Part 35!!

10 1 0
                                    



Kamar ko yaushe bayan na tashi daga bacci gyara dakin nayi na sakko kasa
Kitchen na shiga na hada breakfast na fito
komawa parlor sama inda yake zaune yana kallo kamar ba abunda ya faru
Gaidashi nayi ya sakko kasa nan carpet ya zauna
Na ajje tray da flask din da ke hannuna kusa dashi
Tare da komawa gefe na zauna

Ganin fuskar shi ba alamun annuri yasani shiru ban ce komai ba amma tambayoyi ne fal zuciya ta wanda nake bukatar amsar su
Ya dade yana yangar sa kafin ya gama ya ture tray gefe ya tashi zuwa mini sink din dake parlor ya wanke hannu ya dawo
Daukar tray nayi na fito ganin bashi da niyyar yin mgn
Fitowa ta kenan kiran sultana ya shigo
"Hello maman baby "
"Sareenah kinji abunda ya faru?"
"A gaba na ya faru Sultna wlh gaba daya hankali na a tashe yake "
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un shi ko yaya ne ta mishi da zai mata saki har uku "
Tray hannuna ne ya fadi Jin ta ambaci uku
"Me kika ce saki uku? Anya kinji dai dai"
"Danallah ki fadan Meyefaru ne ta mishi yaki daukar wayar kowa bansan sau nawa na kirashi yanxu haka mgnr da nake miki she's hospitalized Anjima zasu wuce Kano zan cen gsky yaya bai kyauta ba duk da bansan abunda ya hadasu sai dai ke ko Zaki iya sani"
"Wlh ba abunda nasani banga fuskar da zan tambaya hakan ba gaba daya yau Bbu annuri a tattare dashi Idan na tambaya zan iya janyowa Kai na Bala'i "
"Danallah toh Kina mgn dashi ki kirani yanxu zan daga waya ne ana kirana ina Jin nima kano zan wuce gsky abunda ya mata ban ji dadi koma mene yer uwar mu ce ko dan wannan alaqar ya hakura danallah ki samo kuyi mgn "
" in sha Allahu"
Kashe wayar nayi tare da kwashe abunda ke kasa na sakko zuwa part dina
Gaba na faduwa yake da ni kaina bansan dalili ba amma me ta mishi haka da zai yanke wannan hukuncin batare da izinin kowa ba abunda ke raina kenan
Jin karar tada mota yasaka ni bude window hango shi nayi cikin shigar shi ta kayan sojoji an bude mishi kofa ya shige ciki
Wato shi ba abunda ya dame shi kamar ba abunda ya faru anya kuwa kalau yake ? Tambayar da nayi wa kaina kenan tare da rufe window na koma ciki
Wanka nayi na fito
Bobu na sa ta lace na daura dankawli na fito
Waya ta dake parlor sama na dauko
Miss calls nagani na hajiya har biyu
Ba shiri nayi dialing numb ta

"Hello hajiya ina kwana"
"Lfy lau y gd? "
"Alhamdulillah"
"Yana gida yanxu ki miqa masa wayar?"
"Aa ya fita daxunnan"
"Ya fita koma?"
"Eh amma ina Jin ya dawo da wuri"
Shiru tayi na wasu minutes kafin tace
"Wani abun ya samo wayoyinshi ne?"
"Wlh hajiya bansani ba "
"Meyefaru jiya da dare tsakaninshi da Shalina?"
"Hajiya wlh bansani Meyefaru ba ina bacci naji yo hayani ya na sakko kasa lokacin na gansu tare tana kuka shi koma ya wuce ya barta a gurin bai barni na karasa inda take ba balle na san me ta mishi yau ma bai bani fuskar da zan tambayi hakan ba amma Idan ya dawo zan tambaya duk da nasan fada zan sha "
"Nooo karki tambaya stay out of this ki fada mishi na kira ki ina koma jiranshi, bayan hakan ba wani Abu da ya faru a kwanakin baya?"
"Gsky bana ce ba  Idan ba girki na bane baba shiga barinsu haka ita ma koma haka ne a bangaren ta"
"Ki sanar dashi na kiraki sannan idan ya miki wani Abu ki sanar Dani"
Sallama mukayi tare da kashe wayar
Sakkowa nayi na kira su bilkisu su zo su fara aikin su sannan na dafa tea ne citta da bread na fito
Dinning space na karasa na zauna
Cen na jiyo muryoyi na tashi sama sama
ajje cup din dake hannuna nayi na dauko waya ta ma fito ganin bilkisu bakin kofa tana kokarin ture wasu
"Bilki meke faruwa?"
"Madam gurinki suka zo ba koma alkhairi ke tattare dasu ba"
Kallon mamaki nake mata
"Bude su shigo "
Budewa tayi ta koma gefe wasu mata biyu manya daga ganinsu sun baya 40 baya sunyi daurin ture kaga tsiya kamar yadda ta fada ba alkhairi ke tattare dasu ba
"Keee yar gidan talakawa yer matsiyata jikar matsiyata banza jaka Mara hankali da kamun Kai har kin isa ki kori yar mu daga gidannan ne kike ji dashi me kika taqama dashi Idan banda talauci ko ce miki akayi baa san tarihin ki ba toh wlh ahir dinki mun fi karfin ki"
"Ke wai Zaki setting record wato kin kori kishiya wata uku da aure toh wlh Bari kiji na fada miki da babbar murya idan muka so ko kwana daya bazaki kara kwana a duniya ba ita gidan ta bari ke koma duniyar zaki bari baki daya ki sani koma ba wai saki uku ba ko dubu yayi mata sai ta dawo gidannan wannan alkawarin Mama zee ne idan kinsani kinsan bana yin alkawari na koma kasa cika wa Wallahi tallahi zaki san wa kika rabi Zaki san kin dauko ruwan dafa kanki ba ke ba har da kusa dake sai sun san an tabo mu"
Jin sunan da ta fada yasa gabana yayi mummunar faduwa
Sai dayawa nasha jin sunanta a bakin mutane da dama cikkakiyar yar bariki ce haka koma yar bin boka da malam ba wai a iya kananan mutane abun ya tsaya ba ita ke yiwa manyan yen siyasa hanyar bin bokaye kasashe daban daban ban taba tunanin Abu zai hada ni da ita ba sai yau
Amma duk da haka na dake ban nuna naji tsoro ba
Jamila da nice na kira ba shiri suka bayyana
"Ku fita dasu"
Ina fadin haka na juya tare da barin gun
"Ke har kin isa me kike taqama dashi wlh ko me kike ji da shin na dama ki na shanye dan ubanki ni zaki ce a fita dani gidan uwarki ne ko ubanki yar shegu"
Jin maganganun da suke fada yasa na kasa jurewa na dawo dauke da ta barya a hannuna
"Ya ishe ki haka wallahi zan raunata ki" na fada da karfin da ni Kina bansan muryata na karfin haka ba
Dukkansu sai da suka tsorata
ganin dgsk nake yasa su ja da baya
Sunan Allah kawai nake kira a raina
Har lokacin basu daina maganganu ba irin nasu na yen tasha
rufe kofa ta nayi tare da sa key
"Ku cigaba da aikin ku " na tare da miqawa Nice tabaryar na hau sama
tsoron dake raina kara karuwa yake
Numb mama na kira
Zayyana mata duk abunda ya faru nayi
Ita kadai ce ta kwantar mun da hankali tana koma fadan Allah yana sane da komai na cigaba da Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un
Mun dade mun waya kafin na kashe

Sallar azhar nayi na hada lunch na bawa driver ya kai mishi office
Bayan na gama na kira sultana jin ko ta samo wani bayani
"Wlh auntyn baby har yanxu ba abunda nasani nasan sun karasa cen dake Daddy su na nan I think a privat jet dinshi ta tafi I'm very sure aunty ce zata ce ta bar nan tunda ita na cen"
"Toh danallah idan kinji wani ki sanar dani nima idan na samu munyi mgn zan kiraki "
Sallama mukayi sannan na kashe

Misalin karfe 7:30 na gama hada Dinner 🥘
Dauko tray nayi n hada komai a kai na fito zuwa parlor
kamar ko yaushe yana zaune gani na yasa shi sakkowa kasa ya zauna
ajjewa nayi a kusa dashi tare da serving dinshi
Bai dade yana ci ba ya gama
Ruwa na miqa mishi kamar yadda ya bukata na dauke tray zuwa kitchen
wankewa nayi na dawo dauke da tea me citta da ya bukaci na hada mishi
kan 2seter na zauna yana sipping tea shi a hankali yana kallo as usul News yake kalla
gaba daya ba gane me suke cewa nayi ba amma na kurawa tea ido Ina tunani Kala Kala cen na tina mgnr hajiya
"Uhmm hajiya tace tana jiranka "
Kal kallo na baiyi ba haka koma bai bani amsa ba
Juyawa nayi na cigaba da kallo duk da ba fahimta nake ba
"She slept with another man" ya fada ba tare da ya kalle ni ba
"Shalina????"
Nodding kanshi kawai yayi bai ce komai ba
Kallonshi nake Ina jiran Jin Karin bayani amma ko kallona bai yi ba kamar ma ba mutum a parlor
Dan karamin tsaki nayi na juya
amma yana tabbacin ita tayi hakan? yadda ta ke sonshi har zata iya yin hakan abunda da kamar wuya
this's unbelievable ay kamata yayi bincike before ya yanke hukunci
Ni kadai nake sake sake a zuciyata ba karya mgnr ta girgiza ni it's hard to believe

Har karfe I0:30 Muna zaune kafin ya tashi Nima ba tashi tare da kashe Tv na bi bayanshi
Daki muka karasa ya shige toilet ni koma na canza zuwa Pjmas dina na kwanta
Ban jima da kwanciya ba ya fito
"Ki shirya zamu je Kano gobe"
Ya fada yana kallo inda nake
"Toh Allah ya kaimu"
Na fada tare da mai da kaina gefe
Na kasa gane dadi nake ji ko akasin haka a yanxu dai Muhammad nawa ne ni kadai kamata yayi naji dadi amma koma bansan meyesa nake jin akasin haka ba
a mgnr gsky ban taba kawo zai saki Shalina ba har na saba da hakan duk da Ina da tsananin kishi amma na kan fadawa zuciyata shi mijin mace Judy ne haka koma ita matarshi ce
sai dai yanxu da ya kamata naji dadi koma nake Jin fargaba har ga Allah banji dadin yadda suka rabo ba duk da ba shiri muke da ita ba amma da zai dawo da ita zan ji dadi sai dai koma hakan bazai faru ba ba koma yadda zan iya yi
Da wannan tunanain a raina bacci ya dauke ni....

Sareenah

Comments, like & share

!!!!!!!

SareenahTempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang