part 2

15 1 0
                                    

Bismillahir rahmanirrahim

Please follow me on wattpad
Hayratysambo😘

GARIN KADUNA 7:30PM

"Haba Junaid Ka tashi Ka shirya mana idan bazaka ba Ka fadama mana bawai Ka tsaya kana bata mana lokaci ba kasan dai dole tare zamu shiga wajennan ko?

Wanda aka Kira da Junaid din Yana kwance kan sofa bed hannunshi riqe da waya Yana daddannawa,
Kai kallon shi yayi inda abokanansu suke a cikin dakin duk sun shirya kaman yanda Fahad yace, anko sukayi cikin shadda light blue colour saidai kowa design dinshi Kala daban,

Dawo da kallon shi yayi kan gadon inda nashi yake ajiye,
Tashi yayi daga kan gadon tare da daukan towel dinshi da yake saman akwatinshi yayi hanyar toilet,

Fahad ne ya bishi da kallo yana fadin "yanxu fisabilillahi Menene Kuma nase ya Kara yin wani wankan? Kawai dai salon Ka batama mutune lokaci, mu bazamu iya jiran wannan qalailayan nakaba in Ka fito kaga Baka samemuba Seka taho Kai kadai ai kasan hanya" ya qarasa Fadi Yana bankamai harara,

Shidai KO juyowa beyiba balle ya tankashi,
Yayi kusan minti goma sha biyar kafin ya fito yayi tsammanin base samesuba kaman yanda suka ce amma yaga still sunanan suna jiranshi,
Murmushi kawai yayi Dan dama yasan bragging kawai Fahad din yakeyi Dan saboda yai sauri,
Wajen dressing mirror din dakin yaje to bayan ya gama shiryawa ya tsaya kallon Kashi,
Yayi kyau sosai dama gashi Allah ya zuba Mai kyau ba Dan kadan ba, dan tsayawama fadin yanayin kyanshi bata lokaci ne saidai Ka kiyastashi a zuciyarka,   

     Dan koshi yasan Yana da kyau badan kadan ba, koda ace shi baya gani amma mutanen da suke fadamin kadai ya isheshi tabbatar da haka,

    Dan basau daya basau biyu ba ansha tarrshi Yana cikin tafiya a fadamai Yana da kyau hatta da Yan uwanshi mazama Kuma bawai Dan suma basa da kyau dinba.

    Ga wani kwarjini da Allah ya zuba Mai nanan mamaki,
    Dan babu yanda za'ayi ace za'a iya kallon cikin qwayar idanunshi kamai magana me tsayi BA tare da kaji nauyi a zuciyarka ba.

    Tsakin Fahad ne ya katseshi daga tunanin daya tafi "mtseew in Ka gama kallon kan naka seka samu mota Ka biyomu daga yanxu bazan iya qara jiranka ba Kuma"
    Ya juya Yana kallon sauran abokan dasuke zaune" kuzo mu tafi in Kuma zakuci gaba da jiranshi to se kunzo"

   Kama hanyar barin dakin yayi Yana Kada Kada key din motarshi,
     Murmushin gefen Baki yayi tare da binshi yanasa hannunshi cikin na Fahad din suka bar dakin tare.

    Faruk ne da Abbas ya baya, se Junaid a gefen me zaman banxa,
    Basu suka isa hall din da ake event dinba se wajen 7:50,
      Koda suka isa babu kowa a harabar wajen se mutanen dake suka fito da Wadanda Basu Kai da shigaba,
     Tsayawa sukayi a jikin motan tare da daukan waya a Kira sudais,

     Be dadeba ya fito yayi kyau shima cikin shadda ,
     Faruk ne ya fara teasing dinshi" ango ango, ango kasha qamshi,"

    Bashi hannu yayi suka tafa Yana fadin "kunyi latti fah har mun gaji da jirama mun fara tun dazu kamar wanda suke Shirin shekara?"

   Hararar gefen da Junaid yake Fahad yayi Yana fadin "kaima hakan ba Wanda ze bata mana lokaci in ba wannan ba tun dazu shi muke jira, mutum in Banda iyayi be iya komai ba" 
     Sauran ne suka kwashe da dariya, sudais yace" to yanxu dai tunda kun qaraso se muje a qarasa daku tunda Bama adade da farawa bama dan  ba'a yi main abubuwan ba"
   
    Qarasawa sukayi inda sukejin MC Yana sanar da isowar manyan abokan ango da Basu samu isowa da wuriba ba

                *.                 *.                     *.     

ABUJA 8:00
 
   Makeken falone sosai yasha kayan alatu, ga hasken wutan lantarki daya haske falon,
   Wasu manyan Mutane uku ne ke zaune akan wasu manyan kujeru se wani matashi dake zaune daga gefe,

BAKAN GIZO 🕷️Where stories live. Discover now