Part 27

1.1K 97 5
                                    

Amirah
Da Asuba duk tashin da Fainusa ta ringa yiwa Amirah tayi sallah ko motsi batayi ba. Ba wai dan bata jin ta ba, A'a kawai ita ta tsani wannan tashin Asubar da sukeyi tun kafin ayi assalatu.

Tana lafe akan gado ta jiyo Fainusa tana gayawa Dada zuwan Bashir din jiya da daddare, seta miqe zaune. "Kardai ya shigo ya ganni ina sharar bacci" ta fada tana zaro ido.

"Wayyo ya zanyi yanzu" ta sake fada a fili tana tunanin mafita. Tunda akayi rasuwar take masa qaryar bata iya bacci da daddare shi yasa kullum suke raba dare suna waya se yayi dagaske take barinsa ta kwanta.

Jiyan ma abinda yasa bata kirashi ba baccin taji da wuri, seta shirya a ranta da safe in sunyi waya se tace masa ai tasan ya koma gida ne bata so ta kirashi Anty taji haushi toh yanzu gashi qilan ya ganta wai ya ma akayi be gaya mata ze zo a jiyan ba. Yanzu ita wace qaryar zata zabga masa?

Ganin ba mafita ya sakata tashi da niyyar ta yiwo alwala idonta ya sauka akan Maganin tari akan Mudubi. Nan take ta tuno ranar sadakar uku aka siyowa Yaron Anty Amina Babbar Yayar su Bashir da take aure a Bauchi, se akayi rashin sa'a aka karbo na manya dan haka bata bashi ba ta ajiye a dakin.

Da sauri ta dauke shi, seda ta leqa ta jikin qofa ta hango Dada da Fainusa suna Nafila kafin ta bude kofar Toilet a hankali ta shiga ta tuttar da fin rabin maganin a rariya kafin ta koma ta kwanta bayan ta ajiye shi saitin kanta ta bar kwalbar a bude.

Har qarfe shida tana kwance a gurin, Fainusa data gama Azkar dinta ta shiga dakin yin wanka dan zata fita gurin aiki tana koyarwa a makarantar secondary dake kusa dasu ta tarar da Amirah a bararraje tana bacci babu Alamar ta tashi tayi sallah.

"Lallai yarinyar nan, daman baki tashi bama kikayi sallar nidai naga randa zakiyi hankali" ta fada bayan da ta danawa Amirah duka a cinya ta bude ido da sauri dan dukan ya shigeta.

"Akan me zaki zo ki dakeni, Allah ya isana wallahi" ta fada tana sosa inda ta dake tan.

"Ni kike yiwa Allah ya isa mara kunyar banza kawai" Fainusa ta hayayyaqo mata, Dada da tajiyo hayaniyar tasu ta shiga da sauri tana cewa

"Bismillahi safiyar taku tayi zaku fara ba, kamar masu ganin hanjin juna yanzu kuma me akayi?"

"Dada wai fa wannan mara kunyar tunda na tashe ta da Asuba ashe bata tashi tayi sallar ba, shine yanzu fa dana shigo na sake tashinta ta fara zagina tana mun Allah ya isa".

Bude baki Amirah tayi da niyyar magana ta hango Bashir ya turo qofa, se kawai ta fashe da kukan qarya harda sheshsheqa tana cewa

"Wallahi Dada ba haka akayi ba, ni ban ji sanda ta tashi ni ba ban ma san safiya tayi ba kawai yanzu tana shigowa ta hau dana mun duka wai na kwanta ina bacci kamar wata kafura bayan tasan ko baccin bana iyayi, kuma ni maganin mura nasha shine bacci me nauyi ya kwashe ni" ta fara qoqarin miqewa, tana sane ta ture kwalbar maganin dan sauran na ciki ya zube ita kuma ta koma dabas ta zauna a dole jiri take gani.

Sake yunqurawa tayi ta miqe se ta tafi kamar zata kife Bashir yai saurin tarota yana cewa "yi a hankali mana" nan idonsa ya saka akan kwalbar maganin, seda ya zaunar da ita kafin ya daga kwalbar yana kallonta yace "Amirah kina hauka ne, syrup kika sha saboda kin kasa bacci?"

Kuka haiqan ta saka masa tana cewa "to ni yaya ake so nayi? Bana iya bacci ni kadai nasan damuwar da nake ciki babu wanda ya damu da ni har kai din ai baka zo ba bate kasan halin da nake ciki".

Seda ya yi qoqari ya hadiye bacin ransa, kafin ya sassauta murya yana cewa "shikenan, yanzu ki daure kiyo alwala kiyi sallah, lokaci yana qara ja" ya juya ya fita jin ana kiran wayar sa.

Seta miqe tabi bango, dab da zata shiga bayin ta waiga tareda ballawa Fainusa harara ganin babu wanda yake kallonta ta shige ciki.

Daga Dada ko har Fainu bude baki sukayi suna kallon wannan Drama, ita Dada mamakin yanda zata ce bata bacci kuma kowa babu me kula da ita, to wanne baccin ne batayi yarinyar da duk dare seta leqo su kuma ta ganta tana baccin ta qalau kai har na rana yi take, gaba daya fa jimamin na kwana biyu tayi ta ware se idan taga idon mutane ne zata wani koma kalar tausayi duk fa tana ankare da ita.

WATA KISHIYAR (ALKAHIRI CE KO SHARRI)Where stories live. Discover now