Sha biyu

313 22 7
                                    


Kafin Abdul Jalil ya dawo gida Juwairiyya ta kwashi iya abun da zata iya ɗauka na buƙatunta ta bar gidan. Tana shiga ta samu Mama tana gurin aiki sai Nan (Kakarsu) da kuma mai aiki ne kawai a gidan. Babu ɓata lokaci ta buɗe ɗakin da tayi zawarcinta a ciki ta kwanta akan katifa taci gaba da kuka har Nan ta shigo ta sameta a haka.

"Ke ƴar nan ina miki magana kika ƙi kulani sannan kika shigo nan kina kuka? Me ya faru kika bar gidan mijin naki?"

"Don Allah Nan ki barni da abun da yake damuna ki daina mini wasu tambayoyi." Ta faɗi hakan tana mai juyar da kanta ɗayan gefen inda ba zata ga Nan ba.

"Ki ji mini ja'irar yarinya da rashin kunya, don na tambayeki shine ya zama laifi. To mutuwa aka yi kike kukan?" Ta ƙara wata tambayar don bata haƙura ba.

"Ni nace miki wani ya mutu? Babu wanda ya mutu."

"To menene ya faru?"

Daga haka Juwairiyya bata ƙara kulata ba, hakan yasa Nan ta juya ta tafi tana cewa,

"Kici kanki ke ɗaya."

Tunda Juwairiyya ta shiga ɗakin bata fito ba har Mama ta dawo daga aiki, Nan tana ganin ta dawo ta bata labarin cewa ga can Juwairiyya a ɗaki ta zo tana kuka. Gaban Mama ne ya faɗi rass wanda sai da ta ga duhu ya wuce lumm ta gabanta sannan ta dafe ƙirjinta ta nufi ɗakin da Juwairiyyan take tana haɗa hanya.

"Menene ya faru kika zo kina kuka Juwairiyya? Ki tashi ki faɗa mini abun da ya faru." Faɗin Mama tana shiga cikin ɗakin ta tsaya kan Juwairiyya.

A hankali ta miƙe fuskar nan tata ta kumbura idanunta sun yi jajur kamar garwashi sannan sun ƙanƙance duk da girmansu. Hijabin da yake jikinta kuwa ya jiƙe da zufa, hawaye har da guntun majina. Buɗe baki tayi da niyyar magana sai kuma wani kukan ya kwace mata har tana sheshsheƙa.

"Juwairiyya ki faɗa mini abun da yake faruwa domin hankalina ya tashi wallahi. Ki daina kukan nan ki faɗa mini." Faɗin Mama wacce a yanzu tsoron ya yawaita a zuciyarta.

"Daddy ya sakeni Mama, ya mini saki ɗaya."

"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un." Haka tayi ta maimaitawa bayan ta samu guri ta zauna."Me kika mishi Juwairiyya ya sakeki? Rashin kunya kike mishi ko kuma wani abun?"

"Wallahi Mama babu abun da nake mishi mara daɗi, lafiya kalau muke zaune yau yayi tafiya muka rabu lafiya amma ina shiga ɗakinshi na samu takardar akan bedside. Ko a fuska bai nuna mini ya sakeni ba har muka yi sallama Mama." Faɗin Juwairiyya tana ƙara jin haushin Daddy a ranta.

Dama ga abun da take gudu domin duk yanda za'a yi babu mai yarda da cewa ba laifi ta mishi ya saketa ba. Kwata-kwata auren nasu yanzu ya cika wata bakwai da ɗori! Me yasa ba zai ƙara haƙuri har su shekara ba kafin ya ɗauki matakin ba?

"Haka kawai ba zai sakeki ba Juwairiyya dole akwai wani dalili. Ki faɗa mini tun wuri sai mu san yanda zamu gyara al'amarin."

Ga kuma abun da take tsoro! Wato duk yanda zata kai ga faɗa musu cewa ba laifi tayi mishi ya saketa ba ba zasu yarda ba. Idan kuma ta fito fili ta faɗi gaskiyan al'amarin ta tona mishi asiri ne sannan wasu ba zasu yarda ba zasu ce ƙarya take mishi tana son wulaƙantashi ne a cikin mutane. Ta sani kuma zata iya rantsuwa Mama ma ba zata yarda da ita ba, to me amfanin bayyanawan? A zaman da tayi dashi ya kyautata mata don haka ba zata so ta kwaye mishi zani a kasuwa ba, ta wani gurin kuma Daddy uba yake a gurin Halima ƙawarta. Idan ta fito ta faɗi matsalarshi da wani ido zata ƙara kallon Halima? Zata rufa mishi asiri ko don waɗannan dalilai biyun amma ba zata taɓa daina jin haushin yanda ya saketa ba. Me yasa ba zai iya bata takardarta a hannunta ba sai dai ya ajiye ta je ta ɗauka? Ashe tun kafin ya tafi sunanta sakakka ce a gurinshi bata sani ba! Wannan sakin da yayi mata da kuma salon da yayi amfani dashi wajen sakin zai kasance a cikin zuciyarta har ƙarshen rayuwarta, ba zata taba mantawa dashi ba har abada.

TAFIYAR MU (Completed)Where stories live. Discover now