma ba wani abu bane shi yafi komai sauƙi ma".

Cikeda rashin gamsuwa mommy tace"gabaɗaya babu sauƙi acikin lamarin nan,shiyasa naso Salman ya auri Asma,kaga hankali kwance zamu yi ma dukiyar handama da babakere".

Daddy yace"wannan baya cikin tsarina,bazan bari ɗana ya aure ta ba Saboda wasu dalilai".
Tace"wasu dalilai ne?"
"Idan kika zurfafa tunani akan wannan lamarin,koda Salman ya aure ta bazata canza zani ba, sannan bazamuyi yadda mukeso ba,so nake na ɓatar da ita a duniya, labarin ta yazama tarihi kamar yadda na iyayenta yazama shekaru biyu dasuka wuce".
Murmushi mommy tayi tace"Allah yabamu nasara."

Sai ya zuba mata idanu yana kallo nawani lokaci kafin yace"dole muyi hakuri sannan mu jajirce kafin mu cimma nasara, babu abinda zaizo ya samemu na alheri muna zaune batareda mun tashi tsaye mun nema ba,akan wannan qudurin nawa zakiga abubuwan ban mamaki,wanda baki taɓa zato da tsammanin zan iya yinsu ba,amma karki damu nasara tamu ce".

Gyara zama tayi tareda fuskantar shi sosai tace"kamar me me kenan? Yakamata fa na riƙa sanin plans dinƙa kafin ka aiwatar, karka manta Ni ce jinka da ganin ka idan baka nan".

Dariya wacce take nuna tsantsar mugunta yayi sannan yace"ku mata ƙaramar ƙwaƙwalwa gareku,idan nafaɗa miki plans ɗina kanki bazai ɗauka ba,Gara dai ki riƙa ganin actions, sannan wanda ya kamata ki sani kafin faruwarsu zan sanar miki Insha ALLAH".

Riqo tausassan hannunshi tayi wanda suke shan manicure akai akai tace"akan wannan qudurin namu,ina mana fatan alheri dakuma fatan nasara,idan dukiyar mu tazo hannu,zaka zama very powerful Da babu wanda ya isa ya ɗaga maka ƴatsa,kamar yadda yayanka yazama akarsar nan, akullum banda burin daya wuce naga kazama babba fiyeda yayanka".

Ya murmusa kaɗan sannan yace"jannatid duniya"yana kaima hannun ta peck, sannan yacigaba da cewa"rayuwata batareda ke ba tamkar makaho ne acikin duhu yana lalube,kece haske na masoyiyata ALLAH ya kara tabbatar da zaman lafiya tsakanin mu".

ASMA...Donde viven las historias. Descúbrelo ahora