page 14

15 0 0
                                    

💀 *BAƘAR TAFIYA* 💀

( *HORROR STORY* )

*BY MEEN@T A YANDOMA*
*MARUBUCIYAR FATALWA*

🌍 *MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*🌍🖊️

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*SALONSHI NA DABAN NE 💃🏼*

*ALLAH KAJIƘAN MAHAIFINA DA DUKKN MUSULMI  BAKI ƊAYA KASA YA HUTA, KA KAI RAHAMA A KABARINSHI, ALLAH KA GAFARTA MASHI ZUNUBBANSHI, ALLAH YAJI ƘANKA ABBANA*

*MASOYA INA MATUƘAR GODIYA DA SOYAYYAR DA KUKE NUNAMA LITTAFIN NAN, ALLAH YA BARMU TARE, INA MATUƘAR GODE MAKU MASOYA A DUK INDA KUKE*

🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️
*ƳAN BAƘAR TAFIYA FANS COMMENT ƊINKU YANA MATUƘAR TAFIYA DANI KUNA SANI NISHAƊI DA COMMENT ƊINKU ALLAH YA BARMU TARE,MASOYA INA GODIYA*

*ALLAH YA BIYAKU MY PEOPLE, ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MAKU HAR GADON BACCINKU, ƳAN BAƘAR TAFIYA FANS, KUNA SANI FARIN CIKI DA ADDU'O'INKU, ALLAH YA ƘARA DANƘON ZUMINCHI, KUMA BAZANI MANTA DAKUBA SAURAN MASOYA INA MATUƘAR GODIYA DA SOYAYYAR DA KUKE NUNAMA WANNAN NOVEL ƊIN ALLAH YA BARMANIKU MASOYA INA ALFAHARI DAKU.* 🤗🤗🥰

______________________________
*PAGE 26_27*

..............Ahankali iskar da ta kwasosu ta fara lafawa.

Tare da 6acewa 6at! Tamkar bata ta6a wanzuwa ba.

Hannu Jafarne ya fara motsi, idanunshi suna ƙoƙarin budewa, samun kanshi yayi da furta, "
_ALHAMDULILLAHILLAZI AHYANA BA'ADA MA AMATANA, WA ILAIHINNUSHUR_"

Kanshi daya ji yana barazanar tarwatsewa ya dafe yana Ambaton " _INNALILLAHI WA'INNAH ILAIHI RAJIUN, ALLAHUMMA AJIRNI FIYMUSIBATI WA'AKLIFINI KHAIRAN MINHA_ Ya ubangiji ka kawo mana ɗauki akafitar damu daga wannan musiba."

Dubanshi yakai inda su Basma ke kwance basu san mike faruwaba.

Abinda idanuwanshi suka hasko mashi ya sanyashi idan miƙewa daga kwanciyar da yake yayi saurin zaunawa, hannuwanshi yakai kusa da idanunshi ya murza idanun yaga kodai gizone suke mashi.

Ƙara tabbatar wa yayi ta hanyar tsinkulin kanshi yaji kodai mafarki yake, da gaskene su Rabson ne ba gizo idanuwanshi keyi mashi ba.

Wani farin ciki marar misaltuwa ya wanzu azuciyarshi baisan lokacinda ya kalli alƙibla yayi sujadar godiya ga Allah daya bayyanar masu da abokan tafiyarsu.

Motsin dayaji ne ya sanyashi saurin juyawa.

Su Basma, Jamcy da Tk ne yaga sun farka lokaci ɗaya suna dafe kansu dake masu tsananin ciwo.

Rabson ne yafara harba ƙafarshi saman wuyan Salma, ita ma motsi ta fara alamun zata farka Kulu da Nas suma farkawa sukayi.

Rabson waige_waige yafara kamar yana naiman wani abu, su Jafar daya hango yasashi fara ja da baya yana salallami.
" _INNAHUMIN SULAIMANU, LA'ILAHA ILLALLAHU_, ku kuke ganinmu bamu muke ganinkuba,wayyo namutu na lalace, shikenan gasunan sunzo mana da suffar abokan tafiyarmu, wayyoh Salma masoyiya kina ina."?
Ya ƙarashe maganar yana janƙugu yana baya_baya.

"Hhh! Kai Rabi'u Rabson ɗin Kaka, munefa da gaske ba horror bane."
Jafar ya ida maganar yana dariya.

"Mtssw! Sauna kawai, kabi ka cika ma mutane kunne ko ina kaga horrorn."?
Salma ta faɗa tana hararar Rabson.

Wiƙi_wiƙi Jafar yayi yana rarraba ido.

Gaisawa sukayi ta yaushe rabo, bayan sun gama shan hira da taya juna jimamin rashin fitarsu wannan baƙin daji.

Shawara suka yanke ta yanzu bazasu ƙara tafiyaba gudu zasuci gaba dayi sallah da abinci kaɗai zai tsaidasu.

Matsawa sukayi wurin wani iccen gwaba suka tsinka, Jafar ne yafara rarrabama masu.

BAKAR TAFIYA COMPLETEWhere stories live. Discover now