part 4

6 0 0
                                    

Bismillahir rahmanirrahim

Please follow up on wattpad @ayeeshatou

ABUJA 

Tunda ya barta anan wajen take tsaye babu inda ta sani a garin in banda anguwan da suka sauka shima yanxu in za'a kasheta batata iya fadin ga sunan unguwar ba.

           Wayarta  dake cikin yar qaramar pose dinta dake manage a hammata ta ciro, kunnashi tayi ko Allah zesa ya tsaya, kallon wayar takeyi yana starting a zuciyarta ko adduar ta daya Allah yasa ya tsaya  koda 2 percent ne tasman ze iya kira mata koda mutum daya ne Wanda tasan zai iya zuwa daukanta at this time,

Want irin bugawa qirjinta yayi tunanin gidan da tayi, yanzu ta ina zata fara bayanin ga abinda ya faru da ita? Me zatace ta fitayi da mota alhanin ita ba sanin ko ina tayiba, hatta zuwa dinner  ma yaya tazo shine har zata fita?.

              Ta tuna irin draman da sukayi dazu da yah aliyu akan zuwanta abujan,

Shigowa yayi gidan ranshi a bace yana fadin "ina Naidan take"  duk dangine a tsakar gidan wadanda bash tafi waliman da akeyi a gidan kawu uba ba, sai yan mata irin su Naida dake qannin amarya anata shirin dinner da za'ayi anjima.

     Tunda taji muryarshi ta fara zaro idanu dama tasan ko kowa yaji maganar tahowarta baiyi maganaba shi saiya tanka, jin muryan inna binta tayi daga tsakar gida tana fadin 

"Ba'asaninba tunda baka iya sallama ba kawai zaka fadoma mutane gida babu sallama"    juyawa yayi ya kalli sashin da take tana zaune saman farar kujerar robar da tana aka dauko mata daga wajen walima, 

share maganar da taimai yayi yana fadin "Amman fisabilillahi inna yarinyar nan fa exam ne da ita jibi Amman shine aka biye mata saida aka taho da ita bikinnan to wayene zai mata karatun jarabawar?"

"To kai in banda abinka ai ba bikine kadai ba, yanzu ko want wannan taron ma da aka akayi ai zaazo tana dangi itama tayi ziyara ko?

" eh Amman ai akwai bayan biki, in ta gama jarabawar ba sai tazo tayi ziyarar ba , jibine fah exam din yaushe har zatai karatun, to Allah yasa ta qara fadi wanna  karan ma zataga yanda zan babballata" 

     Harararshi inna binta tayi dama ba wani shirin arriving sukeyiba "to alhudahuda uban karatu inta fadi ka kasheta kawai, hakanan baza'abar mutum ya hutaba kullum karatu karatu itama batata sakata ta walaba, inadai jibine kace jarabawar ko? To kasha kuruminka insha Allahu gobe tare zamu koma da ita"

       Kwafa yayi ya juya ya fita yana fadin  "zamu hadu da ita ai"   ita dai tana daga daki tana jinsu tasan tunda taji yace zasu hadun nan to wasan buya zasuyi tayi harse ya manta.


Qarar vibration din wayarce ya dawo mata da tunaninta, har ta gama kunnuwa sannan koma ta mutu alamun shutdown, wani irin zufane ya karyo mata tasan yanzu sha daya ta kusanyi Idan ma bata wuceba,

Wani irin tsorone ke cinta  qafafunta har wani rawa sukeyi bayan zuciyarta dake lugude kaman zai fado qasa,


    Waigawa ta farayi tana qarema irin unguwan da take kallo, irin arean masu kudinnanne babu yawaitan mutane duk da titine Amman babu ko irin shagunan nan ko wasu tarkace wajen fahau sai hasken solar daya haske ko ina, 

        Gajiya da tafiyan tayi ta tsaya bakin titin kallon yanda daidaikun motoci suke zuwa su wuceta fuuu...

Ganin irin kallon da wasu masu motocin suke mata a ganinsu sun dauka irin karuwan nanne masu tsayawa a bakin titi da daddare,

  kallon jikinta tayi ko shigarta tayi kama Dana prostitute ne maybe shiyasa basa tsayawa su taimaketa duk da ita kantar bawai tayi tsayuwan kaman me neman taimako bane tana tsayene irin na Wanda ya rasa abinyi a rude take .

BAKAN GIZO 🕷️Where stories live. Discover now