Part 35

1.3K 116 13
                                    

ASMA'U
Muna cikin wata takwas da aure me kamfanin da Bashir yake aiki ya rasu dan haka akayi rabon gado yayansa suka saka kamfanin a kasuwa abinda ya tilasta wa ma'aikata barin aikinsu.

Wannan dalili yasaka Bashir dawowa zaman gida a koda yaushe saboda har sannan babu wani aiki daya samu ya dai rarraba CV amma babu inda aka kirashi. Da farko abin yazo mana da sauqi saboda Alhamdulillah kusan komai na buqata muna dashi a gida dan abinda ba'a rasa ba muke siya irin su kayan miya ko ganye da dai sauran masarrafi dan haka idan na fita makaranta se nayi amfani da kudaden da suke hannuna na siyo mana komai yanda zamu dan kwana biyu tunda kudi basa yanke mun.

Duk sati Baffa yake bani kudin makaranta dan shi yake dauke da nauyin karatuna ga kuma na man mota da ake hadamun dashi yanzu.

Ta inda matsala ta dan bullo mana rashin lafiyar da Baban su Bashir ya fara, bayan kaishi Asibiti suka tabbatar da cewa yana da Suga da hawan jini ne suka taso masa lokaci daya seda yaci kudi sosai kafin lafiyarsa ta samu sannan aka dorashi akan magani abinda ya turgude dan jarin kasuwancin da yake yi kenan dan da kudin akayi duk hidimar Asibitin sa.

Ganin da nayi rayuwa ta fara yi musu matsi, kuma Baban da yake fita ya nema musu na cefane gashi a gida babu wadatacciyar lafiya. Bashir baya aiki a yanzu Amiru yana shekarar qarshe a Jami'a, Afiya tana Level 1 se Fainusa da Sadiya da suke secondary daga Sa'ad,Samirah har Naziru lokacin a primary suke.

Akwai ranar da mukaje duba Baban da da yamma, abinda ya daga mun hankali muna zuwa na tarar da Dada tana yi musu kwadon garin kwaki harda Baban da yake fama da Siga a sannan shi aka zuba masa yaci. Abun ya bala'in daga mun hankali.

Bayan mun koma gida washe gari banyi shawara da Bashir ba na dauki Buhun shinkafa biyu, taliya, macaroni, semovita komai biyu ga pastar mai hatta Maggi seda na diba na hada sannan na tsaya a hanya na siyi kayan Shayi da kayan miya na tafi gidan.

Yara na samu a qofar gidan suka shigar da kayan, motar Aliyu dana gani ya tabbatar mun da Bashir yana gidan dan daman tun safe yau ya fita dan haka ban shiga ba kawai na wuce gidan mu. A can na tarar da Junaidiyya wai ta zo gida haihuwa ga Yah Bilki ma tazo da tsohon cikinta haka Yah Fati Alawiyya ce dai nata be isa haihuwa ba ni se a sannan ma tunani na ya tafi ga rashin samun cikin da banyi ba.

Dukda ina son yara amma hakan besa na taba damun kaina da sena samu ciki dole dole ba kuma shima Bashir ko sau daya be taba mun maganar ko nuna wani abu akan hakan ba gaba daya mun barwa Allah shi ke bayarwa idan lokaci yayi nasan zamu samu namu muna.

A gidan na wuni har dare dan ina son naga Baffa, se bayan Isha ya shigo gida ashe Yola yaje daurin auren Yar Baffa Sama'ila.

"Mamana ya akayi ne har yanzu baki tafi gida ba" ya fada bayan dana gaishe shi, sena marairaice fuska nace

"Baffa Kasan Alhajin su Bashir bashida lafiya ko"

"Na sani wallahi ai na dubashi ma sanda yana Asibiti sannan bayan sun dawo ma na sake leqa gidan, ciwo ne babu dadi yanzu kuma abinda ake ta fama dashi kenan wannan Siga Allah ya tsare mu dai".

"Amin Baffa, daman wata Alfarma nake nema idan babu damuwa" na fada ina gyara zamana. Se ya kalleni yace

"Gidan ku Ma'u ni zaki kalla kice kina neman Alfarma a gurina, idan banyi muku abu ba wa kuke dashi a fadin duniyar nan daya fini?
Kar na sake jin haka, ki tambayeni kai tsaye abinda kike so ko menene shi a duniyar nan zanyi miki dan duk abinda na mallaka domin na inganta rayuwar ku ne" Baffa ya fada cikin dakewa alamar babu wasa a maganar sa. Sena saki murmushi. So da qaunar Baffan nawa tana qara ratsani nace

"Wallahi Baffa gani nayi gaba daya rashin lafiyar nan ta saka sun shiga wani hali, kaga yanzu baya iya fita kasuwa ga Bashir kuma aikin da yakeyi ma an siyar da kamfanin shine nace ban sani ba ko akwai abinda zaka iya yi akai".

WATA KISHIYAR (ALKAHIRI CE KO SHARRI)Where stories live. Discover now