final chapter

27 6 3
                                    

GIYAR MULKI
(true life story)

             Page  02
     (The final chapter)

_______Kamar yanda ya faɗa kuwa hakance ta kasance, miƙewa yay a hanzarce dedai wannan lokacin Matarsa Hajiya Bintu ta shigo falon, cikin shiga irinta alfarma ganin shigowarta yasa Alhaji Shamsu ya dakata yana me Jifanta da wani rikitaccen kallo me tsayawa a Rai. Wani nannauyan fasali yaja don har cikin Ransa yakejin hajiya Binta na ƙara mamaye lungu da saƙon cikin zuciyarsa, komai tayi burgeshi takeyi, wasu lokutan idan tana gabansa ba ƙaramar shagalta yakeyi da shauƙinta ba.

Ba komai ne ya sama mata wannan kimar a idanunsa ba face zallar tsaftarta da son adonta, babban abinda yafi komai jan hankalinsa a tareda ita shine ni'imtaccen ƙamshin dake tashi a jikinta a ko wani lokaci, wannan yafi komai tafiya da imaninsa a tareda ita. Cikin yanayi na jan hankali ta iso gabansa se faman karairaya takeyi, cikin salo da jan hankali takai hannunta saman ƙirjinsa tana shafawa tace "Gwamnan gobe ya na ganka haka kamar akwai abinda ke neman ɓata maka rai ne?"

Murmushi ya saki cikin wani irin yanayi me cike da ɓoyayyiyar soyayya yace "Bari kawai Gimbiyar mata, nida wani amintacce na ne amma karki damu ganinki kaɗai ya share min ɓacin ran dake Zuciyata." wani ƙayataccen Murmushi ta saki sabida yanda kalamansa sukai mata daɗi , wani irin fari tayi da idanuwanta, tamkar yarinyar ƴar shekara Ashirin da biyar. Harta buɗe baki zatayi magana kira ya shigo cikin wayarsa dake ajiye cikin aljihun wandon Farar shaddar dake jikinsa.

Cikin wani kasalallen yanayi ya sanya hannunsa ya ɗakko wayar yana bin lambar dake yawo a saman fuskar wayar da kallo, tabbas ko duniya zata tashi baze taɓa manta mamallakiyar wannan number ba, da kamar baze ɗauka ba amma kuma seya ɗaga wayar tareda karata a samn kunnensa na hagu, se faman ɗaure Fuska yakeyi kmar wanda akaiwa Dole.

Cikin kamilalliyar muryrta wadda ke ɗauke Amo irin na manyantaka Talatu tace "Me sunan Yaya....."

Shiru yay mata yaƙi cewa komai hakan yasa Talatu ta saki Murmushi me sauti tace "Duk sabida ina inai maka togaciya da rudun Giyar Mulki yasa ka shafe tsahon shekaru baka zo ka ganni ba shamsu? Kada ka manta fa duk duniyar nan baka da wanda yafini, hakan yasa a matsayina na Uwa nake jiye maka tsoron Ranar da zaka tsaya a gaban Allah akan haƙƙin mutanan da kake wakilta, Shamsu har kullum ina gaya maka cewar mulki Bala'i ne, mulki Masifa ce, mulki Jidali ne, amma ko so ɗaya baka taɓa ƙyamatarsa a zuciyarka ba, sabida yanda ka tsunduma a cikin shan Giyar Mulki wadda har yanzu jirinta ya gaza sakinka. Banayi maka fatan komai sena alkhairi Me sunan Yaya, Amma ina me ƙara jaddada maka cewar duk rintsi duk wuya kada ka taɓa bari Mayan son Mulki yasa ka Rabu da Imaninka...."

Takaici ne ya cika masa zuciya, don haka yasa hannu ya janye Hajiya Binta dake jikinsa ya fara magana cikin ɓacin rai "waike Talatu don Allah meye matsalarki ne? Ubanwa ya gayamiki cewar inacin haƙƙin mutane dazaki sani a gaba kinata gaya min magana? Shikenan kuma dan kin haifeni seki samu damar dazaki dinga faɗamin duk maganar datazo bakinki? Toni gaskiya banason karan tsaye a lamari na, don haka don girman Allah kiji da kanki babu Ruwanki da rayuwata...."

Shiru Talatu Tayi kmar Ruwaya cinyeta sabida wani tuƙuƙin baƙin ciki dayazo mata wuya ya toare mata maƙoshi,wata ƙwallar ɓakin ciki da takaici ne ta fara tsatsafowa a tsakiyar kwarmin idanunta, bugun zuciyarya ne ya fara tsananta, ga wani ɗaci da yawun bakinta ke mata tamkar wadda ta tauna icen maɗaciya, bata ankara ba taji wasu zafafan Hawaye masu matiƙar Zafi suna kwaranya a saman fuskarta......

Bakin zanin Atamfar dake jikinta tasa ta goge hawayen tareda ƙoƙarin dedaita nutsuwarta, murmushin ƙarfin hali ta ƙaƙalo kamar yana gabanta tace "Kayi haƙuri ɗan nan, karan bani ne kawai irin nawa, na ɗauka cewar wannan Shamsu dana ɗauki cikinsa a jikina ne tsahon wata goma sha biyu da ƴan kwanaki ne, shiyasa nayi tunani idan nai maka nasiha zakaji ni, tunda har hakan laifine a gareka don Allah kayi haƙuri Ɗan nan, Ubangiji yay maka Albar......."

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: May 14 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

GIYAR MULKIWhere stories live. Discover now