page one

17 0 0
                                    

      😭😔UBANA NE KO KISHIYA TA💔💔

         WRITTEN AND STORY
                BY
              NERNAH MARYAM
                (MEEMARH)

                                          Zafafa Biyar 2024

Gargadi........

Wannan littafin mallaki Na ne kuma bana yi shi don cin zarafin wani ko wata bane hasalima duk wanda ya ga ko ta ga labarin yayi daidai da tsarin rayuwar ta ko makamancin hakan to ina me bada hakuri,

Sannan ban yarda wani ko wata su juya mun labari Na ko su canza ba tare da neman izini Na,

Da sunan Allah me rahma me Jin kai,Allah yanda Na fara rubuta labarin nan lafiya Ubangiji ka sa Na gama shi lafiya,

..............
Page one

**********Bauchin Yakubu

GRA

Karan hayaniyan mutane tare da bugun gate in wani tangamemen gida ne yayi alarming securities in gidan kan bakin da me gidan ke expecting tun safe sun iso

Sunday ne ya mike tare da kallon mal Iro yace "Iro I think they are here already make I do quick and open this gate before oga change am for me"dariya mal Iro yayi tare da bantaran goron sa domin shi sam ba gane wanga turanci na Sunday yake yi ba,normal turanci ma ya ya kare da shi balle wata broken.

Shi ko Sunday cikin sauri ya tashi tare da nufan black gate in saida ya bude kofar ya leka ganin dandazon yan Jaridu ne ya sanya shi saurin bude gate din,gaisuwa suka yi exchanging bayan sun shigo cikin premises din gidan.

Masha Allah na fadi sakamakon karewa gidan kallo da nayi, wato gida ne wanda ya amsa sunan sa gida babban duplex building ne wanda aka kawata wajen gidan da flowers kaloli daban daban,kallo daya za ka yi wa gidan ka san mamallakin sa ba karamin attajiri bane domin duk layin zan iya cewa gidan Sen RILWANU AUDU WAZIRI .... Ya fi na kowanne kyau,da tsaruwa.

Sa'eed ne ya fito daga cikin main house din gidan sanye da black and white uniform, shine mafi kusanci da Senator Rilwan.

Cikin fara'a ya karasa gurin yan jaridun domin an riga an san da zuwan na su,sun zo ne domin tattaunawa da Sen RILWANU AUDU WAZIRI wanda aka tsayar a partyn su domin yin Takaran Gwamnan jahar Bauchi,ganin zabe ya karato ne ya sanya ya hada zaman shi da kanshi domin bayyanar da wasu raayoyin shi tare da amsa wasu yan tambayoyi da suke ta son masa.

Ba karamin lucky da dadi yan jaridun da suka samu zuwa suka ji ba domin sun san ko banza bara su koma hannu na dukan cinya  ba domin Sen RILWANU an san shi da halin kyauta da son jama'a ka'ida ne duk wani wanda ya zo ganin shi to baya zuwan banza.

Iso Sa'eed yayi musu zuwa ga wani babban Hall dake cikin gidan wanda an yi shi ne daman domin taro,
Hall ne babba me kyau dauke da kujeru da Dan karamin tables Wanda ke dauke da snacks and drinks a kan ko wanne.

"Bismillah have a seat" Sa'eed yace yana murmushi su din ma murmushin suka yi tare da fara kokarin zama,inda ya juya yana fadin "bari na sanar da Sen zuwan ku kafin nan ku fara shan ruwa".

Ya wancin gurin ba karamin dadi suka ji ba domin ka je inda za a karbe ka a mutunta ka har a baka abun makulashe ma wani abu ne,nan suka hau Dan ciye ciye da dan shaye shaye kun san mutanan mu ba a ganin bati a bari lol....

Kusan 15 mints da fitan Sa'eed suka fara jin alamun tafiya tare da magananganun mutane wanda ya tabbatar musu gwamman goben su ne ke tafe,da sauri suka yi arranging kansu tare da kokarin setting cameras din su domin kowa so yake ya fara daukan sa a hoto.

Kofar aka bude inda securities din sa ne kusan su biyar a gaba sanye da irin same kayan da ke jikin Sa'eed sai wasu biyar din a baya sai kuma wasu mutane su uku a tsakiya ko wannan su ya hade cikin dakkakiyar shadda sai kyalli kawai suke zuba wa da kamshi.

UBANA NE KO KISHIYA TA Where stories live. Discover now