part one 1

33 3 0
                                    

Bismillahir rahmanirrahim.

Please follow up on wattpad
Hayratysambo😘

Marubuciyar...
Ruwa a bakin daro(incomplete? But this will be complete Insha Allah🙏

GARIN ABUJA 7:30pm

Kamar yanda kowa ya sani Abuja babban birnine da ake taqama dashi a qasa Nigeria,

Ta tara manyan mutane da dama kama daga Yan siyasa, shuwagabanni da masu muqami da Kuma wasu masu hannu da shuni mazauna abujan,
Kowa zaman kanashi yakeyi babu me shiga harkan kowa Kuma kowa da kalan sana'ar da yakeyi,

Yawanchi idan ba wai ghetto area Ka shiga ba ko kasuwanni shine zakaji hayaniya da karakainan mutane amma wasu unguwannin manyan shiru zakaji,

Saidai yau gaba daya garin hayaniyane walau cikin kasuwannin da unguwan masu qaramin qarfi har zuwa unguwannin masu kudin, yayinda sama ya gauraye da hayaki duk da lokacin darene amma bashi ze hanaka tantance hakan ba,
A sakamakon wutan da ya tashi a wani sabon gidan mai na wani babban me kudi da yake garin abujan,

Wanda an Riga an Gama komai a gobe asabar ake Shirin yin liyafar budeshi, saidai yau bayan an shiga sallar isha'i kawai aka dinga jiyo hayaki da iface ifacen mutane, ko kafin asan abinyi a Kira Yan fire service tuni wutan ya Riga ya Gama cinye komai da yake gidan mai din.

Ko kafin ace me..wajen babu komai ya Zama gawayi babu komai a wajen se mutanen da sukai cincirindo suna juyayin abin, yayin da Yan sanda suke zagaye da wajen suna duba daga inda wutan ya faro,

Saidai cecekucen da mutane sukeyi yasa ake zargin tabbas ba hakanan wutan ya tashi ba, kunnashi akayi,
Yayinda wasu daidaikun mutanen da Basu Riga sun shiga sallah ba da Christocin da basa sallah sukace tabbas sunga wasu mutane da bakaken Kaya yayin da fuskokinsu yake a rufe sunzo a mashina sunkai biyar da gudu suna zagaye wajen,

Wanda bayan wucewar su befi da minti biyu ba kawai akaga wajen ya fashe da wuta.

Qarar jiniyar motan sojojine ya qaru sakamakon isowar me gidan mai din alhaji garba Dan sadau,
Budamai hanya akayi ya shiga cikin inda ACP din da yazo shima yake mayar Mai da jawabin abinda ya faru, yayinda Yan jarida keta aikin su na daukan rahoto.

Wani Dan sanda ne cikin Wadanda suke binciken wajen ya qaraso da sauri hannunshi rike da wani envelope,

Yana qarasowa Sara mishi yayi tare da Mika Mai envelope din Yana fadin,

"Yallabai duk mun Gama binciken ko ina Amman bamuga komai ba se wannan envelope din an makale a wani saqo inda be qone ba"

Amsan envelope din yayi tare dasa safan hannu kafin ya Bude, tsira ma rubutun ido yayi na tsawan sakwanni kafin ya mikama alhaji garba,

Gyara zaman gilashin dake idonshi yayi kafin ya karanta me aka rubuta da Jan marker a papern

"BAD J" ya Fadi a fili Yana mikama inspecta papern
Amsa yayi shima kafin ya Bama dayan Dan sanda Yana fadin" Ka adanata sosai shima zamuyi bincike a kanashi"

Ansa yayi Yana qara saramai kafin ya wuce,
Kallan alhaji garba da idanunshi yau jaa ACP yayi tare da fadin "babu shakka yaronnan ya Dade Yana aikata barna a qasannan BA tare da ansan ko wanene shi ba, Kuma har yanxu Allah be bamu ikon sanin shiba,
Amman Kuma munanan muna qara qarfafa tsaro da Kuma bincike har se mun gano KO wanene wannan mutumin"

Kallanshi alhaji garba yayi ba tare da yasan ma meze ceba don ba qaramin narka kudi yayi a wannan gidan Mai da yake Shirin budeshi gobe ba,
Shidai ya sa ma ranshi ko sun duboshi ko Basu duboshi ba shidai zeyi iya bakin qoqrinshi na ganin ya gano wanene wannan Wanda take bata musu aiki a komai da suka sa gaba.

Juyawa yayi ya wuce ba tare daya cemai komai ba, yayin da matakan tsaron shi suka rufamai baya,
Gefe guda kuma ga Yan jarida da suke binshi aunaso suji ta bakinshi,
Shi a yanzu baya da lokacin magana dasu koma yanadashi to Besan Menene zece musu ba,

Basu dena binshi ba har Saida ya shiga motanshi sannan suka koma wajen ACP Wanda shine yau musu bayanin komai tare da yin alqawari kaman kullum na binciko ko wanene wannan BAD J din.

BAKAN GIZO 🕷️Where stories live. Discover now