One

587 46 3
                                    

CANJIN MUHALLI

Na
Suwaiba Muhammad (Mum Fateey) Marubuciyar
Matar Ƙabila
Fatu A Birni
Tafiyar Mu 
Ruwan Zuma

Bismillahir rahmanir rahim.

01
Sauƙan ruwan da take ji a fuskarta da dukkan ilahirin jikinta shi yasa ta fara buɗe idanunta a hankali tana rufewa, lokaci ɗaya kuma ta fara fito da harshenta waje tana ƙoƙarin ɓuɗe bakinta don ta samu ruwan ya shiga makwogaranta da yawa. Bata san lokacin da ta ɗauka tana yin hakan ba, sai ji tayi ta fara dawowa hayyacinta saɓanin ɗazu da bata ma san wacece ita ba.

Hannunta ta fara motsawa tana ƙoƙarin juyar da kanta dalilin ruwan dake shiga cikin hancinta yana barazanar hanata numfashi. Lokaci ɗaya taji wani irin ƙarfi ya shigeta tunawa da rayuwarta da ta yi gaba ɗaya da kuma dalilin samun kanta a wannan halin na gobe da nisa.

Yunƙurin tashi tayi wanda sai da ƙasusuwanta suka amsa, cikin tsananin jin ciwon da jikinta ke mata ta tashi zaune cike da dauriya. Hannayenta tasa a bayanta tayi garkuwa gudun kar ta faɗi don jiri take ji kanta na juyawa, sai dai har yanzu ta kasa tantance ainihin inda take.

Gefen damanta ta kai duba cikin mutuwar jiki yayin da zuciyarta ke bugu kamar zata fito waje. Fili fayau take gani sai ƴan tsiraran bishiyoyi can nesa sosai iya hangenta. Har yanzu ruwan da ya taimaka mata ta farfaɗo bai daina zuba ba, wanda a yanzu kwakwalwarta ta tabbatar mata cewa ruwan sama ne ke zubowa daga sararin samaniya, kyautan Allah a gareta kenan da kuma duk wanda ke cikin wannan dajin na Shi.

Gefen hagunta ta kai duba wannan karon, sai dai shi ma filine fayau babu alamar wata halitta mai rai cikinta. Bakinta ta fara motsawa wanda a da bata ko iya motsashi,

"U.. uustaz. Usss..taz." Ta fara furtawa a hankali, wanda ita kanta bata jin sautin yanda ya kamata balle ta yi tunanin wani zai iya jiyota.

Fashewa ta yi da kuka wanda hakan yayi sanadiyyar komawarta kwance sharaff, domin jikinta bazai iya ɗaukan wannan jarumtar ba. Mirginawa tayi tana mai yin ruff da ciki ta kalli gabanta, wanda a da ta juya mishi baya. A nan ne ta hango ƙafafun mutum cikin ledan PARACHUTE, gangar jikinshi kuma rufe take da ledan, hakan ya tabbatar mata cewa duk ruwan da ake tsugawa mamallakin ƙafafun bai ma san ana yi ba.

Da sauri ta miƙe tsaye cikin zafin nama ta fara tafiya tana layi kamar zata faɗi har ta isa gurinshi sannan ta fara ƙoƙarin yaye ledan parachute ɗin da ya lullu6e jikin nashi. Ta jima tana kokawa da ledan saboda rashin ƙarfin jikinta kafin Allah ya bata nasarar yaye mishi.

Da fuskarshi ta fara tozali wanda ta baɗe da ƙura bakinshi kuma ya tsattsage ya bushe babu alamar rai a tattare dashi. Zuciyarta ce ta mata nauyi da tayi tunanin ya mutu ne.

"Noooo!!" Ta faɗa da ƙarfi hawaye na sintiri a fuskarta.

"Nooo. Pleaaaase." Ta faɗa a karo na biyu tana share ƙurar dake fuskarshi, wanda a yanzu ya haɗe da ruwan sama sun ca6a fuskar.

Jijjigashi ta fara yi tana ambatan wannan suna 'Ustaz' ɗin sai dai bai motsa ba, yana nan kwance kamar yanda ta sameshi tun farko.

Sautin sauƙan ruwa kunnenta ya jiyo mata 'Tal tal tal, a nan kusa da ita, da sauri ta kai dubanta gurin, da takalminshi ta yi tozali wanda ya cika da ruwa yake bada wannan sautin. Zama tayi dirshan a ƙasa ta miƙar da ƙafafunta kana ta jawo kan mutumin da kyar ta ɗaura saman lallausan cinyoyinta.

Da haka ta buɗe bakinshi a hankali gudun kar ya ji ciwo ta fara zuba mishi ruwan lokaci ɗaya kuma tana tarewa da tafin hannunta don ya shiga cikinshi da kyau. Ruwan ta shiga tuttulawa bawan Allah nan wanda da alama yana shiga cikinsa don sha yake yi duk da baya motsi mai kyau.

Bata daina bashi ba sai da taga ruwan takalmin ya ƙare, ai kuwa cikin azama ta jawo ɗayan takalmin ta kafa mishi a baki ya cigaba da sha. Hawaye take yi wanda da dukkan alamu na farin ciki ne dalilin guntun murmushin da ya su6uce a fuskarta.

"Ustaz." Ta kira sunanshi tana hawaye, hannunta na dama ta saka tana goge mishi fuska bayan ta mishi rumfa da kanta don kar ruwan ya shige hancinshi.

"Wake up please. Ina jin tsoro." Ta ƙarisa maganan tana kallon dajin Allah da suke ciki.

"Ji....jidd...da."

Da sauri ta maida dubanta inda taji an ambaci sunan nata kana ta fashe da kuka cikin farin cikin tozali da tayi da idanunshi a buɗe, shima ɗin ita yake kallo cike da ƙarfin hali.

Kyakkyawan runguma ta mishi tana mai ƙanƙame kan nashi a ƙirjinta tana cewa,

"Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! Don't you ever leave me Ustaz. Please don't you ever!"

"I'm sorry, this is all my fault. I'm so sorry Jidda." Shima ya furta a hankali yana zagaye kunkuminta da dogon hannunshi.

Mum Fateey 👌

CANJIN MUHALLIWhere stories live. Discover now