page two

12 0 0
                                    

      😭😔UBANA NE KO KISHIYA TA💔💔

           WRITTEN AND STORY
                       BY
     NERNAH MARYAM
        (MEEMARH)

Zafafa Biyar 20224
      

I Dedicated this whole book to you my dearest ummu Mansur (uwar daki na🥹❤️),I love you so beyond words ........

..............
              Page two

************************

          "Falmata!! Falmata"ihun kiran sunan ta Sen ke yi daga ganin yanayin sa kasan yana cike da tsantsan bacin rai.

Jiki na bari na ga wata yar dattijiwa ta fito tana goge sauran ruwan dake hannun ta a jikin zanin da ke jikin ta alamun daga kitchen ta fito,gaban Sen ta zo tare da zubewa jikin ta na rawa domin ko be fada ba ta san yau ta kade.

Kallon ta yayi na yan seconds sannan ya ja tsaki ya watsar,cikin bacin rai da hargagi kamar ba shi ne mutumin da ya gama magana cikin tattausan murya a gaban yan media dazu ba.

Da yatsar sa manuniya ya nuna ta sannan yace "Ashe Falmata baki da mutunci ban sani ba?"jikin ta na rawa tace "tuba nake uban gida na wlhh tallahi ban san lokacin da uwar daki na ta mike ba, zato na duk tana bacci na shiga kitchen domin samar ma abun da za ka ci in kun gama taro sai kawai shigowar ta na gani da su Sa'eed"ta kare a raunane.

"Dallah rufe wa mutane baki,yar iskar mata kawai, one simple task kawai na baki shine lura da Princess tunda na sanar da ke ina da taro yau amman saboda shashanci kin shiga wai kitchen dafa abinci,ai ko ba shakka kin dafa abincin karshe ke nan domin yau din nan zaki bar gidan nan"ya kare kamar zai rufe ta da duka.

Nan take ta hau kuka tana rokon shi Allah Annabi kar ya daga ta daga gurin neman Halal din ta, shekaru kusan nawa tana masa aiki,yayi hakuri yayi over looking mistake din nan da tayi wlhy ta dauka NADEEYA bacci take har yanzu duba da kwanan ta biyu tana bacci bata farka ba so bata dauka za ta tashi yanzu ba.

Alhaji Salis ne yace " ya isa haka Sen is of no use ka tsaya kana venting anger din ka akan wannan worthless matar,let's go and face our problem"ya fada so calmly.

Tirjewa SEN ya ke yi while Salis Na jan shi domin barin gurin don ya ga alaman ranshi yayi kololuwa gurin baci,da kyar dai ya samu suka bar gurin bayan Salis ya ce da Falmata dake ta faman rokon SEN ta tashi ta koma kitchen ta cigaba da aikin ta.

Har sun kai ga shiga part din shi ya hango Sa'eed,kamar wanda aka tsikara yace " Salis kira mun wancan useless boy d"in, daga gurin Alhaji Salis yayi wa Sa'eed magana kan ya zo SEN na son ganin shi.

Da sauri kuwa ya karaso inda suke tsaye, cike da girmamawa ya dan rusuna yace " Allah ya ja da ran ka gwamman mu na gobe"

"Gwamnan uwar ka!!" SEN yace cikin tsantsan bacin rai bayan ya wanke Sa'eed da wata zazzafan Mari,da sauri ya dafe kuncin shi don ba karya Marin ta shige shi.

"Dan uban ka Sa'eed me kuke yi har NADEEYA ta samu damar shigowa cikin press confirence dina?Nace uban me kuke yi?"Ya kare kamar zai rufe shi da duka.

Kan shi na kasa yace "yallabai wlhh ba laifi na bane laifin Muktar ne tunda su na bari a waje ni kam ai ina tare da kai a ciki"

Cikin bacin rai SEN yace "Salis ka duba ka ji wannan wawan yaro yake fada mun waye chief security dina? Ba kai bane?Ya ci ace duk kai za ka kula da komai, wlhy in har wani abu ya samu kujera ta wlhy tallahi gaba dayan ku baran raga muku ba shashashu kawai wanda basu san inda ke musu ciwo ba".

Jan hannun shi Salis yayi yace "don Allah RILWANU stop all this is not that necessary ta ho mu shiga ka samu ka sha ko ruwan sanyi ne"bayi da option sai bin bayan Alhaji Salis din wanda ke matsayin Aminin shi kuma mataimakin shi domin shi ya tsayar as deputy governor din shi,ko ba don komai ba ya ci ya jiga makoshin na shi don ba karamin bushewa yayi ba.

UBANA NE KO KISHIYA TA Where stories live. Discover now