Arba'in da takwas

99 11 0
                                    

🌍🌍🌍🌍🌍🌍

     *RUƊIN DUNIYA!*

🌍🌍🌍🌍🌍🌍

*NA_NAFISAT ISMA'IL LAWAL*
_UMMUDAHIRAH_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝🏼‍♀️*

*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

'''( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)'''

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*








_________________________

*BABI NA ARBA'IN DA TAKWAS*
_______________Muhibba ta shigo ta ganta a wannan yanayin, wurin ta ta nufa da sauri cikin tashin hankali tana kiran sunan ta, she was very confused sabida ganin ba ta motsi, da gudu ta tashi ta je kiran Yayan su, tana shiga ta tarar dashi a zaune yana duba wasu files

Shigowar ta shima ya ɗaga kai yana kallonta, sai dai tuni ya murtuke fuska sabida a yanda ta shigo masa

Itama ɗin sai ta shiga taitayin ta tare da tattaro natsuwarta, cikin rawan murya tace, "Yaya, Humaira ce ta faɗo a saman gado ta dena motsi."
(Dayake sunan da suke kiranta dashi kenan kasancewar sunan mahaifiyar Aliyun ne)

Shi kuma tsawa ya daka mata mai firgitarwa yace, "ta fitan masa a office."

Har tana karo tsaban yanda ta rikice. Da sauri ta fita ta rufo masa ƙofan, bata tsaya wata-wata ba ta nufi office ɗin doctor Mamman. Yana tare da baƙi but ya bata iznin shigo wa, bayan ta shiga ne ta faɗa masa halin da Arab take ciki

"Subhanallah.." ya iya furta wa yana miƙe wa, sannan ya nemi excuse daga wurin mutanen da ke ciki ya fita shi da ita

Kai tsaye ɗakin suka nufa, a yanda ta barta a haka suka tarar da ita, shi yace, "ta taya shi su mayar da ita a kan gadon."

A tare suka ɗaga ta aka mayar da Arab ɗin saman gadon, sannan ya soma ƙoƙarin duba ta

A lokacin Muhibba har da ɗan guntun hawayen ta sabida tausayin Arab ɗin, fita tayi ta kira Dady a waya ta shaida mishi

Ai kuwa kafin mintuna ashirin sun bayyana a asibitin

Time ɗin ma har Arab ɗin ta farfaɗo, sai dai ta sha matuƙar wahala tunda sai da aka ƙara ɗaurin wuyan, ga ƙafanta da ta bugu har ƙara kumbura tayi, sai da aka sanya mata magani aka shafe wurin dashi, hannun ne bai yi komai ba, domin a lokacin shima mai ɗaurin ya ƙariso ya duba hannun, an yi Sa'a bai goce ba karayan sai dai an ƙara gyara mata

Dady yana ta faɗa, "meyasa aka barta ita kaɗai? Mene ne amfanin duk Nurses ɗin asibitin da baza a iya tura ɗaya ta kula da ita ba?" Daga Muhibban har Doctor Mamman ya tisa a gaba yayi musu tatas, kuma yace, "ya je ya kira mishi Aliyu sai ya ci mutuncin sa tunda duk laifin nasa ne."

Amma koda Doctor Mamman ya je office ɗin sa ba ya ciki, ya rufe office ɗin ma alamun ya bar asibitin. Sai ya dawo ya sanar da Dady

Shi kuma ya kira sa a waya but kiran ba ya shiga, ƙwafa yayi yace, "zan ci ubansa zai zo ya same Ni, ina nan zan ci masa mutunci."

Doctor Mamman dai sai ba shi haƙuri yake yi cikin kwantar da hankali

Hajja kuma da take taya Dadyn tace, "ai shiyasa nace maka wannan yaron bai da zuciyar imani, sam ba ya tausayin yarinyar nan, kullum idan ya zo sai ya saka ta kuka, don ta faɗo ai ba damuwarsa bane, abu mai sauƙi ya dena duba ta ka mayar da kulawan ta wurin Mamman tunda shi bazai iya kula da ita ba, in ba haka ba kullum a haka zata zauna baza ta warke ba tunda bai saka kansa zai yi ba."

RUƊIN DUNIYA!Where stories live. Discover now