GIYAR MULKI

72 8 0
                                    

*GIYAR MULKI*
True life story

*MALLAKAR: Zainab muhmd Chubaɗo*

*_Da sunan Allah mai Rahama maijin ƙai, salati da ɗaukaka su tabbata ga manzon tsira Annabi muhammad (s.a.w). Ya Allah kai ruƙo da hannayena tun daga farkon wannan littafi har zuwa ƙarshensa 🤲_*

*Eid Mubarak to all Muslim's ummah Allah ubangiji ya karɓi ibadun mu yasa muna cikin bayin da aka ƴanta a cikin watan Ramadan🤲*

*_GIYAR MULKI gajeran labari ne, wanda baze wuce 3 pages zuwa 4 ba insha Allah, labarine wanda ke ɗauke da wani babban al'amari me matiƙar karya zuciya, amma ba lallai ku fahimci hakan ba har sai kun kasance a cikin tafiyar😊 idan kinsan kinada saurin kuka irina pls don't read it don wllh zaki zubar da hawaye_*

*Wannan littafin Sadaukarwa ne ga IYAYE MATA, waƴanda suka jure wahalar mu tun daga ciki har zuwa girman mu, Allah ya saka muku da mafi girman alkhairi duniya da lahira😀*

01

___A shekarar 1980 data gabata a cikin jihar Bauchi cikin ƙaramar hukumar Toro, Wata magidanciyar macece ɗauke da ƙaton cikin tanata murƙususu a saman tabarmar dake shimfiɗe a ƙaramin tsakar gidanta, bakajin tashin komai sena sautin muryarta dako fita batayi sabida Azabar ciwon Naƙuda. Ta jima a haka tun tana iya juyawa har ƙarfinta ya fara ƙarewa, amma a haka ta sake yunƙurawa cikin yanayi na ƙarfin hali, dason fafutukar ganin ta haifo abinda ke cikinta lfy, bu kamar wasa seda ta shafe Awa tara tana Abu ɗaya sannan Ubangiji ya Sahale mata haifo abinda ke cikinta. Wanda ya kasance ɗa Namiji

Tasha matiƙar wahala sannan ta Samu kanta a dai-dai wannan lokacin Mijinta Malam Muntari ya shigo gidan a matiƙar gajiye, ganin Matarsa Talatuwa a yashe ƙasa tana maida numfashi, gefanta kuma ga jariri Sabuwar haihuw yana tsala ihu yasa ya jefar da ƙaramin buhu da fatanyar dake hannunsa ya isa gareta, ganin har lokacin cibiyar yaron na jikinta ba'a yanke ba ne yasa ya fita da sauri zuwa gidan dake maƙotaka da nasu, ya kira wata kamilalliyar mata wadda bazata wuce shekaru Talatin da bakwai ba (37), Anai mata laƙabi da Hansatu unguwar Zoma, kusan a tare suka shigo gidan shida Hansatu, cikin ƙanƙanin lokaci ta taimaka mata ta yanke cibiyar, tareda sanya zani ta ɗauki Yaron lafiyayye dashi se faman harba ƙafa yake yana tsala kuka. Murmushi Hansatu Tayi a lokacin data kalli Fuskar Yaron wanda ke sauke numfashi a hankli, sannan ta miƙawa Malam Mutari shi tace "Malam riƙeshi bari in taimakawa Talatuwa ta gyara jikinta."

Washe Baki Malam Mutari yayi annurin dake kwance a saman fuskarsa yana ƙara yalwatuwa yace " to Hansatu bari in shiga dashi ciki kafin ki gama kimtsata sabida kar sanyi ya kama yaron." dariya Hansatu Anguwar zoma tayi a ranka tana mamakin Halin Malam Muntari

Cikn gajeran lokaci ta gama gyara tsakar gidan tsaf, sannan ta jiƙa toka ta wanke tsakar gidan yay fess dashi ba ƙarnin jini ko kaɗan, inda kasan ba'a gurin akai Haihuwar ba, nan ta haɗa wuta ta ɗora mata ruwan zafi a babbar tukunya wanda ita Talatuwar zatyi Wanka dashi, Muntuna talatin ne suka ɗauki Ruwan ya tafasa.

Nan ta juye mata shi a wata kwatanniyar Roba takai mata makewayi, seda yaɗan sha iska sannan ta taimaka mata suka isa Banɗakin, Sosai Ta gasa mata jikinta ciki da waje, sannan ta ɗaura zanin suka fito tare A bakin ƙofar ɗakin suka tarar da Malam Muntari sai faman safa da marwa yakeyi da jaririn a hannunsa, Murmushi Hansatu unguwar Zoma tayi tareda kallon Malam Muntari tace "Malam duk zumuɗin ne haka, naga har yanzu kana rungume da yaron baka ajiyeshi ba, kodai bazakai kunyar ɗan-fari dashi bane?"

Murmushin dake saman fuskarsa malamMuntari ya faɗaɗa fiyeda farko yace "ko ɗaya Hansatu wannan ɗan bazanyi ɗan fari dashi ba, sabida yanda nakejinsa a kusa da zuciyata, kinga kuwa ni bazan taɓa bari kara da kunya su hanani jan ɗana a jikina ba." malam Muntari yay maganar yana maida kallonsa ga fuskar yaron, wanda ke tsananin kama dashi tamkar yayi kaki. Itadai Talatu Murmushi kawai tayi don bata kasance a cikin jerin mata masu yawan surutu ba. Awa ɗaya dayin Haihuwar matan Unguwa suka fara shigo mata barka, kasancewarta mace me kirki da karamci ga kowa.

GIYAR MULKIDonde viven las historias. Descúbrelo ahora