Sha shida

310 9 0
                                    

Yana aiki a office amma lokaci-lokaci hankalinshi na komawa kan Amaryarshi da ya raɗa mata suna 'Masifa' amma babu wanda ya san da hakan sai shi kaɗai. Murmushi yayi a karo na ba adadi da ya ƙara tuno da abun da ya faru jiya da dare, shi kanshi bai yi zaton hakan zai faru ba domin yayi alƙawarin kama kanshi sai dai ganinta da yayi a ƙarƙashin rufin gidanshi da kuma sunan matarshi ta sunnah sai ya ji ba zai iya haƙuri ba sai ya ɗanɗani zumarta.

Tunawa yayi da ranar da ya fara ganinta bayan ya raka abokinshi kuma marigayi Hafiz hira gurinta. Sanin halin Hafiz na tara ƴan mata yasa ya ji baya son sabawa da ita gudun kar daga baya Hafiz ɗin ya dawo ya ce mishi sun yi faɗa sun rabu ko kuma ya ji ya daina sonta, ba karya yake yi ba hakan ya faru sau biyu zuwa uku. Sannan kuma a lokacin da Hafiz ya kira sunanshi akan ya zo su gaisa da ita baya jin daɗin jikinshi ne domin kanshi ciwo yake yi kamar zai tsage gida biyu, hakan yasa bai fito suka gaisa ba wai ashe hakan ya ɓata mata rai har ta ɗauki gaba dashi wanda shi a gurinshi ya ɗauki hakan a matsayin shirme da kuma rashin girmama na gaba.

Bayan Hafiz ya roƙeshi akan ya bincika mishi halinta ya bincika, binciken ma mai tsanani. A nan ya samu labarin rayuwarsu har da halayenta masu kyau, ganin ana yabonta yasa ya ƙarfafawa Hafiz gwiwa don ya aureta. Bayan haka ya so ya gyara tsakaninsu ganin tana da hankali sannan da gaske Hafiz ɗin zai aureta amma sai ya lura tayi nisa a fushin, hakan yasa shima ya ɗauke mata wuta domin bai ga abun fushi don ya ƙi zuwa su gaisa ranar ba, shine saurayin nata ko abokinshi Hafiz? Ko kuma shi zata aura?

Ko bayan auren ya ƙi zuwa gidan abokin nashi saboda baya son ta mishi raini don ko ɗaga mishi gaisuwa bata yi, to kenan shi take jira ya gaisheta? Idan ba zata bashi girma a matsayinshi na abokin mijinta ba ai zata bashi girma saboda ya sani ya bata shekara goma zuwa goma sha uku. He deserve some respect.

Bayan auren Hafiz kuwa ya haɗu da Salima wacce ta dace da siffar matar aurenshi, wato mai kunya, mai haƙuri sannan uwa uba submissive! A cikin wata biyu da haɗuwarshi da ita bata kauce maganarshi kuma bata mishi musu sannan ko da wasa bata taɓa mishi rashin kunya ba, hakan yasa bai jima da fara nemanta ba ya aureta gudun kar wani ya rigashi, sannan ko bayan aurensu bata canja hali ba tana mishi biyayya wanda ya so hanata yawan hulɗa da matar abokin nashi gudun kar Saliman ta koyi irin halinta amma sai ya ga tana son zumuncin da ita, wannan dalilin yasa ya barta sannan yasan idan ya hanasu zumunci Hafiz ba zai ji daɗi ba domin kuwa duk da rashin kunyar matar tashi yana sonta sannan ya lura bata yiwa mijin nata sai shi kaɗai da sauran mutanen da ta ƙullata a ranta.

Sau da dama idan suka haɗu ba zata gaisheshi ba sai Hafiz ya mata magana, hakan yasa shima ko ta gaisheshi baya amsawa don bai ga amfanin amsa gaisuwar da ba'a yi niyyar yinta ba. Wannan dalili yasa ko a ranar da Hafiz ya ɗauketa suka je gaisheshi a asibiti ya ƙi amsawa don ya ga lokacin da Hafiz ɗin ya take ƙafarta sannan yana ganin yanda tayi kicin-kicin da fuska sannan ta ɗaga gaisuwar wanda yayi kamar bai ji ba. Wannan karon ya lura Hafiz ya fara gajiya da halinsu domin bai ƙara tursasata ta gaisheshi ba ya nemi su fita waje su sha iska sai su jira matan nasu a can. A nan ne kuma ya fallasawa abokin nashi sirrin zuciyarshi na cire rai ga rayuwa! Kamar yanda kowanne ɗan Adam yake rashin lafiya sa'i da lokaci a rayuwarshi haka shima Muhammad yana wannan rashin lafiyan wanda in ya sha magani zai ji ya warke a wuce gurin, amma a yanzu baya wuce wata ɗaya zai kwanta rashin lafiya har gadon asibiti, an yi test kala kala don duba me yake damunshi amma sai dai a ce Malaria ce da Typhoid, ƙarshe kuma likitocin suka bashi shawara akan ya rage cin maiƙo sannan ya dinga yin exercise don rage kitse. Wannan dalilin yasa ya fara tunanin ko cutar ajali ce ta fara taɓashi domin shi kaɗai yasan me yake ji a jikinshi.

"Ina so ko bayan mutuwata don Allah ka kula mini da ahalina, sannan zan roƙeka don girman Allah ka mini wani alƙawari guda ɗaya!"

"Ina jinka." Hafiz ya amsa mishi fuskarshi cike da damuwa.

TAFIYAR MU (Completed)Where stories live. Discover now