Bakwai

369 38 15
                                    


Yau Ilyas ya zo gurin Juwairiyya, abun mamaki yana aikawa kiranta bata ɓata lokaci ba ta fito, sannan ta ƙara bashi mamaki ta hanyar yi mishi sallama tare da ɗaga mishi gaisuwa. Tunani ta yi mai zurfi, duk maneman nata da suka rage Ilyas ne kaɗai ta ga zata iya rayuwa dashi in har ta faɗa son shi. Sauran kam ko tunaninsu bata so kwakwalwarta ta kawo mata.

Shi kuma Ilyas tsabar murna kasa rufe bakinshi yayi, a jikin motarshi ta jingina yayin da shima ya fito ya tsaya a gefenta. Bayan ƴan gaishe-gaishe su ka ɗan yi shiru na wasu ƴan seconds kafin ya buɗi baki ya fara magana.

"Alamu sun nuna addu'ata ta karɓu, na ɗauka akwai sauran aiki a gabana Hajiya Juwairiyya."

"Hmm." Kawai tace don bata san me zata faɗa ba.

  Basu jima ba ta koma cikin gida domin tuni hirar ya gundureta ba don kuma Ilyas bai burgeta ba, a'a haka kawai ta ji bata son su tsawaita hiran. Tun daga ranar suka fara soyayya a hankali har ta kai Juwairiyya na iya hira da shi cikin walwala a nan kuma ta gane ta kamu da son Ilyas. Ita a rayuwarta idan namiji ya iya soyayya nan da nan zai sace zuciyarta, sannan ya dinga martaba mace ya ɗauketa a matsayin abu mai tsada abar tattalawa kamar yanda Hafiz yake cewa. Ta ɗauka ba zata taɓa samun namiji irinshi ba amma sai gashi Allah Ya kawo mata Ilyas duk da cewa bai kai Hafiz ɗinta ba. A hakan ma ta godewa Allah sannan tana ji a jikinta in dai ta aureshi zasu zauna lafiya domin tana da labarin matarshi tana da hankali bata da fitina ko kaɗan, to me ya fi ranta?

Wata ɗaya har da sati biyu da fara soyayyarsu ta ji shiru bai mata maganar aure ba, hakan yasa da aka ƙara sati biyu ya zama saura mata wata ɗaya wa'adinta ya cika ta yanke shawarar mishi magana.

Yau ma ya zo hira kamar kullum tana jingine a jikin motarshi wacce ya mata nacin su dinga shiga ciki suna hira amma ta ƙi. Saboda ko a lokacin da take budurwa bata shiga mota ta yi hira da saurayi, saboda bayan Mama ta haneta ita kanta ta san abun da zai iya faruwa a ciki ba mai kyau bane.

"Ni fa sanyi nake ji a wajen nan, nayi da ke mu shiga mota mu yi hiranmu a ciki amma kin fi son sanyi yayi ta shiga jikinmu."

Murmusawa kawai Juwairiyya ta yi kana ta fara tunanin ta yaya zata ɗauko mishi zancen tunda in a al'adance ne namiji ne yake fara kawo maganar aure ita kuma ta amsa.

"Bikin Sumayya yanzu saura wata ɗaya."

"Haka dai muke ta lissafi tare. Allah Ya nuna mana da rai."

"Ameen Ameen." Ta amsa sannan ta yi shiru.

"Ya dai naga kamar kina cikin damuwa?" Faɗin Ilyas yana matsowa kusa da ita.

Idan za'a tambayi Juwairiyya aibun Ilyas abu guda zata furta shine bai ɗauki taɓa macen da ba nashi ba a matsayin zunubi. A farkon zuwanshi yana respecting space ɗinta, amma suna fara sabawa ya nemi ya riƙe hannunta tare da son su shiga cikin mota su yi hira, babu ɓata lokaci ta nuna mishi bata son hakan don bata manta da cewa laifi ne mai girma aikata hakan ba.

"Wallahi Mama ce ta damu wai sai a haɗa aurena da na Sumayya. Na ce mata ni dai har yanzu baka mini maganan ba."

Shiru Ilyas ya yi, can kuma yace,

"Dama tuntuni ina son mu yi wata magana da ke amma na rasa ta yaya can ɗauko miki ita."

Jin furucinshi yasa cikin Juwairiyya ya kaɗa, nan da nan kuma ta fara addu'an Allah Ya sa ba cewa zai yi ba zai aureta ba, domin in har ya mata haka ya kassarata. Duk manemanta dama ƙalilan ne suka rage, a hakan ma tana fara soyayya da Ilyas ta koresu don ita tace ba zata yaudaresu ba, ba zata haɗa manema da yawa a lokaci ɗaya ba. Ilyas kuma da niyyar aure ya zo mata domin har bincike ta sa anyi mata a kanshi aka ce bashi da aibu. To me zai faɗa mata?

TAFIYAR MU (Completed)Where stories live. Discover now