Six

189 23 2
                                    

Jidda tana fitowa daga wanka ta yi sallan azahar sannan ta zauna ta fara cin abincin hannu baka hannu kwarya, bata saba da yunwa ba, don haka a yau da bata samu tayi lunch da wuri ba sai yunwan ya wahalar da ita. Tana gamawa ta ɗauko Assignments ɗin da aka basu ta fara yi domin ta san anjima kaɗan zata fara jin bacci dalilin gajiyar da ta kwaso, bata gama ba har kusan biyar na yamma. Miƙewa tayi tsaye tare da yin guntun hamma sannan ta fita daga ɗakin, a bakin ƙofar ta haɗu da Mrs Smith.

"Na zo ɗaukan kwanukan ne, nace a yanzu kin gama amfani dasu."

"Ohh. Gasu can a ɗaki, thank you." Da haka ta nufi stairs don nemo yayarta.

"Baby sis! Yanzu nake da niyyar kiranki. Ya gajiyan naki? Ga makwabciyar mu gidanta shine a gefen daman mu, sunanta Mrs Adrian." Faɗin Haajar tana zaune a sitting room tare da wata baƙuwa mai jan kunne.

"Hello. Just call me Karen. She look just like you, beautiful." Faɗin Mrs Adrian tana kallon Jidda with big smile a fuskarta.

"Hello Aunty Karen. It's nice to meet you." Jidda ta amsa wanda maganarta yasa mata mai jan kunnen ta dafa ƙirjinta tare da zaro idanunta waje cikin mamaki.

"Har na tsufa haka ne?" Ta tambayi no one in particular tana taɓa fuskarta.

"Ohh no! A Nigeria mu muna kiran waɗanda suka girmemu da title irin Aunty ko Uncle, I'm sure hakan yake ga ƙanwata. Ko Jidda?" Haajar tayi saurin gyara zancen don ta lura kamar ran Mrs Adrian ya ɓaci, wani abu sai bature, a baka girma kace baka so?

"Yes. Haka nake nufi. You look ok Karen."

Haajar ta dafa goshinta tana jin dariya na son kwace mata domin Jidda ta ƙara kwaɓa zancen.

"Ok? Hajay, na tuna ina da abun da zan yi a gida." Faɗin Mrs Adrian bayan ta miƙe tsaye ta nufi ƙofar fita Haajar kuma ta taka mata baya tana cewa sai ta sake ganinta.

"Jidda kin kora mini baƙuwa." Haajar ta kwashe da dariya ta zo ta samu guri kusa da ƙanwar tata ta zauna.

"Me na mata ne? Kamar ranta ya ɓaci fa." Ta ɗauki biscuit da ke kan tray ta kai bakinta.

"Ke baki san bature baya son a tsufar dashi ba ko? Musamman matansu. Yanzu Baban Hamza cewa yayi in kirashi da sunanshi haka gatsau nace ba zan iya ba. Kuma ke da zaki ce 'You look lovely or you look gorgeous' sai ki ce mata she look ok?" Ta ƙara kwashewa da dariya don dama ba wani shiri take yi da Mrs Adrian ɗin ba. Farkon zuwanta unguwar tana mata wani gani-gani da guntun baƙar magana a kan race ɗinta, sai daga baya Haajar ta buɗeta sannan suka fara zaman lafiya amma kuma na ciki na ciki.

"Ohh to ai ni ban sani ba. In kun ƙara haɗuwa ki bata haƙuri, ni ba baƙuwar zafi bace." Faɗin Jidda ba tare da damuwa ko ɗigo a ranta ba.

Don ta ɓata mata rai a rashin sani ba damuwarta bane, ita abun da ta fuskanta a gurin masu kalar fatarta ko kare ba zai ci ba. Tun daga yanzu kuwa ta fara tara enemies a maimakon friends ɗin da ta ci buri. Tana son faɗawa yayar tata abun da ta fuskanta amma sai ta ji ta kasa domin bata son sakata damuwa, zata cigaba da zuwa makarantar amma idan abun yayi yawa zata faɗawa Daddy ya cireta.

"Hamza yace mu haɗu a cikin gari zai kai mu restaurant mu yi dinner a yi celebrating first day ɗinki a school."

"Su kuma turawa komai sai an mishi celebration? Amma ba zai zama takura ba don kin ce tun safe ya fita yana buƙatar hutu."

"Nima na faɗa mishi haka amma yace babu komai, kuma kema na ga kin gaji gashi gobe akwai school. Zan saka ya canja ranar sai mu je Friday night."

Da haka suka cigaba da hira har zuwa maghrib sannan suka wuce ɗakunansu don gabatar da Sallah. Wannan tarbiyya ce da mahaifiyarsu ta basu na rashin wasa da sallah a duk inda suka tsinci kansu.

CANJIN MUHALLIWhere stories live. Discover now