page 13

11 1 0
                                    

💀 *BAƘAR TAFIYA* 💀

( *HORROR STORY* )

*BY MEEN@T A YANDOMA*
*MARUBUCIYAR FATALWA*

🌍 *MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*🌍🖊️

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*SALONSHI NA DABAN NE 💃🏼*

*ALLAH KAJIƘAN MAHAIFINA DA DUKKN MUSULMI BAKI ƊAYA KASA YA HUTA, KA KAI RAHAMA A KABARINSHI, ALLAH KA GAFARTA MASHI ZUNUBBANSHI, ALLAH YAJI ƘANKA ABBANA*

*MASOYA INA MATUƘAR GODIYA DA SOYAYYAR DA KUKE NUNAMA LITTAFIN NAN, ALLAH YA BARMU TARE, INA MATUƘAR GODE MAKU MASOYA A DUK INDA KUKE*

🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️
*ƳAN BAƘAR TAFIYA FANS COMMENT ƊINKU YANA MATUƘAR TAFIYA DANI KUNA SANI NISHAƊI DA COMMENT ƊINKU ALLAH YA BARMU TARE,MASOYA INA GODIYA*

*ALLAH YA BIYAKU MY PEOPLE, ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MAKU HAR GADON BACCINKU, ƳAN BAƘAR TAFIYA FANS, KUNA SANI FARIN CIKI DA ADDU'O'INKU, ALLAH YA ƘARA DANƘON ZUMINCHI, KUMA BAZANI MANTA DAKUBA SAURAN MASOYA INA MATUƘAR GODIYA DA SOYAYYAR DA KUKE NUNAMA WANNAN NOVEL ƊIN ALLAH YA BARMANIKU MASOYA INA ALFAHARI DAKU.* 🤗🤗🥰

🤧🤧
_kwana biyu kunjini shiru, hakan ya farune sanadiyyar rashin lafiya danayi, masoya na haƙiƙa naga saƙonninku ina matuƙar godiya,Allah yabar zuminci_

___________________________
_dan Allah ku sanya auntynah cikin addu'a, yau kwana Ukku tana labour Allah ya sauketa lafiya_

*PAGE 24_25*

..........A guje sukayo wurin Basma domin ceton rayuwarta.

Sunyi iya ƙoƙarinsu wurin fiddo Basma a cikin ruwan amma abun yaci tura, saboda ruƙon da Mandiya tayi mata bana wasa ne.

Ƙarfi suka haɗa suka fizgota daga cikin ruwan.

Tare da Mandiya da ta yi mata mugun ruƙo suka fiddota.

Ganin yadda Mandiya ta koma yasa sauran abokan tafiyar ja da baya in banda Jafar da yake naiman hanyar da zai taimaki Basma.

Tamkar yunwataccen zaki haka Mandiya tayi wurgi da Basma tayo kan Jafar gadan_gadan.

Da nufin cizonshi ta iso takamashi da kokawa sukayi ƙasa.

"A'uzubillah! Subhanallah!!."
Jafar ya furta ganin mace wadda ba muharramarshi ba ta ta6i jikinshi suna kokawa a ƙasa.

Tunyana kare kanshi daga muggan hare_hare da take kawo mashi harya fara mai da mata martani.

Su Jamcy ba kata6us tsaye suke sun haɗe wuri ɗaya ita da Tk suna surutan da ko su basu san mi suke faɗaba.

Ƙoƙarin yakiceta Jafar yayi ya wurgar da ita can gefe.

Abinda ya lura da waɗannan Horror ɗin basu taba mutuwa sai dai suyi doguwar suma inkayi nasarar luma masu wani makami ta bayansu.

Dube_dube ya fara naiman inda suka yada itatuwanda suke kamun kifi da su.

Can nesa da inda suke ya hango su.

Da gudu ya nufi inda suke, yana gaf da ida isa yaji an warto ƙafarshi ba shiri yayi ƙasa.

Ganin Mandiya na ƙoƙarin kawo mashi hari ta kowace hanya ya sanyashi kai mata harbi da ƙafafunshi cikin zuciyarshi yana karanto duk wata addu'a data zo mashi, yana ƙara ƙaimi wurin isa ga iccen da yake ƙoƙarin kaiwa.

Yayi nasarar ɗauko icce inda yayi nasarar luma matashi a tsakiyar baya, wata firgitacciyar ƙara ta kwala ta faɗa cikin ruwan ta 6ace 6at.

Wurin Basma dake kwance magashiyan dafe da wuyanta suka yo aguje.

BAKAR TAFIYA COMPLETEWhere stories live. Discover now