page 7

22 0 0
                                    

💀 *BAƘAR TAFIYA* 💀

( *HORROR STORY* )

*BY MEEN@T A YANDOMA*
*MARUBUCIYAR FATALWA*

🌍 *MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*🌍🖊️

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*SALONSHI NA DABAN NE 💃🏼*

*ALLAH KAJIƘAN MAHAIFINA DA DUKKN MUSULMU BAKI ƊAYA KASA YA HUTA, KA KAI RAHAMA A KABARINSHI, ALLAH KA GAFARTA MASHI ZUNUBBABSHI, ALLAH YAJI ƘANKA ABBANA*

*MASOYA INA MATUƘAR GODIYA DA SOYAYYAR DA KUKE NUNAMA LITTAFIN NAN, ALLAH YA BARMU TARE, INA MATUƘAR GODE MAKU MASOYA A DUK INDA KUKE*

🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️
*ƳAN BAƘAR TAFIYA FANS COMMENT ƊIN YANA MATUƘAR TAFIYA DANI KUNA SANI NISHAƊI DA COMMENT ƊINKU, ALLAH YA BIYAKU INA MATUƘAR GODIYA*
🥰🥰🥰🥰

*WANNAN FEJIN SADAUKARWA NE GA DUK MASOYANA ADUK INDA KUKE, ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MAKU, INA GODIYA*

*MASOYA INA MAI BADA HAƘURI BISAGA JINA DA KUKA YI KWANA BIYU SHURU, HAKAN YA FARUNE BISA GA MATSALAR NEPA DA MUKA SAMU, AMMA YANZU KOMI YA DAI_DAITA, INA GODIYA MASU TURO MANI SAƘONNIN DA KIRANA DAMA WAƊANDA BASU SAMU DAMABA INA MATUƘAR GODIYA,ALLAH YABAR ZUMUNCHI* 🥰🥰🥰🥰
___________________
*PAGE 12_13*

.......Gudu suke iyakar ƙarfin su, domin ceton rayuwarsu.

Basu ankara ba suka gansu gaban wani kogo, basu tsaya 6ata lokaci ba suka kutsa kai cikin kogon.

Cirko_cirko sukayi suna mai da numfashi saboda gudun da suka sha.

Sai lokacin suka lura da inda suke,

"Mun shiga ukku minike gani nan?, ina muka kawo kanmu."
Salma ta faɗa tana nuna masu ƙwarangwal ɗin mutane birjik wurin.

Kogon ko ina ka kai dubanka ƙwarangwal ɗin mutane ne birjik ga yana duk ta mamaye wurin.

Ido suka fara rarrabawa suna ƙara bin wurin da kallo.

"Kada tsintar kammu a wannan ya tada mana hankali, mutsaya mu naimi mafita mu dage da addu'a,kada  mu kuskura mu rabu da junan mu."
Biba ta faɗa tana binsu Rabson da kallo.

"Eh haka ya kamata mu riƙa tafiya tare da junanmu, kada muyi kuskuren rabuwa da ƴan uwanmu."
Salma ta faɗa muryar ta na kyarma tana ƙara shigewa jikin Biba.

"Muje mu naimi abinci nidai jina nike  cikina kamar an hura wuta."
Rabson ya miƙe tare da yin gaba.

Bayanshi suka bi tare da nausawa ciki kogon.

Tunda suka fara tafiya Basu gamu da komi ba sai ƙasusuwan mutane da yanar da ta tare hanyar sai sun ɗebe ta da hannunsu suke samun hanyar wucewa.

Tirjiya suka ja ganin
Mutum tsaye.

Salma cikin in iyna ta furta da..da..daddyy.....

____________________
Sunyi gudu har sun galabaita.

Tsayawa sukayi ganin sun baro wurin duhuwar, sun bullo wani wuri mai yawan kwazazzabai ruwa na wucewa a hankali ta ƙasansu.

Yanayin wurin gwanin ban sha'awa.

Nan suka tsaya suka gabatar da sallolin da ake binsu.

Cikin ruwan da ke wucewa suka shiga suka ci gaba da tafiya, suna jan ƙafafu a hankali.

Jafar ne gaba sai su Basma a bayanshi.

Mandiya ji tayi kamar an tsunkule ta a ƙafa, a zabure ta yi tsalle ta ruƙunƙume Basma tana.
"Nashi ga ukku na lalace miye ya cijeni a ƙafa?, wayyo uwar daba da magajiya Allah ya tsinemaku albarka, duk ku kuka jefani ciki halinda nike ciki."

BAKAR TAFIYA COMPLETEWhere stories live. Discover now