Hamsin da uku

105 11 0
                                    

🌍🌍🌍🌍🌍🌍

     *RUƊIN DUNIYA!*

🌍🌍🌍🌍🌍🌍

*NA_NAFISAT ISMA'IL LAWAL*
_UMMUDAHIRAH_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝🏼‍♀️*

*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

'''( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)'''

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*








_________________________

*BABI NA HAMSIN DA UKU*
_______________Duk abun da ya faru sai da Arab ta sanar musu, sun yi mamaki kuma sun tausaya mata matuƙa, domin Ummu har da hawayenta na tausayin ƴar uwanta

Inna tace, "kinga rashin jin magana ai Auta, da yanzu kin dawo a lokacin da nace miki da duk haka bata faru ba, Ina ke ina ma mutanen ƙetare sata? Mutanen da basu da hankali komai zasu iya yi? Na tabbata ko nan kika zo wlh sai sun biyo ki, to kinga yanzu sai ya zame miki izna tunda kin rasa ɗan kuɗaɗen ki, duk da haka Allah ya isanmu matsiyata fatararru, sun ma kansu ai, yanzu tunda komai ya wuce shikenan ai Allah ya kyauta gaba. Yanzu ita wannan ɗin ne suka ce za ki auri ɗan su?"

Sai da ta yamutsa fuska sannan tace, "Eh."

"To ai bazan ce komai ba idan kina son sa, naga alamun suna da kuɗi Mutanen tunda daga ganin Matar ƴar gidan Manya ne; kuma Mutanen Abuja ne fa. Allah yasa shima Yaron yana da kuɗin ai ba wata matsala bane tunda akwai jin dad'i, Allah ya tabbatar da alkhairi zamu ce."

A nan ne Arab ɗin take tambayar ina Zahra ta shiga kasancewar bata ji motsin ta ba; kuma su basu yi mata maganar ba

Sai kuwa Inna ta zayyane mata komai halin da ake ciki, har auren su da aka yi da abun da ya faru da Ummu

Sai Ummun ta ɗauki waya ta kira Zahra ta shaida mata dawowar Arab

Wani irin ihu Zahra ta saka daga cikin wayan, yayinda ta kasa haƙura tace, "ta ba Arab ɗin wayan ta ji muryanta."

Da dariya Arab ta amshi wayan tana cewa, "ƴar uwa rabin jini..."

"Arab ina kika shiga kika bar mu cikin tashin hankali? Me ya faru da ke? Kin san kuwa wanne irin hali muka shiga?"

"Ba da son raina bane Aunty Zahra, but you have to come and hear what happened, come now, I miss you!"

"Ok gani nan yanzu kuwa. Give me a few minutes and I will come." Sai ta kashe wayan da sauri ta zari gyale. Dayake babu Haidar bai dawo wajen aiki ba, fita kawai tayi ta nufi gidan nasu a cikin ɗan ƙanƙanin lokaci har ta iso
  

Sun yi farin cikin ganin juna. Bayan sun natsa ne itama Zahran ta ji me ya faru, gaskiya ta tausaya wa Arab, domin duk wanda ya santa da zai tabbatar da cewa tayi muguwar canza wa, tamkar ba ita ba ta wani yanƙwane ta firirice, ga baƙin wahala. Don ma wai ta samu kulawa a gidan su Aliyu; shiyasa ta soma dawowa dai-dai, but duk da haka jinyan da ta sha ba na wasa bane, still har yanzu tana fama da kanta tunda ko a yanzu ɗin ma ta kasa cin komai a cikinta, duk yanda suka yi da ita suna ta lallaɓa ta amma ta kasa cin komai, sai zuwa tayi ta kwanta bayan ta sha maganin ta

Daga nan ne fa bata sake farka wa ba sai kusan ƙarfe takwas na dare. Time ɗin ma Zahra bata tafi ba tana gidan, daɗin ganin ƴar uwanta yasa tace, "baza ta koma ba a nan zata kwana." Tuni ta kira Haidar ta sanar mishi ma

Wanka Arab ɗin ta soma yi sannan ta ci abinci, ta ɗan samu daɗin jikinta, daga nan sai tayi Sallah suka zauna a falo suna ɗan taɓa hira

Inna tace, "su je su kwanta haka nan tunda dare ya yi sosai a lokacin."

RUƊIN DUNIYA!Where stories live. Discover now