page 17

10 0 0
                                    

💀 *BAƘAR TAFIYA* 💀

( *HORROR STORY* )

*BY MEEN@T A YANDOMA*
*MARUBUCIYAR FATALWA*

🌍 *MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*🌍🖊️

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*SALONSHI NA DABAN NE 💃🏼*

*ALLAH KAJIƘAN MAHAIFINA DA DUKKN MUSULMI  BAKI ƊAYA KASA YA HUTA, KA KAI RAHAMA A KABARINSHI, ALLAH KA GAFARTA MASHI ZUNUBBANSHI, ALLAH YAJI ƘANKA ABBANA*

*MASOYA INA MATUƘAR GODIYA DA SOYAYYAR DA KUKE NUNAMA LITTAFIN NAN, ALLAH YA BARMU TARE, INA MATUƘAR GODE MAKU MASOYA A DUK INDA KUKE*

🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️
*ƳAN BAƘAR TAFIYA FANS COMMENT ƊINKU YANA MATUƘAR TAFIYA DANI KUNA SANI NISHAƊI DA COMMENT ƊINKU ALLAH YA BARMU TARE,MASOYA INA GODIYA*

*ALLAH YA BIYAKU MY PEOPLE, ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MAKU HAR GADON BACCINKU, ƳAN BAƘAR TAFIYA FANS, KUNA SANI FARIN CIKI DA ADDU'O'INKU, ALLAH YA ƘARA DANƘON ZUMINCHI, KUMA BAZANI MANTA DAKUBA SAURAN MASOYA INA MATUƘAR GODIYA DA SOYAYYAR DA KUKE NUNAMA WANNAN NOVEL ƊIN ALLAH YA BARMANIKU MASOYA INA ALFAHARI DAKU.* 🤗🤗

____________________________
*PAGE 32_33*
...........Biba da Kulu da sauri suka riƙo Basma da ta fara chanza kamanni.

Ganin haka yasa Jafar  juyawa domin samun wani abu wanda zai iya zuba ruwa ciki, ya duba ko ina baisamu inda zai zuba ruwanba, chan gefenshi ya hango wani fasasshen ƙoƙo, ɗaukoshi yayi tare dayin basmala ya wankeshi tas, ya ɗauki ganyan Magarya guda bakwai ya zuba cikin ruwan tareda kanga bakinshi kamar zaisha ruwan ya fara karanto fatiha iskan bakinshi na bugun ruwan, saida ya karanta fatiha ƙafa bakwai, ya nufo inda Basma ke kwance batare da tasan wandake kantaba.

Biba ya miƙama ruwanya umarceta da ta bata ruwan ta kur6a sauran kuma ta shafa mata ajiki.

Kulu da Jamcy suka taimaka mata ta samu da ƙyar Basma tayi kurba biyu, sauran ruwan ajikinta ta ida shafe mata ajiki, Jafar umartarsu yayi su Kwantar da ita.

Matsawa sukayi daga inda take.

Kama an tsikareta da allura haka tayi wuf tamiƙe zaune tafara kwarara wani irin amai baƙiƙirin, tamkar zata amayo ƴan cikin ta.

Fuskarta kaɗai zaka kalla ka tabbatar ta wahala iya wahala.

Tana gama aman tayi baya luuu! Ta sume.

Biba hada gudunta zata kamo Basma Jafar yayi saurin tsaidata.

"Alhamdulillah da alamu maganin ya fara aiki, kada wanda ya matsa inda take har sai ta farka."

Cikin jimami da matuƙar tausayin Basma su duka suke kallonta kwance kamar matatta.

Abinda majigin idanuwansu suka hasko masu ne ya sanyasu matuƙar kaɗuwa zuciyoyinsu suka fara bugawa da sauri da sauri.

Aman da Basma tayine ya zama wasu irin baƙaƙen tsutsotsi sunata bille_bille, lokaci ɗaya suka kama da wuta suka ƙone ƙurmus.

Jikin su yayi matuƙar sanyi, wasunsu wani sabon imani ya riƙa shigarsu.

Dubansu suka kai ga Basma dake kwance, ilahirin jikinta yadawo lafiya lau takoma ainahin Basmarta, sai dai abinda ba'a rasaba na baƙar azamar da suke sha a wannan Baƙar tafiya.

Hamdala Jafar yayi tare da kallon Salma data ke raku6e wuri ɗaya tamkar wata mairainiya.

Itama ruwan ya ɗebo yayi mata ƙwatan ƙwacin yadda yayima Basma.

Tana gama shan ruwan ta maka sauran a kanta, yana ida isowa inda Mandiya ta cijeta ta ƙwala wata gagarumar ƙara tareda faɗuwa ƙasa ta fara bille_bille tana tada ƙura tamkar ana yaƙi.

BAKAR TAFIYA COMPLETEWhere stories live. Discover now