Part 58

2.2K 222 40
                                    

BASHIR

Beyi niyyar zuwa sallah Gombe ba amma saboda karya shiga haqqin Amirah yasa ya tuntubeta ko zasuje. Suna zaune ita da Addah a palour ya fito daga dakinsa da ya mayar dimun da iman yana ciki indai yana gidan.

Ledar kayan sallar ta daya karbo dazu ya dauka ya fito palour,
Suna zaune Tayi daddaya a qasa taba cin Gyada dafaffiya ga cikinta nan daya fara girma a waje saboda Half vest ce a jikinta kawai ta daura zani kanta babu dankwali wai zafi take ji dukda akwai wuta sun kunna Ac  suna hira da Addah da tayi shar abinta duk rama da baqin da tazo dasu babu to aci me kyau a kwana a Ac meya dameta.

Zama yayi ya gaida Addah ta amsa tana hararar sa dan haushin sa take ji, bama ya zama bare suyi magana da ita tun ranar nan da tayi masa zancen kayan sallah be kulata ba gashi har yanzu ana jibi sallah koda uwarsa yake so taje idi oho.

"Ya jikin naki? Me yasa kika zauna haka a cikin sanyi gashi kanki ko rufeshi bakiyi ga dare ba bakya son kula da lafiyar kwata kwata" ya fada bayan daya amsa gaisuwar da Amirah tayi masa.

"Kai in ka gaya mata qila taji ai mata da ciki ki zauna duk kiyita budewa Aljanu da ifiritai jiki suna kallo ai se kiyi tayi se wani abu ya same ki kuma azo ana yaya za'ayi" Addah ta fada tana gyara zama.

"Babu abinda ze sameta In sha Allah kawai dai ta ringa kula kuma meye ma amfanin zamanki idan bazaki ringa nuna mata abinda ya kamata tayi ba"

"Bazan nuna ba ubana nace bazan nuna ba, kaifa daman ba mutunchi ne dakai ba to ni banzo dan in kula da ko wacce qatuwa ba zuwa nayi nima a kula dani na hutawa rayuwata a toh" ta hayayyaqo masa.

Be kulata ba ya turawa Amirah ledar daya fito da ita Addah tayi zaraf ta dauke ta zazzage kayan ciki a qasa.

Kayane kala hudu, Atamfa biyu se Lace daya da Brocade material shima daya duk an yi musu dinkuna masu kyau. Seda ta ware ko wanne dukda a goge suke tas ta hargitsa kafin ta watsar qasa tana cewa

"Ina nawa naga duk wasu riguna fici fici babu wadda zatamun a ciki"

"To daman an ce miki da naki a ciki ne kayan Matata ne kema ki siya da kudinki mana ai kina dasu ko ni aka ce na miki kayan sallah?" Ya fada kansa tsaye.

Amirah kanta da take murna tana daddaga kayan dan babu wanda beyi kyai ba kana kallo kuma kasan masu tsada ne seta tsaya tana kallonsa jin abinda ya fada tace

"Yaya Addah ce fa kake gaya mata haka"
Harara ya maka mata yana cewa
"Gobe Solomon zezo ya kaiki ki siya takalmi da mayafi zan tura miki kudin sannan na manta ban tambayeki ba ko zakije sallah Gombe ne dan ni bazan je ba"

"Uwarka Nafi ita kake wulaqantawa Bashir bani ba shege wanda be gaji Arziqi ba. Ni zaka kalla kayiwa gori to wallahi bazanyi da kai ba da uwarka zanyi dan ita ce daidai dani se inji idan ma ita ta baka damar ka ringa wulaqanta ni. Idan ma banda lalacewa Bashir in haifar maka matar ka aura amma baka da wadda ka raina a duniya sama dani ko? Nagode.

Ke kuma kina zaune yana qarewa uwarki tana di ai Shikenan gaki gashi nan kuci kanku" Addah ta fada tana miqewa, har tayi gaba kuma ta dawo tana cewa

"Babu Gomben da zamuje uwar me muka manto acan da zamu koma dakkowa?"

Shidai be kulata ba ya kalli Amirah yana jiran tata amsar itama a sanyaye tace
"Anan zamuyi sallah"
"Shikenan, goben da wuri zezo daganan se ku biya kuyi cefanen abincin sallah"

Ya dauki wayarsa yayi danne danne kafin ya miqe ya shige daki yana cewa "gashi nan idan kunje ze kaiki inda ake siyar da Ready made ki dauki 50k ki siya mata kala biyu ai zasu isa".

Wayarta da take gefen ta ce tayi qara alamar shigowar saqo ta janyo ta duba, dubu dari da Hamsin ya tura mata tayi ihun murna daidai sanda Addah ta fito daga dakin da take da waya a kunne tana cewa

WATA KISHIYAR (ALKAHIRI CE KO SHARRI)Where stories live. Discover now