Page 4

0 0 0
                                    

             😭😔UBANA NE KO KISHIYA TA💔💔

            STORY AND WRITTEN
                       BY
      NERNAH MARYAM
        (MEEMARH)

Zafafa Biyar 20224

Ga masu son a tallata musu hajojin su kofa a bude take,suyi mun magana ta wannan no:

          08100046388

............
           Page four

***********

"Ranka ya Dade in har da gaske Hajiya Nadeeya jefan ta aka yi to ai magungunan gargajiya ya kamace ta ba Asibitin mahaukata ba??"Tambayan  da wani Dan jarida ya jefo wa SEN ke nan

Madadin ya amsa shi da kanshi Alhaji Kabiru ne ya mike ran shi a dan bace yace " wai why are you people after rayukan mutane ne?Can't you see irin stage in da yake and you guys are trying to rub salt on his wound,da wannan silly questions in naku"

Dafa shi Sen yayi domin ya san halin Aminin nashi da saurin  hawa and hakan ba karamar barazana bace ga siyasan sa.

Cikin calm voice yace "allow them su tambayi duk abunda suke son tambaya,tunda ai ni daa kai na na gayyato su,beside ai ba wani tambayan ban haushi yayi ba,yana da gaskia don kowa ya ji statement dina  ya kuma ji gidan mahaukata aka aika princess dole yayi mamaki,pardon my friend's behavior kasan ance,abokin da zai taya ka kuka yayin da wani abun rashin dadi ya same ka shine Aminin ka na ainihi, kamar yanda ka tambaya yeah jifan Nadeeya ta aka yi wanda duk mun sani Asiri gaskia ce tunda har fiyayyen halitta ma an masa ta kama sa,and kamar yanda ka fada haka ne maganin gargajiya ya kamaci wanda  aka jefe,saidai wannan jifan ta sha banban
domin a sanadin haka brain in Nadeeya ya tabu tabi me girma ma,ya kare yana share hawaye,wanda  bani da option sai dai dole a kaita asibitin su fara magance wannan matsalan domin wata jijiya da Is connected to her brain yaa samu matsala wanda  ya ci a gyara shi domin ceto ranta,bayan nan sai a koma na gargajiyar ganga ganga,duk da yanzun ma ba zama za a yi ba har sai an jira likita"

Wani ne ya kuma tashi domin yin wata tambayan, hannu Sen ya daga mishi tare da cewa "don Allah ku bar ni haka,bana cikin jin  dadi zuciya ta zafi take mun,ya ci na sha magani na kwanta ko zan samu hutu,domin yanda na ga daran jiya haka na ga rana  ko rintsawa ban yi ba,na gode sosai da zuwan da kuka yi,ina me bada hakurin rude behaviors din Nadeeya na jiya,domin ba a cikin haiyacin ta tayi ba,na yafe  mata duniya da lahira Allah ya baki lfy princess ita,ina rokon duk wanda ya kalli video din nan don Allah make sure ya sanya Nadeeya Rilwanu Audu Waziri a addu'a,ya kare with pleading hands,yana cewa mu je Kabiru, make sure Sa'eed ka sallame su"da haka suka bar cikin confirence Hall din.

..........NADEEYAH

Ni dai tun ana tafiya ina tunanin ina wannan mutanan mara sa imani za su kai ni,har idanu na suka lumshe bacci barawo ya kwashe ni,sun yi tafiyan mintoti kafin suka iso Teaching hospital dake nan garin Bauchi wato Specialist,inda direct Psychiatric clinic suka nufa(wato bangaran masu tabuwan kwakwalwa).

Parking driver yayi a bakin clinic din,inda nurses din da Doctor Bashir yayi waya da su akan su fito da stretcher (gadon daukan marasa lfy),suna bakin gurin suna jiran isowan sa.

Bude kofa yayi yace "where is Sister Kareematu?" "Am here Sir" wata mata ta amsa tana daga hannu.

"Maza ku dauke ta ku kai ta Isolated room din da na miki magana akai,I hope an kai komai da komai da za ta bukata ko,domin wannan ba kamar regular marasa lafiya bace wannan daban ce,don yarinya ce daya tilo a gurin SEN kin ga kuwa dole mu kula da ita yanda ya kamata"

Da mugun mamaki duk yan gurin ke kallon Nadeeya da ke kwance alamun bacci ma take abunta saidai daga yanda take baccin kasan na wahala ce.

Mamaki suke yi me zai kawo  Hajiya Nadeeya Rilwanu Audu Waziri wannan asibitin a hakan ma wai mara lfy,rashin lfyn ma na cutar brain,to wai yaushe ta haukace ne ma?and miye silan haukan nata,shine tambayan da yawancin nurses din gurin ke wa kan su.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Mar 06 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

UBANA NE KO KISHIYA TA Where stories live. Discover now