Two

209 30 6
                                    


Siraran yatsu guda biyu ne aka yi amfani dasu wajen kwankwasa ƙofar wani office wanda a jiki aka maƙala sign ɗin 'Do Not Disturb' wanda mamallakiyar yatsun tayi mishi kallon taro da kwata.

"Come in." Aka amsa daga ciki.

Jin haka yasa ta murɗa handle ɗin ƙofar tare da turawa kana ta kutsa kai ciki tana kallon tsarin office ɗin kamar yau ta taɓa shiga cikinsa. Cikin seconds da basu fi biyar ba ta gama assessing babban office ɗin sannan ta mayar da dubanta gefen dama inda Mahaifinta Governor Sufi Adam ke zaune a kan kujera mai juyawa da mutum, gabansa kuma babban office table ne da aka ajiye komai a mazauninsa a tsare. A gefenshi kuma yayanta Ahmad ne ke tsaye hannunsa rike da wani file suna dubawa tare.

Basu ɗago suka kalleta ba wanda dama ta san hakan ne zai faru, cikin sabo da halinsu ta yiwa kanta mazauni a kan ɗaya daga cikin Royal chairs dake gefen hagu na office ɗin tana mai duba wayarta da ke hannunta ta fara latsawa.

Mintuna biyar da haka ta ji ta ƙosa domin har lokacin basu gama maganan ba, gyaran murya tayi wanda hakan yasa suka ɗago da kansu suna dubanta.

  Mahaifinta da suke kira Daddy shi ya fara murmusawa kana ya zare medicated glass ɗin da ke idanunsa ya ce,

"Mamana kin gaji da zama ko? Yanzu zamu gama sai inyi magana da ke. Ok?" Ya ƙarisa maganan cikin lallami da kuma sanyin murya.

Kallonshi tayi fuskarta babu yabo ba fallasa ta gyaɗa kanta kana ta cigaba da danne-dannen wayarta ba don ta so hakan ba. Da haka suka mayar da dubansu kan file ɗin Ahmad na magana Governor Sufi Adam na gyad'a kanshi yana jefa tambaya idan buk'atar hakan ta taso.

Bayan wasu mintuna biyar suka gama Ahmad ya fita ya barsu su kaɗai. Governor Sufi Adam ya miƙe tsaye ya isa gaban wani dogon standing fridge da ke manne a jikin bango ya bud'e kana ya d'auko ruwan gora ya tsiyaya a glass cup sannan ya dawo gurin da ƴar tashi take zaune shima ya zauna.

"Mamana ga ruwa." Ya mik'a mata wanda hakan yasa ta ɗago fuskarta kana ta girgiza kanta tana cewa,

"No, ina azumi Daddy."

Ajiye ruwan yayi a wani stool da ke gefenshi kana ya tattara duk hankalinshi ya mayar kanta, hakan yasa ta ajiye wayarta a cinyarta itama ta dubeshi nervously a karon farko tun shigowarta, amma wannan karon zuciyarta ce ta fara bugawa tana fatan da kuma addu'ar kar mahaifin nata ya ƙi na'am da buƙatarta.

"Na yi nazari akan maganar da kika zo mini dashi last week, shin har yanzu kina son tafiya baki canja ra'ayinki ba?" Yace da ita yana mai tsareta da ido.

"Ban canja ba Daddy." Ta yi saurin amsawa har tana shaƙewa da yawun bakinta.

Shiru yayi yana nazari sannan ya yi ajiyar zuciya ya gyara zamanshi ya ce,

"Meyasa kike son tafiya ki barmu Jidda? Meyasa ba zaki bari sai kin gama secondary school a nan Nigeria sai ki tafi University a can ba? You are still young mamana shekararki sha biyar...." Bai kai ga ƙarisa maganan ba ta katseshi da cewa,

"Daddy I'm sixteen last month wanda har shirya mini birthday party ka yi that you never showed up. Can't you see dalilin da yasa bana son zama a nan? Because kullum baka nan Daddy. Aikin ka shine top priority ɗinka mu iyalanka comes second, how could I live a gidan da babu wani mutum ɗaya da zan gani in ji farin ciki? Kullum baka gida, Yaya Ahmad shima yana tare da kai, I lived all by myself sai bunch of servants da suke bina da pitiful eyes saboda sun san halin da nake ciki. I just want to be out of here saboda every damn thing in this house remind me of my mother and it sadden me." Muryarta ce ta fara karkarwa idanunta suka ciko da hawaye suka fara zuba a fuskarta.

"We all missed her, amma tafiyanki ba mafita bane saboda idan tana nan baza ta so mu watse haka ba. Zata so mu zauna tare as one big happy family."

"Family is when all its members are home Daddy, nakan yi kwana uku ban sakaka a idona ba. Ta yaya zaka san damuwata har ka magance mini? Ta yaya zamu zama one big happy family alhali kowa harkan gabansa yake yi? Ta yaya wannan burin nata zai cika bayan members ɗin are not willing to try? Idan kana son ganina cikin farin ciki just let me go, please Daddy. And I told you ba ni kaɗai zan zauna ba as I said earlier zan zauna ne a gidan Yaya Haajar."

Ta ƙarisa maganan tana zamowa daga kan kujeran ta rarrafo ta zauna a ƙasa inda ƙafafunshi suke ta dubi fuskarsa da ta haɗe guri ɗaya babu annuri ta ce,

"Please ka barni in je gurin ƴar'uwata in zauna tare da ita, I promise you zata kula dani fiye da kulawan da masu aiki suke bani a nan Daddy. Please. Just don't say no."

Sai da ya ɗauki kusan tsawon minti biyu yana tunani sannan ya buɗe baki ya ce,

"Na amince zaki tafi amma da sharaɗi..."

Jidda da tunda ta ji ya amince ta fara murmushi domin ya gama biya mata buƙatarta don haka duk wani sharaɗinsa zata iya ɗauka. Kaɗa kanta ta yi alamar tana sauraranshi tana goge hawayen fuskarta, annuri kuwa cike fal a fuskarta.

"Na farko duk hutun da aka yi zaki dawo gida kiyi a nan, na biyu kullum zaki mini text na halin da kike ciki sannan duk abun da kike buƙata ni zaki tambaya ba yayarki ba. Na uku zan saka bodyguards da zasu dinga kula dake from a far saboda bana son abun da ya faru a baya ya sake faruwa, I can't take it again."

Maganarshi ta ƙarshe ita tayi sanadiyyar ɓacewar murmushi a fuskar Jidda dalilin tunowa da tayi da baƙar ranar da har yau tana mafarkinsa idan ta kwanta bacci. Dukkaninsu fuska babu walwala suka cigaba da magana akan wannan CANJIN MUHALLIN da Jidda zata yi nan da sati huɗu masu zuwa.

Four weeks Later

Jidda ce zaune a cikin Abuja International Airport tana jiran jirginsu da zai tashi ƙarfe tara na safe, gefenta Yayanta ne Ahmad yana mata nasiha wanda tun satin da ya gabata yake mata a duk lokacin da ya samu damar yin hakan.

"Ki tsare mutuncinki kar kuma kiyi wasa da ibada don Allah Jidda. Wallahi bana son wannan tafiyan naki amma babu yanda na iya ne."

Har ta buɗe baki zata yi challenging ɗinshi kan cewa ko tana nan ɗin ma bata ganinshi a gida amma sai ta fasa ganin damuwa a fuskarsa ƙarara. Ta san yana sonta domin jini ba wasa bane, sannan halin da suka tsinci kansu a ciki ya samo asali ne daga tashin hankalin da ya faru dasu shekara biyu da suka wuce. Sai kawai ta samu kanta da cewa,

"I will miss you Ya Ahmad. Take care of yourself."

"You too Kitten." Ya faɗa yana riƙo hannunta cikin nashi hawaye na taruwa a idanunsa amma bai bari sun zuba ba.

Wannan suna 'Kitten' da ya kirata dashi shi ya karya mata zuciya, nan da nan hawayen da take dannewa suka fara sauƙa kan ƙuncinta. Mamanta ce take kiranta da wannan sunan dalilin idanunta da suke kama da Cat Eyes, yawan kiranta da take yi dashi yasa Yayanta Ahmad ma ya kama amma zata iya rantsewa rabon da ya furta wannan sunan shekara biyu kenan da suka wuce.

  Kwantar da kanta ta yi a kan kafaɗarshi tana share hawayen fuskar tata. Sun jima suna zaune suna hira kad'an-kad'an suka jiyo muryar wata mace a loudspeaker tana cewa,

'Good morning passengers. This is the final boarding call for flight 37B to Newyork, USA. Please have your boarding passes and identification ready and proceed to gate....'

Cikin Jidda ne ya ɗuri ruwa nan take ba don komai ba sai don tsoron canjin muhallin da zata yi. Suna yawan fita ƙasar waje hutu amma wannan karon idan ta tuna wai zama zata yi a can sai ta ji tsoro ya shigeta. Sannan idan tace baza tayi kewan gidansu da mutanen ciki ba tayi ƙarya, shin anya wannan tafiya tata baza tayi regretting ɗinshi daga baya ba? Tana wannan tunanin ta jiyo muryar Ahmad yana cewa,

"They are calling you."

Miƙewa tayi tsaye ta ɗauki Handbag tare da jakar laptop ɗinta dake ƙasa kana ta ratayasu a kafaɗarta sannan tayi hugging ɗinshi briefly ta nufi inda ake kiransu. Kafin ta sha kwana ta juyo tana kallon Ahmad wanda yake tsaye yana ɗaga mata hannu bayansa kuma securities ne har guda biyar cikin kayan gida suna kalle-kalle. Murmusawa ta yi itama ta ɗaga mishi hannu tana tunanin itama tabbas ba ita ɗaya zata yi wannan tafiyar ba, dolene akwai securities da suka yi shigen kayan gida da zasu rakata har ƙofar gidan yayarta.

Bayan an gama checking ɗinta da sauran mutane ta shiga jirgi inda ta zauna a first class tare da wasu tsiraran mutane irinta. Kashe wayarta tayi kamar yanda aka umurcesu sannan jirgin ya tashi ya luluk'a sararin samaniya cikin gudu.

Please vote, comment and share with your friends. ❤️

Mum Fateey 👌

CANJIN MUHALLIWhere stories live. Discover now