Page 3

0 0 0
                                    

       😭😔UBANA NE KO KISHIYA TA💔💔

        STORY  AND WRITTEN
                BY
             NERNAH MARYAM
                (MEEMARH)

                                          Zafafa Biyar 20224
.............
             Page three

*************

Karfe goma daidai doctor Bashir ya iso cikin gidan SEN shida workers din shi a cikin motan daukan marasa  lafiya wato (Ambulance).

A zaune suke a parlor din SEN daga ganin alamun su tattaunawa suke me matukar mahimmanci

Doctor ne ya dago tare da kallon SEN yace "ranka ya Dade ban ki ta taka ba saidai ina jin  tsoron abunda ke iya zuwa ya zo"katse shi Kabiru yayi da fadin

"Look Bashir we do trust u ne ya sanya har muka damka amanar Princess a hannun ka so pls don't let us down"Kabiru ya fadi yana kallon cikin idanun doctor

"In sha Allah Alhaji I will not let you down yanda kuka ce hakan za a yi"ya kare yana washe baki,cike da alhini Sen yace " I still can't believe this wai Nadeeya Rilwanu audu waziri ce tayi hauka ya salam!!!don Allah Doc  do take care of my Princess for me I don't mind spending ko nawa ne ni dai all I want shine ta dawo normal"ya kare kamar zai yi kuka.

Patting bayan shi Kabiru ke yi yana "haba my friend be a man mana,na san da ciwo sosai ko dan kasancewar ta ' ya daya tilo a gurin ka amman  we are doing this for her own good,so allow the doctors to do their job pls"

Numfashi ya sauke sannan yace "yeah haka ne you gat some point ni dai all am saying here is Bashir ka kula mun da princess kar a samu wata matsala make sure duk abubuwan da Kabiru ya sanar maka ka gane ko?"

Da sauri Ubaidullah yace "yeah sir na gane in sha Allah bara a samu ko wani matsala ba ai mun sha dealing da cases din da ya fi na Princess ma in no time za ka ga ta samu lfy"

Nan take Kabiru ya ciro wayan shi tare da masa transfer din mil 5,debit alert ya nuna masa sannan yace "ga shi for a start mu dai fatan mu komai ya tafi daidai and ta samu lfy make sure a siya mata duk abunda take so extra kula nake so ku bata"

Nan take ya washe baki tare da zaro idanu Jin huge amount din da aka ambata hakan ma wai for a start wow harka da gidan gwamnati akwai samu ya fadi a can kasan ranshi,while a fili kuma godia yake ta zuba wa tare da kara jaddada musu kan cewa babu wata matsalan da za a samu daga gare shi his daughter will be safe and sound.

Mikewa SEN yayi yace "okay in dai haka ne ai no need of wasting time mu je ku tafi da ita kawai"

............... Nadeeyah

Ba yanda Falmata bata yi da Nadeeya ba kan ta tashi daga kwanciyan kukan nan da take yi tayi wanka ta sauya kaya ko itama ta ji dadin jikin ta domin Sen ya aiko ace da ita ta sanya Nadeeyan wanka za a tafi da ita,tayi kuka sosai tare da tofin Allah tsine ga duk me sa hannu a samun rashin lfyn Nadeeyan.

Kallon ta Nadeeya tayi da red eyes din ta tace "wai Inna Falmata ke ma kallon mara lfy kike mun?wai me yasa kun kasa gane wancan mugun mutumin azzalumi ne,I thought in duk duniya sun kasa fahimta ta ke za ki fahimce ni duba da irin shakuwar da ke tsakanin mu,ta kare tana kuka don Allah Inna Falmata kar ki bari a kai ni ko ina tunda ke ma kin ce baki san yanda za a kai ni ba ni fa lafiya ta lau"ta kare tana share hawaye.

Ita din ma Inna Falmata hawayen take yi tana "Allah ya baki lafiya uwar daki na tabbas an cuce mu, an kuma zalunce mu,in ba haka ace duk irin shakuwa da soyayyar dake tsakanin ki da Ranka ya Dade ace ki masa irin wannan diban Albarkan??"

Jin knocking din kofar da aka yi ne ya sanya ta mike wa da sauri Nadeeya ta  riko ta tana rokon ta don Allah kar ta bar ta,jiki a sanyaye tace "yi hakuri uwar daki na ina zuwa"da sauri ta bar gurin don ta cigaba da zama kuka za suyi ta yi,hakika ciwon nan Nadeeya ke yi amman har cikin Jinin jikin ta take Jin zafi da radadi.

UBANA NE KO KISHIYA TA Where stories live. Discover now